Sashe 57
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri Sarah ta ƙariso wajen tana faɗin, "Lah, Ai'n kece? Shigo mana kin tsaya a waje kamar baƙuwa. Ke ɗaya ce?" Hanya Khalil ya bata ta shigo tare da faɗin, "Bamu san da zuwanki ba, ashe kina tafe" kai tsaye yayi maganar don har ga Allah bai so zuwanta ba don zata shiga haƙƙinsa na rashin bashi damar kasancewa da matarsa. Da kallo ta bishi tana ji kamar rungumesa saboda ƙaunarsa dake fuzgarta. Shi kuwa Khalil komawa yayi ya zauna tare da ɗaukar remote ya kunna tv ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya. "Ai'n mai zaki ci? Ki zauna mana." Wani kallo Khalil ya watsawa Ai'n ɗin tare da maida kallonsa izuwa ga Sarah yace, "Babe, ba girkin da za kiyi, saboda ban so kiyi stressing kanki shiyasa na fita da kaina na haɗa maki breakfast. Ohh nama manta, akwai sauran abincin da Aunty Maryam ta aiko mana dashi gashi can a dining. She should go and serve herself kamun mu dawo daga cikin gida wajen hajiya. Let go wife!" Ya faɗi hakan tare da kama hannun Sarah ya saka cikin nashi. Kallonta Sarah tayi tare da faɗin, "Aina'u bari muje mu dawo. Hajiya zanje na gaisar in dawo yanzu." Yaƙe tayi tare da faɗin, "Ok sai kun dawo." Suna fita Khalil ya saki tsaki tare da faɗin, "Killjoy?" "Wa?" Sarah ta tambaya tana kallonsa. "Ƙanwarki mana. Bata iya zuwa gidan amare ba. Ita da ake bari sai irin bayan sati biyun nan, duba fa ki gani ko 12:00 bai yi ba. Ni dai wallahi an shiga haƙƙina. Ɗaukar hutun wata guda nayi domin in huta tare da matata, amma naga alama ana son hanani more amarcina." Tsungulinsa tayi a hannu har sai da ya furta, "Auch! Mai nayi maki?" "Duk fa wanda zai zo ba kwana zai yi ba, dole zai tafi ya bar mu tare, to menene abun damuwar bayan we will always sleep together babu mai raba mu?" Cak ya tsaya yana kallonta tare da faɗin, "Haba, dagaske? Za ki biyani duk bashin soyayyar da aka hanani nunawa da ranar?" Dukan kafaɗunsa tayi tare da faɗin, "Wallahi happiness kana da negative mind. Ni ba abunda nake nufi kenan ba." "To ni kuma kinga abunda nake nufi kenan." Faɗin Khalil. Da sauri tayi gaba saboda kunyar da ya bata. Haɗawa yayi da gudu ya isketa tare da faɗin, "Yarinya kina da aiki, wai kunyata kike ji? Taɓ, kina ruwa can gaban breaker." Cak ta tsaya kasancewar sun iso daidai ƙofar part ɗin Hajiya. Shi ya ƙarisa tare da murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da sallama. Gaba ɗayansu suna parlour ana hira, Hajiya, yaya Abdul-Hakeem, yaya Muhammad Kabir, Aunty Maryam, aunty Khairat, aunty Zakiyyah matar yaya Abdullahi, Nafeesa, Aysha, Laure, Aunty Jamila autarsu uncle Ameeru, sai ƴaƴansu da kuma kaɗan daga cikin sauran mutanen Maiduguri da basu koma ba. Juyawa Khalil yayi tare da faɗin, "Babe, shigo mana." Da sauri Aunty Khairat ta tsunguli aunty Maryam jin sunan da Khalil ya kira Sarah dashi suka bushe da dariya. Ita kuwa Sarah a kunyace ta shigo ɗakin kanta na kallon ƙasa ƙafafuwanta na harɗewa. Har ƙasa ta duƙa tare da faɗin, "Hajiya ina kwana?" Da murmushi a fuskar hajiya ta amsa tare da faɗin, "Zo taho nan kinji ƴata." Zama tayi kusa da ƙafafun Hajiya