← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 112

Sashe 22

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 7 min read

ta fita. Yana nan inda Lami ta barsa. Tana bud'e k'ofar suka yi ido biyu dashi. Kwafa yayi tare da fad'in, "Na d'auka ai baza ki fito ba." A shagwab'e tace, "To wai ni mai zanyi maka ne? Dan Allah ka fita daga harkata." Gyara tsayuwa yayi tare da fad'in, "Zaki fara shagwab'an naki ko? Ki dai kiyayi kan ki, tom! Dama zan fad'a miki Baba ya riga ya damk'a min ke. Don haka ke tawa ce. Kuma sannan ki kular min da kanki da kuma babyn mu. Mai kike so in kawo miki a idan zan zo gobe?" Kuka ta saki tare da fad'in, "Wallahi kar ka k'ara zuwa mana gida. Ni bana son ganinka. Kuma babu abunda zai saka na aure ka. Ina haihuwa zan baka abunda na haifa maka, shikenan mun rabu!" D'age gira yayi tare da fad'in, "Za dai ki haifa min ko? In dai zaki haifa min baby d'in ai shikenan. Sai muyi deal ni dake. Idan kin amince, kamar yanda kika ce d'in, kina haihuwa zan karb'i d'an nawa shikenan kowa sai ya kama gabansa." Da sauri Sarah tace, "Eh na amince!" Waro idanu _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Tun kamun ma kiji deal d'in har kin amince. Ok, to shikenan. Na farko, duk lokacin da nazo, zaki fito, kar fa kiyi tunanin don in ganki zan zo, sam baby na nazo gani. Sannan idan na kira ki a waya, dole ki d'auka, shima ba don inji muryanki bane, lafiya babyna zan ji. Sannan duk abunda kike son ci zaki fad'a min, shima fa kar kiyi tunanin ke zan sayo mawa, a'a sam baby na na sayo mawa don nasan shi ke saka ki kwad'ayin. And dole ki rik'a shan magani tare da kiyaye duk wani abun da zai damu cikin jikin ki, sannan idan lokacin zuwa asibiti yayi, zaki je dole domin a duba min baby na. Idan kin amince da wannan sharad'in, bayan kin haihu ni da kaina zan shaidawa Baba na janye maganar auren ki, amma kuma idan baki harda ba, duk wad'annan abunda na lissafo dole ayi su, kuma a k'arshe sai na aure ki dole." Zaro idanu Sarah tayi tare da fad'in, "Kuma duka wad'annan sharad'in sai na cika?" D'aga k'afada tare da tab'e baki _Khalil_ yayi tare da fad'in, "If you wish, ki karya d'aya daga ciki. Amma ki sani, karya d'aya daga ciki yana nufin rushe deal d'in gaba d'aya. Kuma kin san dai abunda zai faru." Marairaicewa tayi tare da fad'in, "To ta yaya zaka gane idan ina son wani abu, kuma nak'i in kira in fad'a maka? Kuma misali idan ka kira wayar bana kusa fa?" Dariya ne ya kama _Khalil_, amma sai yayi murmushi kawai tare da fad'in, "Zan yi connecting CCTV camera ta inda zai r'ika hasko min duk wani motsin ki, idan ma bakya kusa na kira waya, zan sani, idan kuma da gangan ne, shima zan sani." Turo baki tayi tare da fad'in, "To amma baza a rik'a dad'ewa ba ko idan ka kira wayar?" D'aga kai sama yayi tare da fad'in, "Eh to, sai yanda babyn cikin ko yayi suggesting." Shuru tayi tana tunani, can kuma tace, "To amma kayi alk'awari idan na haihun zaka amshi babynka ka tafi baza ka sake dawowa ba?" B'ata rai yayi tare da fad'in, "Ohh wato baki ma yarda dani ba ko? Wato ga k'atoton mak'aryaci ko? To na ma fasa deal d'in. Zan yi duk abunda nace da k'arfi da yaji." Da sauri har da d'aga hannu Sarah tace, "A'a dan Allah kayi hak'uri ba haka nake nufi ba. Na amince da deal d'in." Wani mugun dariya ne ya kama shi cikin zuciyarsa. K'are mata kallo yayi ya tabbatar da yarinya ce ita. "Shekarunki nawa?" Ya tambayeta. Kanta a k'asa tace, "I'm 21years old." Sai da ya kuma kallonta daga sama har k'asa sannan yace, "I see. Yanzu to ki shiga gida. Deal d'in mu zai fara daga yau. Bye ki kular min da kanki." Sarah bata san