← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 112

Sashe 95

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta idar da sallar, sai ta jingina da gado tana tunanin Khalil hawaye na zubo mata, hannu ta ɗaga sama tare da faɗin, "Ubangiji mahaliccin sammai da ƙassai, mai kowa mai kome, ga bawanka nan Ibrahim, ka kiyaye shi daga sharri da tsafin Aina'u, ga kwato shi daga hannun azzaluma mara imani Aina'u, ya Hayyu ya Ƙayyumu, alfarman soyayyar dake tsakaninka da mafificin halitta, Muhammadur Rasulullah (SAW) ka ceto mijina daga halakar Aina'u ya rabbis samawati al'ardi." Ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka. Juyawa tayi ta kai hannu kan handbag ɗinta dake kan gado tare da buɗe zip domin ta ɗauko wayarta, a firgice ta soma zazzage jakarta tana neman wayarta mai tsada da Khalil ya canza mata ranar da suka yi celebrating first anniversary ɗinsu bayan haihuwar twins. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Wallahi to duk yanda aka yi a tasha aka sace wayar nan, shikenan I missed everything including our history pictures!!" Faɗin Sarah tana mai fashewa da kuka, don sam ba satar wayar bane yafi tsaya mata a rai, hotuna da videos ɗin dake cikin wayar ne wanda dawowarsu zai yi matuƙar wuya ke mugun bata takaici. Jin alamar ana nufo ɗakin sai tayi saurin goge hawayenta tana mai ƙirƙirar smiling face tana ɗaurawa a nata fuskan. "Assalamu alaikum, Maman twins kin idar?" Faɗin Suhana, ganin Sarah a zaune sai ta juya ta koma parlourn, can sai gata da abincin a rufe a plate, murmushi Sarah tayi mata tare da faɗin, "Nagode Suhan." Murmushin itama Suhan ɗin tayi mata tare da faɗin, "Bari naje parlour wajen su twins, don har yanzu basu gane bake bace ba." Ta faɗi hakane tare da miƙewa ta fita. Bayan fitan ta, Sarah sai ta buɗe plate ɗin, alalen gwangwani ne yaji miyan source da hanta. Guda ɗaya kawai Sarah ta iya ci ta rufe, don da kyar take haɗiyewa saboda damuwar dake cinta a rai, data rufe idanunta, Khalil kawai take gani yana yi mata gizo, idan ta tuna lokacin da suke farin ciki kamun zuwan Aina'u, sai taji daɗi har sai hakan ya bayyana a fuskanta, idan kuma ta tuna baƙin cikin da Aina'u ta ƙunsa mata, sai taji hawaye na wanke fuskanta. Wani ƙaramin ƙur'ani ta gani irin mai zip ɗin nan a side drawer, hannu ta kai ta ɗauko tare da zuge zip ɗin ƙasa, ajiyar zuciya ta saki tana mai ƙoƙarin tuna when last ta riƙe ƙur'ani a hannunta ta karanta, kuka ta fashe dashi ganin ta kasa tuna wani lokaci ne na ƙarshe data ɗauki Qur'ani domin karatu, ko a can gida sai dai idan zata goge ta saka masa turare take ɗauka, amma bayan haka kam, bata ɗauka domin niyyar karatu, har akai azumi guda biyun da tayi a gidan Khalil, bata taɓa karatun ƙur'ani ba, sai dai ana yin asham wani lokacin har da tahajjut kasancewar masallacin a cikin gidansu Khalil ɗin yake, "Dole ko mai aka yi mana ya kama mu tunda mun saki Allah mun kama Duniya!" Faɗin Sarah cikin zuciya. Suratul Yusuf ta buɗe ta soma karantawa don surar na ɗaya daga cikin surorin da take matuƙar so a cikin Alqur'ani don sai da ta haddace tsaf amma rashin muraji'a yasa duk ya zube, suratul Ma'ida, Maryam, Buruj da Nisa'i, don Nisa'i ma gaba ɗaya