← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 112

Sashe 64

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu haka Hajiya ta koreni daga gidan nan saboda na faɗa mata gaskiya abunda take yi bata kyautawa. Yanzu hakan sarƙan nan bata nan na ɗauko shi na kawo maki ba. Nasan za kiyi mamaki mai yasa na tona mata asiri tana matsayin ƴar uwata, to nayi hakan ne saboda na tseratar da ita ganin tayi aure gidan mutunci, bana so aurenta ya mutu sanadin abubuwan da take aikatawa. Shi kansa Khalil ɗin ba jin daɗin zama da ita yake yi ba, a wannan ɗan zaman da nayi na fuskanci haka, kullum cikin ƙorafi take yi masa akan dole sai ya saya mata gida a wani waje ita bata san zama waje ɗaya da uwar miji da matar ƙani ko wa, tafi son zama ita kaɗai ta wala. Hajiya baki ga irin ɓarnar kuɗin da Sarah take yi ba da dukiyar ɗanki, duk abunda tace kamar ta shanye shi, jiki na rawa yake yi mata. Hajiya sai fa kun tashi tsaye sosai akan Khalil!" Hajiya baki sake take bin Aina'u da kallo tana mamakin ƙaramar yarinya irin wannan da hassada da kuma iya tsaro zantukan ƙanzon kurege, don tun daga furucinta na farko ta fuskanci inda ta dosa, babu abunda ke damunta illa tsantsan hassada da mugun hali. "Ina so tambayarki." Hajiya ta faɗi still tana kallon Aina'un. Gyara zama Aina'u tayi har da matsar hawaye tare da faɗin, "Ina jinki Hajiya." "Ke da Saratu uwa ɗaya uba ɗaya kuke?" Jinjina kai Aina'u tayi tare da faɗin, "Uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya da ita Hajiya, halin ne kawai ba ɗaya ba." Hajiya tsuke fuska tayi tare da faɗin, "Tabbas kuwa hali ba ɗaya ba. Amma Allah yayi wadaran naka ya lalace! Yanzu saboda lalacewa da rashin hankali da tunani, ƴar uwarki ciki ɗaya kike yiwa baƙin ciki da hassada? Duk wani mai hankali idan yaji wannan magana da kika yi ya san cewa ke munafuka ce kuma baki ƙaunar ƴar uwarki. Ina matsayin uwar mijinta, shine zaki zo kina faɗamin maganganun ɓatanci akan ƴar uwarki saboda naji haushinta! To ki sani, na san wacece Saratu, tun lokacin da aka kawota cikin gidan nan nake lura tare da karantarta, yarinya ce mai natsuwa da hankali. Laure kuma shekaru bakwai kenan muna tare da ita, bata taɓa ɗaukar min ko mayafi ba balle kuma sarƙa. Bata ma san darajarsa, kuma yanda nasan tarbiyyarta da halinta baza ta taɓa amincewa a haɗa baki da ita ba domin a cutar dani. Kuma ni tun ɗazu na fahimci ke kika ɗau sarƙoƙin nan saboda yanda kika riƙa tada jijiyoyin wuya, na rabu dake ne domin inga iya gudun ruwanki don na riga na san baza su taɓa saiduwar maki ba duk inda za kije don sai kin bata risiti (receipt). Kalle ni da kyau, mahaifiyarki ma na haifeta, baki isa kiyi min makirci da wayau ba, kuma auren Khalil da uwata Saratu, mutuwace zata raba shi in Sha Allah. Ba Saratu da take ƴar uwarki ba, Ni kai na mahaifiyar Khalil ban amince ki ƙara tako ƙafarki cikin gidan nan ba. Kuma kin san dai ina da ƴaƴa hukumomi ko? Tashi ki ɓace min da gani tun kamun na wanke fuskanki da mari!" Aina'u da baƙin ciki tarkon da ta ɗana bai kama ba ta miƙe tana yiwa Hajiya wani irin kallo sannan ta juya fuuu ta