Sashe 79
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Numfashinta ne ya soma ɗauke, idanuwanta kuma suka soma rufewa ga wani irin azababbiyar azabar da take ji a ƙasanta. Hannu ta kai ƙasanta ta kuma taɓo gashin kan babynta daya soma turowa, wani irin ƙarfine ya kuma zuwa mata, da ƙarfi ta furta, "La'ilaha illalah Muhammadur Rasulullah, Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Take taji kamar hannun da ya shaƙi wuyarta an janye shi da ƙarfi, a wani irin nishi tayi mai ƙarfi daidai lokacin da Khalil ya turo ƙofar, da gudu ya ƙarisa tare da taro babyn da yayi fut ya fito, idanunta ne ya soma rufewa kuma ga wani kan babyn na ƙoƙarin fitowa amma kuma ƙarfinta ya soma ƙarewa saboda wahalar da tasha, cinyarta ya soma bugu bayan ya ajiye jaririn dake tsandara kuka akan gado, cicibarta yayi ya kwantar akan resting chair ɗin dake ɗakin ya soma ƙoƙarin cetonta, da taimakonsa Sarah ta kuma sunkuto ɗayan jaririn, yana fitowa ita kuwa ta sume. Rasa inda zai saka kansa yayi, sai ya mance gaba ɗaya taimakon da zai yi mata, da sauri ya fita daga ɗakin ya koma nashi ɗakin ya dawo hannunsa ɗauke da sabuwar reza ya yanke cibin yaran, basu da muguwar ƙanƙanta kamar ba bakwainiba, kuma dukansu maza kamar Khalil ɗin yayi kaki. Ruwa ya shafawa Sarah a fuskanta yana goga tafin ƙafarta har ta farfaɗo, rungumeta yayi tare da faɗin, "Kin gama min komai Sarah, thank you, thank you Soo much mine, mai kike so a duniyar nan inyi maki shi yanzu nan?" Murmushi tayi tare da faɗin, "Ka cigaba da sona har bayan raina, kar ka juya min baya a kowani irin hali!" Ta ƙarisa maganar tana mai shafa fuskansa. Hannu ya kama yayi kissing sannan yace, "Kin riga kin daɗe da samun wannan Sarah, Khalil naki ne ke ɗaya har abada. Tashi mu tafi asibiti a duba min ke." Aina'u gudu take yi akan titi kamar mahaukaciya domin Sarah na fara salati hotonta ya ɓace a tafin hannunta na _Hell Ofulafu_ da wannan mummunar halittar ya bayyana gaba ɗaya fuskansu ɓutu-ɓutu, mummunar halittar nan ya soma magana da ƙarfi, "Kar ki kuskura ki bari a fita da jariran nan daga gidan nan, idan ba haka ba zaki fuskanci hukunci har na tsawon shekara ɗaya, Hell ba zai ƙara amsa buƙatunki ba, don idan har suka bar gidan, jinin jariran bazai shawu ma Hell ba, kasancewar sun shaƙi iskar waje." Yana gama faɗin haka suka ɓace ita kuma ta hau buga uban sauri, cikin ikon ubangiji duk keken da ta tsayar sai yace mata ba zai je unguwar ba. Kawai sai ta hau gudu kamar mahaukaciya a kan titi. Khalil fita yayi ya nufi ɗakin Hajiya jikinsa har rawa yake yi tsabar murna, murɗa handle ɗin yayi don ƙofar a rufe take, tun da Aina'u ta nufi Abi, Hajiya ta tsiri rufe shashinta, shiga yayi amma babu kowa a parlour, kai tsaye ɗakin hajiyan ya nufa, zaune ya same su ita da Laure sun yi jigum-jigum. "Hajiya Sarah ta sauka! Kin samu mazaje har biyu!" Out of excitement ya faɗi. Hajiya ta mance rabon da tayi murna a rayuwarta irin yau, Laure kuwa kuka ta fashe dashi tare da fita da gudu ta nufi part ɗin Khalil ɗin, so take tayi magana ta nunawa Khalil irin farin cikin da take ciki, amma kuma babu bakin maganar, Hajiya