surar ta haddace ita da Kahfi, don lokacin da suke tashin ƙawance da Muneeba, duk juma'a sai sun sauketa don musaffa suke yi. Sarah bata iya baccin kirki ba, Allah yaso ma Suhan tazo tayi mata sallama a kan tare zasu kwana a ɗayan ɗakin ita da ƴan biyu, ita kuma Sarah anan ta kwana ita kaɗai, sai dai rabi da kwata na cikin daren, raya shi tayi da tsayuwan dare saboda ta kasa baccin. A idanunta akai sallar asubah, abunda yayi matuƙar burgeta a gidan shine, tun bayan saukowar masallaci take jin sautukan ƙira'a mabanbanta na Alkur'ani cikin muryoyin maza da mata ya ɗume gidan, sai kawai itama ta hau karatu da wannan ƙur'anin data gani a ɗakin. Sai ƙarfe takwas daidai taji gidan ya ɗauki tsit, sai itama ta saka aya sannan ta rufe ƙur'anin tana mai yin sujada ɗon ta tsaya ne a kan ayar da ake sujada. Suhan ce ta shigo ita da twins har anyi masu wanka amma sun ƙi yarda ko wando ta saka masu, akwatin kayansu Sarah ta buɗe tare da fiddo kayansu ta mikawa Suhan ɗin tare da rufe akwatin ta miƙe tsaye tana nannaɗe dardumar, "Maman twins ki fito za muje muyi breakfast, you will be shock idan muka shiga side ɗin Nnanne." Ba tare da ta cire hijjab tabi bayan Suhan data rigata fita, Sarah tayi mamaki ganin duk da twins sun ganeta amma basu ƙoƙarin gudu daga wajen Suhan ba duk ƙiwarsu. Bata taras da kowa ba a parlourn, duk sun hallara ɗakin Nnanne, "Ina su Ba Lukman?" Faɗin Sarah, "Suna can ɗakin Nnanne." Suhan ta bata amsa tare da fita both hannunta na ɗauke da twins. "Da kin ajiyesu su taka da ƙafursu, sai baki wahala suke yi." Faɗin Sarah, su kuwa twins najin haka suka ƙare lafewa a jikin Suhan, Suhan Kuma cewa tayi, "Ai wallahi ban sauke su." Dariya kawai Sarah tayi don ta lura Suhan ɗin na matuƙar ƙaunar twins, itama sai taji tana ƙaunar Suhan ɗin. Sun ɗan yi tafiya kamun suka iso sashen Nnanne da yake da girman ban mamaki, ga uban uban takalma birjik a ƙofar ɗakin na maza da kuma na mata. Sallama su Sarah suka yi kamun suka shiga ciki, da maɗaukakin mamaki Sarah ta take kallon jama'ar dake ɗakin suna zazzaune akan ƙatuwar carpet ɗin dake shimfiɗe a ɗakin sun zagaye wata farar tsohuwa mai mugun kwarjini da kuma kamala kasancewar mai riko da ibada, ta tsufa sosai, amma babu ruɗewa a tattare da ita saboda zuciya da gangan jikinta sun ginu ne akan Addinin Allah cikin tafarkin _SUNNAR MA'AIKI SAW_. Suna shigowa gaba ɗaya idanu ya koma kan Sarah da kuma ƴan biyu dake hannun Suhan, gyaran muryan Nnanne tayi, sai koma ya dawo cikin nutsuwarsa don sun san dokar, babu mai magana har sai an kammala cin abinci kamun nan ake gabatar da meeting na tsawon awanni biyu rak, a dunƙule Sarah ta gaishe da duk manyan wajen, cike kuma da sakin fuska suka amsa mata gaisuwarta sannan suka nemi waje suka zauna, daga nan ƴan aikin gidan wanda a ƙalla sun kai ashirin suka gabatar da abinci, daga kowa yayi serving kansa, tunda aka fara cin abinci babu wanda ya ƙara ko kwakwkwarar motsi har suka kammala sannan ƴan aiki suka ƙara zuwa suka kwashe komai. Nnanne kuwa tun da takai lomar abinci ɗaya baki take kallon Sarah har ta kammala baya yi cokali biyar kwarara ba. Shuru gaba ɗaya ɗakin yayi ana jiran Nnanne ta soma yin magana don hakane zai bawa