← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 112

Sashe 91

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana kaisu ɗaki tare da rufesu har kai, bata yarda ko gawa ɗaya Lami ta taɓa ba, sai da ta kulle ɗakin sannan ta fito sanye da hijjab tana kuka ta nufi makarantarsu, shugabar makarantar ta sanarwar komai tare da roƙonta akan tazo tayiwa yaran wanka ta shiryasu. Sosai shugaban makarantar mai suna Malama Nusaiba ta tausaya mata tare da lallashinta ta kuma bata baki sannan ta kira su Nuratu don saura mintuna goma a tashi a islamiyar, suma sai da tayi masu nasiha mai ratsa jiki sannan ta shaida masu abunda ke faruwa, kuka suka fashe dashi duka, bata hanasu ba kasancewar ba kururuwa suke yi ba. Tare suka koma gidan har da Malama, kuma kamar yanda Na'ima ta buƙata, malamar ce tayi masu wanka sannan ta suturtasu da kikkafani. Khalil na kwance yayi ruf da ciki akan gado, ya rasa duniya mai ke yi masa daɗi, gaba ɗaya ji yake ya tsani kansa gaba, "Why am I even alive?" Be san sanda ya faɗi hakan ba yana mai kaiwa katifa nausuka kamar zararre! Burum Aina'u ta faɗo ɗakin tare da kama ƙugu tana kallonsa idanu a ƙanƙance, da sauri ya miƙe zaune yana kallonta gabansa na faɗuwa don duk lokacin da ta zuba masa idanu haka, matsanaicin tsoronta yake ji har gabansa na bugawa da sauri-sauri. Nuna kanta tayi tare da faɗin, "Ni! Ni zaka wulaƙanta Khalil saboda kaga matarka da ƴaƴanka? Wato idan mutuwa zanyi sai dai in mutu ko? Ka san cewar ban kawo ba, amma saboda tsabar iskanci da wulaƙanci shine ka sauka ka barni da wahala ko?" Ko mai Khalil bai iya ce mata ba, ji yake ƙirjinsa yayi masa wani irin zafi da ƙunci, hawaye ne yaji suna neman zubowa amma bai basu sararin haka ba, yana jin mugun tsanar Aina'u kamar ya kasheta, amma yana jin sam ko afuska ba zai iya nuna mata hakan ba, duk haushi da tsanar da yake yi mata, idan har suka haɗa idanu sai yaji komai ya washe. "Ina magana ka min shuru! Mahaukaciya ka mayar dani ko kuma me?" Ta faɗi a tsawace. Sam Khalil bai tsorata da tsawarta ba, amma yana ɗagowa suka haɗa idanu da Aina'u be san lokacin da ya furta, "Kiyi haƙuri dan Allah" ba. Harararsa tayi tare da faɗin, "Idan kana so inyi haƙuri in yafe maka, ka tashi yanzu ka sauka ƙasa ka samu ruɓaɓɓiyar matarsa ka koreta ita da ƴaƴanta, idan ba haka ba kuma...." Ta ƙarisa maganar tare da jan ɗan yatsarta akan kuyanta. Ƙura mata idanu Khalil yayi ko kyaftawa bai yi ba, wani uban tsawar ta kuma daka masa tare da faɗin, "Ko baka ji bane?" Da sauri ya miƙe tare da faɗin, "As you wish Ai'n!" Yana gama faɗin haka ya gittata ya fita daga ɗakin. Wani irin tsalle Aina'u ta daka tare da faɗin, "Yyyesss!" Khalil na fita daga ɗakin wasu zafafan hawaye suka shiga zubowa daga idanunsa har zuwa kan ƙirjinsa, kamar kwai ya fashe a cikinsa haka ya riƙa takawa har zuwa ƙofar ɗakin Sarah. Ya jima tsaye kamun ya saka hannu ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga, duƙe take a bakin gado tana sakawa Sam'an wando, da farin ciki gami da ihu yace, "Daddy!" Yana mai nuna shi da hannu. Da sauri Sarah ta waiga tana kallon Khalil ɗin dake bakin ƙofa yana kallon ƙasa hawaye