lokacin da tace, "Bye" ba har da d'aga masa hannu. Sai bayan ta shiga cikin gida sai haushin kanta ya kamata. _Khalil_ kai tsaye gida ya nufa, cikin mota sai sak'e-sak'e yake yi na yanda zai tari Hajiya da maganar Sarah. Ya san dai akwai k'ura. Shi yafi jin nata ma akan nasu Uncles d'insa. Don idan har ta amince, to shafawa idanunsa toka zai yi. Ai ba wani zai zauna masa da matar ba. Beside shi ya lalata masu yarinya don haka shi zai d'auki abunsa. Horn yayi mai gadi ya wangale masa gate ya shigo. Sai da tayi parking mai kyau sannan ya fito daga motar. Gani Honda anyi parking d'insa daga gefen motarsa, ya saki siririn tsaki don ya shaida ko su wanene suka zo gidan. Kamar ba zai shiga ba, sai kuma ya doshi hanyar cikin gida amma ta baya ta yanda babu wanda zai fahimci ya dawo gidan. Sai dai abunda bai sani ba, tun shigowarsa Uncle Ameeru ya gansa, don shi ya fito harabar gidan domin amsa waya. Kuma yana kallonsa lokacin da yabi ta baya ya shige cikin gidan zuwa d'akinsa. A fusace Uncle Ameeru ya shiga ciki tare da Fad'in, "Bilkisu! Bilkisu!! Wallahi babu abunda za muce maki sai Allah ya isa! Yanzu tsabar yanda baki nunawa _Ibrahim_ mahimmancin mu ba matsayinmu na k'annai da yayyin mahaifinsa, shine zai dawo cikin gidan na don bai son ya ganmu sai ya zagaya ta baya ya shige ciki. Na san ma kece zaki kira sa a waya ki fad'a masa mun zo don ya doje mana. Wallahi Bilkisu ki kiyayi kanki damu. Kuma yanzu-yanzu ki tashi ki wuce ki kira mana shi dan ubansa." Hajiya da ranta yayi mugun b'aci da abunda _Khalil_ yayi, mik'ewa tayi tare da fad'in, "Kuyi hak'uri dan Allah. Bari na kira sa." Tana gama fad'in haka ta nufi wani corridor da zai sadata da matattakar da zai kai ta d'akin _Khalil_ d'in. _Khalil_ na shiga d'aki ya zauna bakin gado tare da kai hannu ya jawo side drawer ya d'auko *_MASTIKA GUM_* ya jefa a baki ya hau tauna yana mai kwanciya rigingine tare da saka hannayensa biyu ya tallabo kansa yana tunanin hanyar da zai bi yayiwa Hajiya bayanin Sarah da kuma cikin dake jikinta. Ya san Hajiya sai ta kusa kashesa da masifa. Don da ana aro baki, sai ta aro tabbas. Da ace mahaifinsa nada rai ne, to da worse kenan, don ko da ace zai amince ayi auren, to sai ya kullesa a prison ko da na sati biyu ne tukun. He's father *_Nurudden Muhammad Ibrahim_* was the chief justice of Nigeria (CJN) before he died. Yana da mahaukatan kud'i wanda kwakwalwa ba zai d'auka ba. Sam baya d'aukar raini da rashin adalci. He raised all his children very well. "I really miss you papa. I miss everything about you daddy. Allah ya jik'anka da rahama ya gafarta maka." Yana fad'in haka ya lumshe idanu siraran hawaye na zubowa daga idanunsa. Dai-dai nan jai ana danna doorbell da k'arfi. Da sauri ya tashi zaune yana kallon k'ofar. Wani abu ya danna daga gefen gadonsa, sai ga hoton Hajiya b'aro-b'aro ajikin wani screen dake saman k'ofarsa. Kai baza ka tab'a ganin screen d'in ba sai idan shi ya danna wannan madannin. Da sauri ya sauka daga kan gadon tare da isa wajen k'ofar ya bud'e. Ido hud'u suka yi da Hajiya ranta a mugun b'ace. "Ai sai ka fito tun da kai a rayuwarwa kafi so kaga raina yana ta b'aci." Tana gama fad'in haka ta juya tabi corridor d'in da ta biyo. Shima bayanta yabi don yasan dama tatsuniyar gizo bata wuce ta k'ok'i. Fuska babu yabo babu fallasa ya isa parlor. A zazzaune ya taras da gaba dayansu su biyar k'annai da yayyin mahaifinsa. Zama yayi a kan carpet tare da fad'in, "Barkan ku da zuwa Uncles." Uncle Ameeru ya kallesa tare da fad'in, "Kalle ni, ungo nan!" Ya fad'i haka tare da yi masa dak'uwa............
Chapter 22 · 0% Book details