Kowa damar yin magana, ita kuwa Nnanne taƙi magana sai kallon Sarah da take yi kawai babu kyaftawa, "Yarinya!" Ta faɗi slowly still tana kallon Sarah. A hankali Sarah ta ɗago tana kallon Nnanne, nan take taji wasu irin ruwan hawaye na kwaranyo mata akan fuskanta ganin gaba ɗaya ɗakin nan da take duk yawansu ƴan uwan mahaifinta ne. "Yarinya daga ina, kuma ke wacece?" Nnanne ta kuma jeho mata wata tambayar, Sai da Sarah taja majina kamun tace, "Sunana Sarah, mahaifina kuma sunansa Nuhu kuma a nan gidan aka haifesa." Ta faɗi hakan tana mai nuna Ba Nura (Mai kama da Baba Nuhu) tare da cigaba da faɗin, "Sak haka Babana yake" ta ƙarisa maganar tare da rushewa da kuka tuno halin da Baba yake ciki na mutum-gawa. Wani irin ajiyar zuciya Nnanne tayi tare da soma goge hawayen da yake shirin zubowa, matan ɗakin masu raunin zuciya har sun soma kuka, Nnanne miƙawa Sarah hannu tayi alamar ta taho kusa da ita, da rarrafe Sarah ta ƙarisa tare da rungumeta ta fashe da tsumamman kuka wanda ya taɓa zuciyar mutane da dama dake ɗakin. "Ina ɗana? Ina kika baro min Hussaini na!" Faɗin Nnanne cikin kuka. Ƙara kwakwuneta Sarah tayi tare da faɗin, "Ina can Kaduna, Yana can Nnanne kullum bashi da magana sai taku, duk lokacin da zai bani labarinku, cemin yake yi ba zai iya haɗa idanu daku ba saboda abunda ya aikata maku. Nnanne baba yana can kwance kamar gawa, ba magana babu motsi!" Sarah na kowa nan sai ta kuma fashewa da kuka sosai har tana ƙanƙame jikinta duk kukan gaba ɗaya da biyu take yinsa, tunowa take da halin da Baba yake ciki da kuma halin da take ciki yanzu, sai kukan ya zama biyu. Kuka Nnanne ta fashe dashi wanda ya tada hankalin dattijan dake ɗakin sai duk suka taso suka zagayeta suna bata baki. "Na janye dokar da na saka akan Hussaini, na janye wallahi. Kuje ku taho da ɗan uwanku, kuje Hassan ku taho dashi. Ina son ganinsa kamun na koma ga Allah. Na yafe masa har abada, na yafe maka Nuhuna." Ko wannensu sai da ya share guntun hawaye. Ba Lukman kuwa wani irin farin cikine ya lulluɓesa yana mai jin daɗin saukowar Nnanne, domin ba dadun ita ba, da tuni sun nemi Baba Nuhu a duk inda yake." Hannun Nnanne a kan Sarah tare da faɗin, "Jikanta kuma takwarata, bani labarin ɗana Nuhu!" Gyara zama Sarah tayi tare da faɗin, "Nnanne idan har kina da ƙarfin zuciyar ji, to ki saurareni sai dai labarin Babana ko kuma ince maki dukkanmu, ba labari bane mai daɗin ji!" Gaba ɗaya ɗakin wani irin tsit yayi na wasu daƙiƙu kamun Sarah taja wani numfashi tare da soma faɗin...., "Tun da nake ban taɓa ganin mutum mai haƙuri da sauƙin kai kamar mahaifina ba, mu shidda ya haifa mata sai namiji ɗaya, Na'ima, Nuratu, Hassana, Lukman (Tana faɗin sunan Lukman, Ba Lukman ya ɗago don ya san tabbas shi akai wa takwara) Marfu'a, Ni Saratu da kuma autarmu Aina'u......." Tun daga karayar arzikin baba, taɓarɓarewar tarbiyansu Na'ima da irin karuwancin da suka zuba sanadin huɗubar Lami, lalacewar Lukman, sanadin shiga islamiyarta, aikin da tayi a restaurant wanda shine sanadin haɗuwarta da Khalil, cikin da yayi mata zuwa zubewarsa, gwagwarmayar da aka yi kamun auran da kuma auren, farin cikin da ta samu a gidan zuwa ciwon da tayi
Chapter 95 · 0% Book details