a kan capet sannan tabi kowa ɗaya bayan ɗaya ta gaida su, kowa ya amsa fuska cike da fara'a babu nuna wani kyara ko wulaƙanci. Khalil ɗin ma gaida waɗanda suka girme shi yayi, wanda ya girma kuma suka gaida shi. "Yayanmu ka iya zaɓe fa wallahi." Faɗin Nafeesa tana ƙara leƙo fuskan Sarah. "Kun san ni komai nawa mai kyau ne shiyasa matata sai da na hanga na waiga na zaɓota zuƙeƙiya gata nan." Aunty Zakiyyah matar ya Abdullahi tace, "Gaskiya Ibrahim baka da kunya, a gaban yayyin naka nake irin wannan magana haka." "To Aunty kuma ni mai nace? Yabon matata fa kawai nayi." Faɗin Khalil yana dariya. "Wai, Hajiya sai kinyi haƙuri don zaki ga rawar kai!" Gaba ɗaya aka kwashe da dariya. Saukowa ƙasa Khalil yayi tare da zama daidai inda Sarah take sannan yace, "Wife, na san baki san kowa a nan wajen ba idan aka cire Laure da tazo ɗakinmu ɗazu. Bari na fara ta kan wannan babbar aunty, (yayi nuni zuwa ga Aunty Zakiyyah), ita ce matar babban wanmu, sojane a Abuja yake aiki. Lokacin da papa yake dai rai, we all are living there duk dani zaman na hutune don a abroad nayi rayuwata kaf, Hajiya ce ta matsa na dawo saboda Allah ya rubuta sai na haɗu dake mun ƙunla alaƙa mai girma. Last year suka aurar da second daughter ɗinsu mai sunan Hajiya ana kiranta little hajjaju, very smart girl don ni ta biyo a kwakwalwa." "Ai ka san mu duka kwakwalan tunkiyoyi gare mu sai kai ɗan gwal" Faɗin yaya barrister. Waro idanu Khalil yayi tare da faɗin, "Ni ba haka nake nufi ba. Mine saurareni kiji." Ya ƙarisa maganar yana kallon Sarah, "Wannan sunansa ya Abdul-Hakeem, wannan itace matarsa Aunty Maryam wacce ta aiko mana da breakfast ɗazu, ƴarsu ɗaya Maimoon... Wannan kuma shine ya barrister, shi kuma kin ga matarsa nan, sunanta Aunty Khairat, ƴaƴansu biyu...." Haka ya dunga nuna mutanan parlour ɗin yana mata bayani. Ita dai kai kawai take ɗaga masa. Yanda aka amsheta kowa na nan-nan da ita ya saka ta mance da wata Aina'u. Shikuwa Khalil yana sane, addu'a kawai yake yi cikin zuciyarsa Allah yasa ta gaji da jira ta wuce gida. Ɓangaren Aina'u kuwa, bayan fitarsu babu inda bata buɗe ta duba ba, sai faɗin, "Kan bala'iiii!" Kawai take yi tana kwafa. Sai da ta gama tsaf sannan ta dawo parlour ta zauna a kan kujera tana girgije-girgije ƙafa, "Wallahi in har sunana Aina'u ɗiyar Lami da Nuhu, wallahi tallahi ba zan taɓa bari kiyi farin ciki ba, ba dai anyi auren ba, enjoy the first week of your marriage before the war begins!" Ta ƙarisa maganar tana mai rausayar da kai. Tun tana ƙirga mintuna har ta dawo awa. A can cikin gida kuwa, kirar sallar azahar ne ya fitar da mazan zuwa masallaci yayin da matan suka ɗauro alwala. Bayan kowa ya idar da Sallah, sai suka haɗu gaba ɗaya a dinning don har an kammala lunch. Kujerun dinning ɗin irin mai sha huɗu ne, kuma sun ɗauke gaba ɗaya don ma yaran an haɗa masu a parlour don suna da yawa. Khalil ƙafa ya tura ya shafo ƙafar Sarah, ɗagowa tayi suka haɗa idanu ya kashe mata idanu, gaba ɗaya a idanun Hajiya komai ya faru amma sai ta nuna kamar bata ga komai ba ta cigaba da cin abincinta. Zumbur Sarah ta miƙe tana faɗin, "Inna lillahi!" Gaba