na tsiyayo masa har yana ɗiga a ƙasa. Kallon su Sam'an tayi tare da faɗin, "You two should go and play in the parlour, will meet you there in the next two minutes!" Da sauri Sauban yace, "With daddy?" Ya faɗi hakane yana mai nunasa da hannu. Ɗaga masa kai tayi tare da sauko dashi daga kan gado, dukkansu sai da suka yi shaking hannun daddynsu, har zasu wucesa sai ya dawo dasu baya ya rungume a jikinsa tare da fashewa da kuka yana mai shafa fuskansu. Sarah ce ta ƙariso wajen itama kukan take yi sosai tare da kama hannunsu ta fitar dasu sannan ta jawo ƙofar ta rufe. Kallonsa ta riƙa yi hawaye na zubar mata, shi kuma kansa a ƙasa yana zubda hawaye kuma ya kasa ɗagowa ya kalleta, "Happiness!" Ta kira sunansa a hankali. Da wani irin ƙarfi ya jawota jikinsa ya rungume ƙas tare da sakin kuka kamar yaro, irin ruƙon da yayi mata sai da taji kamar haƙarƙarinta zai ɓaɓɓalle, "Ɗan sassauta kaɗan." Sarah ta faɗi muryanta na rawa don wani irin shauƙi da missing ɗin mijinta ne ya dirar mata, "Saraaah!" Ya kirayi sunanta cikin wani irin raunataccen murya tare da riƙeta gam-gam yana jin wani irin natsuwa na mamayesa, don ba zai iya tuna when last ya riƙeta haka ba. "Sarah meke faruwa damu! Sarah na haukace, ban cikin hayyacina, ban san meke faruwa dani ba, ina jin kamar an ɗauke Khalil ɗin dake cikin jikina, Saratuuuuuu." Ya ƙarasa kiran sunansa tare da fashewa da kuka jikinsa na rawa. Wani irin tausayinsa ne ya mamaye zuciyarta, soyayya da ƙaunarsa na kuma ruruwa a zuciyarta, a lokaci guda kuma tana aikawa Aina'u da kwandon tsinuwa na raba tsakaninsu da tayi. Don Sarah duk wannan abubuwan dake faruwa har ganinsa turmi da taɓaryan da tayi da Aina'u, bai taɓa sakawa taji ta tsaneshi ba, saboda tayi imani duk abunda yake yi ba'a cikin hayyacinsa yake ba, sai dai baƙin ciki da takaici kam ta ɗebe shi iya ɗiba, don ta tabbata da za'a gwada zuciyarta, za'a tabbatar ta samu matsala, Hassan jini kuwa idan yana kaiwa million, to nata sai ya wuce, don babu ranar da bata kwana ta kuma tashi da ciwon kai mai tsanani. "Addu'a itace makamin mumini daddyn twins, ka tashi tsaye ka kai kukanka gaban Ubangiji! Ka rage bacci ka raya darenka wajen roƙon ubangiji, ka yawaita saurarar karatun Alƙur'ani in Sha Allah duk wani abun da yake damunka a zuciyarka zai yaye kuma zaka samu sauƙi. Mun samu jin daɗin duniya, mun bar ubangiji shiyasa Allah ya barmu, amma idan muka miƙa wuya zuwa ga mahalicci, komai zai wuce kamar ba'a yi ba." Ƙara rungumeta yayi tare da faɗin, "Hakane! Hakane!! Maganar ki haka take Mine." Sun kusa mintuna biyar a haka suna jin bugun zuciyar juna kumun zuwa can yayi saurin janyeta a jikinsa ya nufi wardrobe tare da soma zubo da kayan sawanta dana su twins a kan gado kuma a lokaci guda yana kuka. Da sauri ta nufesa tare da kamo hannunsa tana faɗin, "Haolii menene haka? Mai yasa kake fiddo mana da kayan sawarmu?" Fincike hannunsa tayi ba tare da yace mata komai ba ya cigaba da fito da kayan kuma yana hawaye. Ƙara kamo hannun nasa tayi tare da faɗin, "Menene haka Khalil!" Da ƙarfi yace,"Ki sake ni Mine, ki sake ni dan Allah!" Ya faɗi tare da sakin rigar da ya ɗauko ya