Kuma ƙasa ta nufa tare da yin sujada sannan ta ɗago tare da fashewa da kuka tana faɗin, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah ubangiji ya raya bisa sunnar ma'aiki ya kuma karesu daga dukkan sharrin mutum da aljan. Muje Mu'azzam inga jikokin nawa!" Ta ƙarisa maganar tana mai share hawaye. "Hajiya ai ɗauki hijjab ɗinki kawai don daga nan asibiti muka yi. Yaran da uwar suna buƙatar kulawar likitoci." Juyawa Hajiya tayi ta ɗauki hijjab har da na Laure sannan tabi bayan Khalil, a can ɗaki kuwa, Laure har ta soma gyara jinin Sarah da ya lalata ɗakin, abun mamaki kuma babu tsutsa ko ɗaya. Hajiya ɗaukar ƴaƴan tayi duka biyun ta rungume a jikinta tana jin wani irin ƙaunarsu na ratsa jikinta, "Sannu kinji, Allah yayi maki albarka uwata, sannu da ƙoƙari." Murmushi kawai Sarah tayi tare da sunkuyar da kai ƙasa. "Ɗauko mata mayafinta mu wuce asibitin." Faɗin Hajiya tana kallon Khalil ɗin, da sauri ya ɗauko hijjab a cikin wardrobe ya saka mata tare da miƙar da ita tsaye sannan ya ɗauko silipas ya saka mata. Sai da Hajiya ta saka masu kayan sanyi sannan ta miƙawa Khalil Hassan yayi masa kiran sallah a kunna tare da yi masa huɗuba da sunansa, (Ibrahim Khalil) Hussaini kuma ya saka masa sunan mahaifin Sarah (Nuhu). Hajiya riƙe da Hassan, Laure kuma ɗauke da Hussain suka fita daga ɗakin, Khalil ya kama hannun Sarah suka sauka ƙasa tare da fita daga ɗakin gaba ɗaya suka nufi parking space. A gidan baya ta zauna ita da Hajiya, shi kuma da Laure a gaba, kamar ance ya kalli ƙasa, sai ya hango kwalin _Mastika gum_ a ƙasa, da sauri ya kai hannu ya ɗauko tare da ɓare kwalin ya ɗau ɗaya ya jefa a baki yana murmushi don har ya manta rabon daya kai chewing gum bakinsa. Suna fita daga gidan keke napep ɗin da Aina'u ke ciki ya tsaya, zuciyarta sai da tayi wani irin tsalle ganin motar Khalil ya fito daga cikin gida, ko kamun ta yunkura motar Khalil ta kusa bakin titi don gidan yana gaba da titi ne. Haɗa kai tayi da guiwa tare da fashewa da kukan baƙin ciki. Juyowa mai napep ɗin yayi tare da faɗin, "Lafiya baiwar Allah?" Ba tare da tace komai ba ta fito daga napep ɗin saboda tsabar rashin imani ta bugi goshinsa da tafin hannunta tare da faɗin, " _Hell_ ga jinin wannan matsayin sassaucin hukuncinka gareni." Da sauri mai napep ɗin nan yaja kekensa ya bar layin don ya tsorata da abinda Aina'u tace, sai dai yana zuwa titin bypass, trailer tabi ta kansa. Aina'u kuwa shiga cikin gidan tayi rai a mugun ɓace ta nufi side ɗin Hajiya. A can asibiti kuwa, jariran a incubator aka saka su sannan itama uwar aka shiga kula da jikinta, sai dai aka mata ɗinki uku sannan aka saka mata ƙarin ruwa domin taji ƙarfin jikinta. Hajiya kuwa ta ɗauki waya ta dunga kiran dangi da abokan arziki tana shaida masu matar Khalil ta samu ƙaruwan ƴan biyu. Khalil kuwa bayan Sarah ta samu barci, sai ya sulale ya fita domin zuwa can gidansu Sarah ya shaida masu Sarah ta haihu. Wajajen ƙarfe goman Safiya, gaba ɗaya suna zaune tsakar gida suna karyawa, Na'ima ta kalli Lami tare da faɗin, "Lami baza ki duba baba? Tun safe ban ni ɗuriyarsa ba, ko wa'azin da ya saba kunnawa banji ya kunna