ɗaya aka haɗa baki wajen faɗin, "Mai ya faru?" Khalil kuwa har ya zagaya ta bayanta tare da jan kujeran da take kai baya. "Na manta ina da baƙuwa a ɗaki. Kuma tun ɗazu tana can tana jirana." Hajiya tace, "Laure maza haɗo mata abinci a basket ki tafin mata dashi." Khalil kuwa tsaki yayi a zuciyarsa don bai so ta tuna ba. Shima abincin da bai ƙarisa ci kenan ba yabi bayan matarsa. Kowa Sarah ta murɗa handle ta shiga, a zuciye Aina'u ta juyo zata fara ruwan bala'i sai ga Khalil ya shigo rai ɓutu-ɓutu. Washe baki Ai'n tayi tare da faɗin, "Kun jima, har nayi bacci na farka. Amma dai mancewa kuka yi nazo ko?" Ko kamun Sarah tayi magana caraf Khalil yace, "Ni na ɗauka ma kin wuce ai. Ashe kina nan kina jira." Sarah tace, "Kiyi haƙuri Aina'u wallahi mancewa nayi kina nan. Kinci abincin?" "Ban sani ba shegiya munafuka. Wato kin shigo cikin arziki har kin soma wulaƙanci. Kiyi, lokacinki ne. Nawa na nan zuwa." A Cikin zuciya tayi maganar, amma a zahiri sai cewa tayi, "Naci!" Sama Khalil ya hau yana faɗin, "Love, ɗauko min energy drink a fridge ki kawo min sama." Da "To" ta amsa tare da nufar kitchen ɗin. Da wani irin kallo mai tattare da shauƙi Ai'n tabi bayan Khalil. Sarah kuwa kitchen ta shige ta ɗauko drink ɗin ta dawo parlour tare da faɗin, "Aina'u ina zuwa dan Allah. Bari na kai masa na dawo." Ko tari Aina'u bata yi ba. Sarah kuwa dama bata jira cewarta ba ta nufi sama, kwance ta same shi daga shi sai boxer yana danna waya. Yana jin shigowar ta ya ajiye wayar tare da miƙa mata hannu alamar ta taho garesa. Sai da ta ɗan yi jim sannan tayi taku ta isa gareshi. Janyota yayi gaba ɗaya ta faɗo jikinsa ya saka hannu biyu ya rungume tare da faɗin, "Taho inji ɗumin jikinki matata." Ya ƙarisa maganar yana sunsunar wuyarta. "Dan Allah ka sake ni, Aina'u fa tana parlour." Hannu ya kai ya cire ɗan kwalin kanta ya cusa hannunsa cikin gashinta tare da faɗin, "Duk wacce tazo gidan amare ai ta san hakan zai iya faruwa da ita, ni kuma saboda wata Aina'u ba zan ƙi hutawa da matata ba." Ya ƙarisa maganar tare da murginata yayi mata rumfa yana kallon kyakkyawar fuskanta. "Waiyy! Nauyi gareka, ɗaga ni." Ta faɗi duk da kuwa be sakar mata nauyi ba. Jin abunda tace sai ya ɗan sakar mata kashi talatin a cikin nauyin nasa. Da sauri ta shiga bugun bayansa tana faɗin, "Nauyi, nauyi, nauyi! Wallahi ka sakar min nauyi." "Au haba, dagaske?" Kukan shagwaɓa ta sakar masa tana tsungulin damtsensa. Juyawa yayi ta koma samansa tare da zagaye ƙugunta da hannunsa ya matso da kansa ya haɗe bakinsu ya shiga bata deep kiss, Sarah kuwa sai mutsu-mutsu take zata kwace kanta yayi saurin juyata ta koma ƙasa yayi mata runfa ya shiga bata zazzafan romance, tun tana noƙewa har ta saki jikinta ba tare da ta shirya ba ta shiga mayar da martani. Sai da komai ya kammala ta shiga kukan shagwaɓa tana faɗin zafi. Shi kuwa ya biye mata yana ta lallashi. Tare suka yi wanka wanda a can bayin ma sai da suka ɓata lokaci, suna fitowa daga bayi ana kwaɗa kiran sallar la'asar. Sauri-sauri ya shirya ya fita gudun kar yayi missing ɗin sallah. Turus ya tsaya ganin Aina'u a zaune ta cika tayi faam, shi har ga