zauna a bakin gadon tare da riƙe kansa yana kuka. Duƙawa tayi a gabansa itama tana kukan tare da soma faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir!" Tun tana maimaitawa ita kaɗai har shima Khalil ɗin ya ɗauka, duk sai suka cika ɗakin da faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." Aina'u dake ɗaki tana kallon komai a tafin hannunta ta kwaso da uban gudu har tana a dungure a steirs, ko kamun ta ida dungurowa ta saka yatsa ta caki tafin hannunta da ƙarfi, a take Khalil dake zaune ya zabura da ƙarfi tare da ture Sarah ya shiga faɗin, "Tashi! Ki tashi ki kwashi duka kayanki ku bar min gida ke da yaranki sai na neme ki!! Ki tashi nace!!!" A kiɗime Sarah ta tashi don ba ƙaramin ruɗewa tayi ba da jin wawan tsawar da ya buga mata. Ƙaton akwatinta ya jawo tare da soma loda kayanta dana yaran a ciki dai-dai lokacin da Aina'u ta banko ƙofar ɗakin ta shigo tana huci, "Wato kai kake haɗa mata kayan ko? To zo ka fice ta haɗa da hannunta." Idanu jazir Sarah ta kalli Aina'u tare da faɗin, "Aina'u ke ƴar wuta ce babu tantama! Baza ki taɓa gamawa da duniya lafiya. Fir'auna Kina samanki yake Aina'u. Uwa da uba ɗaya suka haife mu, amma wallahi tallahi billahil azeem bazan taɓa yafe maki ba ko da zanga kabarinki naci da wuta! Kin shiga tsakani na da mijina, kin shiga tsakani uwa da ƴaƴanta, Aina'u mutuwarki abun tsoro ce wallahi." Wani irin shu'umin murmushi Aina'u tayi tare da kallon Khalil tace, "Kana jin abunda take faɗi baza ka ɗau mataki ba?" Khalil dai bai ce komai ba, Sarah kuma a zuciye ta ƙarisa wajen Aina'u tare da wanke fuskanta da mari hagu da dama tare da fashewa da kuka tana faɗin, "Allah ya tsine maki Aina'u, Allah ya tsine maki albarka muguwa azzaluma, mara imani! A kafuran ma ke dutse ce, makamashin wutan jahannama! Yanzu baki ji komai ba Aina'u? Ki kwanta da mijina agaba da ƴaƴana Aina'u! Mijin yarki Aina'u!! Anya akwai tsoka a ƙirjinki kuwa? Aina'u ke ƴar wuta ce!" Wani kallo Aina'u tayiwa Khalil tare da faɗin, "Kamar yanda ta ɗaga hannu ta wanke fuskata da mari, haka nake so ka ɗaga naka hannun ka wanke fuskanta da mari, ka nuna mata babu wanda ya isa ya taɓa ni a gabanka ya zauna lafiya ko uban wanene kuwa!" Da sauri Khalil ya ce, "Aina'u......" "Don as I said!" Ta katse shi da ƙarfi. Juyawa yayi ya kalli Sarah tare da nuna mata ƙofa yace, "Get out of this house right now, and don't forget to go with your kids!" Hawaye kawai Sarah keyi tana kallonsa, irin kallon kar kayi min haka. Juya baya yayi yana hawaye gabansa na wani irin faɗuwa. Sarah kuwa wani irin kuka ne ya kufce mata, da sauri ta ƙarisa kusa dashi ta ɗuka tare da riƙe ƙafafunsa ta shiga faɗin, "Happiness, Kar Kayi min haka, ka manta alƙawarin da kayi min? Ka manta kace min zamu kasance tare, for better for worse, ka mance kace baza ka taɓa bari nayi hawayen baƙin ciki ba, ka manta kace an halicceni ne domin ka, kai ma Kuma an halicce ka ne domin ni? Ka dubi girman Allah ko don Sam'an da Sauban ka barni a ɗakin mijina." Da ƙarfi Aina'u tace, "Capital NO! You're more welcome. Park your things and get lost!" "Da mijina nake magana ba dake ba
Chapter 91 · 0% Book details