fita tare da rufo ƙofar da ƙarfi. Laure na zaune ta zubawa talabijin idanu taji saukar mahaukacin rankwashi a tsakiyar ka sai da ta kwanta flat a ƙasa tsabar gigicewa. Dawowa tayi daidai kanta tare da faɗin, "Sai na zama ajalinki, shegiya mummuna!" Tana baro part ɗin ta tsaya tana mamaki domin bata taɓa kawowa a ranta wannan makircin da ta haɗa ba zai yi aiki ba. "Hajiya kin jawowa kanki bala'i da masifa da tashin hankali! Kin yi kuskure tura hannunki a ramin maciji kuma wallahi sai ya ɗanɗana maki zafin dafinsa...." Tana gama faɗin haka ta ja akwatinta ta wuce ta bar gidan. Bayan fitar Aina'u a ɗakin Hajiya, Hajiya ta zabga tagumi tare da faɗin, "Duniya ina zaki damu ne? Ɗan uwanka ciki ɗaya amma shine ke yi maka hassada da baƙin ciki, kai Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allah kasa mu cika da imani, Saratu ce dai zama daram dam a gidan nan in Sha Allah!" Wani ajiyar zuciya Sarah ta saki lokacin da ta tabbatar Aina'u ta bar gidan. Kitchen ta shiga domin haɗawa Khalil abinci don ya kusa dawowa. Bayan ta kammala girkin ta haura sama ta cancaɗa wanka ta saka wata doguwar rigar shadda pink colour wanda yasha aiki da baƙin zare, ɗaurin ɗan kwali tayi mai kyau sannan ta fesa turare ta ƙara kallon fuskanta a madubi ta saki murmushi tare da fita ta sauko ƙasa ta zauna a kan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya tana kallon tanƙameman plasma tv ɗinta dake haska film ɗin _Mohabbatain_ a tashar Bollywood. Da sauri ta miƙe jin ƙarar door bell, buɗe Ƙofar tayi tana kallonsa. Shima kallon nata yake yi daga sama har ƙasa yana faɗin "Ma sha Allah!" Cikin zuciyarsa. Hannu ta kai ta karɓi jacket ɗin hannunsa da ya ratayo tare da kai bakinta saitin kumatunsa ta sakar masa kiss tare hura masa fuska tace, "Kar fa a cinye ni." Hannu ya kai zai cafkota tayi saurin ja baya tana dariya, "Ki tsaya ki gani idan ba'a cinyekin ba." Gwalo tayi masa tare da faɗin, "Ka kama ni idan zaka iy....." Ko kamun ta rufe baki har ya iso inda take ya cafki hannunta biyu tare da haɗata da ƙirjinsa yana mai faɗin, "Ni da zan iya haɗiye kin ma da na huta da kewarki, kullum na fita aiki sai kin hanani sukuni, domin da zarar na bar gida, kece kike min gizo a ko ina." Hannun ta saka ta rungumosa tare da faɗin, "To ni dai matsalata kar dai garin yi maka gizo kaje kaga wata macen ka ɗauka nice kawai kace mata, Ina son ki! Tabbas zuciyata zata buga daga nan." Janyeta yayi daga jikinsa tare da kama hannunta suka nufi sama yana mai faɗin, "Wannan kalmar mai tsada ga macen biyu kawai nake furtawa, Hajiya da kuma ke, bayan ku, babu macen nan gaskiya." Ƙanƙame hannunsa tayi tare da faɗin, "Ina son ka, ina sonka sosai." Bakinsa ya kai dai-dai kunnanta tare da faɗin, "Muje ciki a nuna min!" Tsungulinsa tayi a damtsensa tare da yin dariya. Bayan kwana biyu, Khalil ya fahimci Aina'u bata gidan, hakan ba ƙaramin daɗi yayi masa ba, amma ko a fuska bai nunawa Sarah ba, kuma bai taɓa yi mata maganar ya akai baya ganin Aina'un ba, ita ma kuma bata yi masa maganar ba. "Aunty Rose Merry, ina son don Allah ki kai ni wajen _Hell Ofulafula_ da kike bani labarinsa, amma kar ki bari ko Lami ta sani, ya zama sirri tsakanin mu kamar yanda muka saba." Aina'u ta faɗi bayan ta kamo hannun Aunty Rose Merry ɗin bibbiyu. Aunty Rose Merry da kallon mamaki ta bita tare da faɗin, "Lili mai za kije kiyi a wajen _Hell Ofulafula_? Kin san wanene Hell kuwa? Ko daga jin sunansa kawai ya isa ya firgita ki, ganinsa kuwa, kamar bala'i ne a wajenki." Aunty Rose Merry ta girgiza kai tare da cigaba da faɗin, "Baza ki iya da Hell ba, dokokinsa nada tsauri, bazan baki wannan shawarar ba, domin zai saka ki aikata wani mummunar abu mai girma wanda Yesu Almasihu ba zai yafe maki ba, gwara dai kije wajen _Iya fulowa_, itama ta iya aiki sosai. Wai ma menene za kiyi? Wa kike so ayi wa wani abun!" Faɗin Aunty Rose Merry. Sake hannunta Aina'u tayi tare da ɓata rai ta juya baya tana faɗin, "To shikenan! Amma ni duk abunda kika saka ni, ina yi maki kai tsaye, har babana na cutar saboda ke, amma ni baza ki iya mun ɗan ƙaramin alfarmar nan ba, ashe soyayyar da kike min na ƙarya ne, saboda ke na koma addinin Christian, na kwana arba'in da biyar a cikin ɗakin duhu daga Ni sai pastor William yana min wankan zunubi tare da amfani dani, ya aske min gashin kaina, ya saka na kwanta kamar dabba ina shan nonon kare duk saboda ke, amma shine baza ki iya min wannan ƙaramin abun ba. Shikenan!" Ta ƙarisa maganar tana mai fashewa da kuka. Jawota Aunty Rose Merry tayi tare da faɗin, "Kiyi haƙuri Lili, ba dai _Hell Ofulafu_ kike son zuwa ba?" Gyaɗa kai Aina'u tayi tana share hawayen fuskanta, "To ki kwantar da hankalinki, zan kai ki wajensa, sai dai tafiya ne mai nisa, don a Abia yake can wani ƙauye mai nisan gaske, kuma shi bai jin yaren Hausa, bai jin English, sai Igbo, yoruba da ifem." Wani murmushi Aina'u tayi tare da faɗin, "Wannan ba matsala bane Aunty, ba sai kin raka ni ba, kiyi kwatanci kawai." Shuru Aunty Rose Merry tayi mai tsayi kamun ta saki ajiyar zuciya ta soma zayyano mata kwatanci tsaf har da yanda zata samu tafintan da zai riƙa faɗa mata abunda Hell yace da kuma ita abunda zata ce masa. Bayan kwana biyu Aina'u ta shirya kuɗi tsaf tare da ɗaukar hanyar Abia ba tare da sanin kowa ba idan aka cire aunty Rose Merry, awanni goma sha ɗaya da rabi suka yi a mota kamun suka isa kuma cikin dare. Aina'u ta zauna, ta mike ta rasa inda zata saka kanta saboda gajiyar zaman mota. Taji waƙa a wayarta har na Allah ya isa Kasancewar ta tafi da power bank har taji ya fita a cikin ranta. Hotel ta kama ta kwana, washa gari da sassafe ta nemi wanda Aunty Rose Merry ta Bata number ɗinsa, sai da suka yi ciniki ta bashi 50k kuma ita za tayi masa kuɗin motar zuwa can sannan suka ɗauki shatar mota zuwa *_Asaokpuaja_*. Tafiyar awa Shidda ce ta kai su can, nan ma ɗin mai motar jiransu yayi a bakin wani hanya sabida mota baza ta iya shiga ba, nan ma suka soma cin uban tafiya, sai da suka yi tafiyar awa ɗaya da rabi sannan suka isa wani ƙatoton baƙin gunki wanda aka yi masa penti da jar kala, da mugun gudu Aina'u ta koma bayan Ugo ta ɓoye saboda yanda gunkin ya tsoratata da girmansa,
Chapter 64 · 0% Book details