ba." Taɓe baki tayi tare da faɗin, "Yesu ne yayi min maganinsa! Ai ba ƙaramin addu'a nake yi ba akan Nuhu ya daina kashe mana kunne da wannan karatu da wa'azin nan da yake saka mana ba, har fata nake Allah yasa Tv ɗin ya lalace ko kuma ya faɗo daga saman ya fashe." Miƙewa Na'ima tayi tare da nufa ɗakin baban ta ɗaga labule, wani irin ihuu ta saka tare da faɗin, "Baba ya mutu mun shiga uku!" Ai a sittin daga Lamin har sauran suka nufo ɗakin don ganin halin da yake ciki. Gashi nan dai kamar me rai kamar kuma gawa! Baki a karkace, hannu a lankwashe, ƙafa ɗaya da hannu a shanye. "Yes......" Da ƙarfi Hassana tace, "Dalla Lami ki rufe mana baki, baba na cikin wannan halin shine kike ƙoƙarin kira mana Yesu, Allah dai ya tsinewa wannan addini da kika koma!" Da sauri Lami tace, "Zan ci ubanki idan kika zagi addinina, ai gwara ni kowa yasan ba addinin sallah nake yi ba, kuma duk Sunday sai naje Church, ku Kuma fa? Sai dai kullum ayi ta faɗi a baki mu musulmai ne, amma ko sau ɗaya ba'a yin sallar!" A fusace Marfu'a tace, "Dan Allah Lami ku bar wannan maganar aji da lafiyar baba." Daidai nan suka jiyo sallamar Khalil a ƙofar gida don tun yana hanya yake kiran layin baba amma ba'a ɗagawa kasancewar bargo ya rufe wayar shiyasa su Aina'u basu ji ringing ɗin ba. "Kamar muryan mijin Sarah!" Faɗin Na'ima tare da fitowa daga ɗakin ta nufi kwar gida, "Alhamdulillah!" Faɗin Na'ima bayan taga Khalil ɗin tsaye a ƙofar gida, "Shigo Khalil, Allah ne ya turo mana kai wallahi. Babane babu lafiya yana can kwance gaba ɗaya rabin jikinsa ya shanye." Da sauri yace, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Tare da gitta Na'iman ya wuce ciki da sauri. Hassana da Marfu'a sai sharan hawaye suke yi ganin kamar babu rai a jikin baban, suna ganin Khalil suka matsa suka bashi hanya. Cicciɓan baba yayi tare da fito dashi daga ɗakin ya nufi mota, gaba ɗaya suka rufa masa baya har da Lami wacce ko arzikin mayafi babu a jikinta, hatta su Na'iman ma babu mayafin a jikinsu. Lami, baba Hassana da Marfu'a a baya, Na'ima kuma ta zauna gaba ita da Nuratu. Sai da suka hau titi sannan Khalil ya ɗan juyo ya kalli Lami tare da faɗin, "Mama, Sarah ta sauka, ta samu ƴan biyu duk maza yau da safe, dan girman Allah kar a faɗa mata halin da baba yake ciki don itama tana can asibitin ita da yaran don an saka su a kwalba ne kasancewar basu isa watannin haihuwa ba." Gaba ɗayansu cike da mamaki da kuma farin ciki suka furta, "Ƴan biyu! Inna lillahi, Hassana ashe Sarah ce zata riga ki." Na'ima ta ƙarisa da faɗin haka, Lami kuwa cewa tayi, "Yesu Almasihu nagode maka da wannan kyauta da kai min, a lokacin da ka kwace lafiyan mijina, sai kayi min kyauta da jika har biyu." Tana gama faɗin haka sai ta hau waƙa, " _Yayi! Yayi!! Yesu yayi!!! Yayi, yayi...._" "Ke dallah Lami ana jimamin halin baba kin zo kin wani dame mu da zancen banza! Yesun me? Mu Allah ne zai cecemu ba wani yesunki ba!" Faɗin Marfu'a dake kusa da ita. Lami kuwa sai da ta saka bayan hannu ta bugi Marfu'an sannan tace, " _Ya Allah mai-iko duka, Uban Ubangijinmu Isa Almasihu, wanda ba ya son mutuwar mai-zunubi ba, amma ya