← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 112

Sashe 33

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 2 min read

da komai. D'akin ba k'aramin kyau yayi ba. Gadon kalar b'aki da purple. Wardrobe d'in kuma irin mai cin bangon nan ne mai k'ofa shidda. Hatta labule sabo suka saka mata sannan suka mak'ala mata TVplasma sannan suka fita suka koma d'akin Baba. Shima haka suka jera masa nasa kayan irin na Lami sak sai dai akwai bambamcin launi. Shi nayi farare ne k'al. Kuma kamun su saka sai da suka shimfid'a masa lallausar carpet da ya mamaye d'akin mai tsada kalar blue-black. Sannan suka saka masa TVplasma irin flatscreen d'in nan wanda kud'insa zai kai 250k zuwa 300k, dama kuwa akwai masu had'a dish a waje kuma har sun kammala, sai kawai suka shigo suka yi settings kasancewar ko wani d'aki yana da decoder d'insa. D'akin Baba har da tvstand mai kyau. D'akin su Sarah suma ab had'a masu nasu furniture d'in wanda ga kasance white and baby pink. Kuma gadonsu six by seven ne yayin da su d'akin Baba ya kasance six by six. Gaba d'aya gidan sai ya koma kamar gidan amare. Komai sabo. Don har da dank'areran deepfreeze da kuma fridge _Khalil_ ya siya masu. Wajejen k'arfe biyu suka kammala komai suka wuce. Lami kuwa sai uban gud'a take yi. Lokacin da ta shiga d'akin Baba domin taga irin nasa gyaran, sai bak'in ciki ga rufe ta ta shiga surfa bala'i mai yasa ita ma ba'a saka mata Tvstand stand ba. Baba kasancewar baya son tashin hankali yace ta d'auka ta kai d'akinta. Babu kunya kuwa ta kama ita da Nuratu suka mayar d'akin nata. Aina'u kuwa ba ita ta dawo gidan ba, sai bayan magriba. Tana sauka daga napep ta taras da zambad'ed'iyar motar _Khalil_. Wani mugun tsaki ta saki tare da isa k'ofar gidan ta tura ta shiga kuma a dai-dai lokacin ta hangi bayan _Khalil_ d'in zai shiga d'akin Baba. Tsayawa tayi tana k'arewa d'akunan kallo ganin ko Wanne da sabbin labulaye. Dai-dai nan Sarah ta fito daga bayi hannunta rik'e da buta, tazo dai-dai inda Aina'u take, sai ta saka mata k'afa tayi wani irin mugun fad'uwa, ji kake tim. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Sarah ta fad'i da k'arfi tana mai kai hannu k'asan mararta. Aina'u kuwa sai tayi saurin sunkuyawa tana fad'in, "Sannu Sarah, garin yaya kika fad'i haka." Gaba d'aya gidan suka fito, _Khalil_ ya riga kowa fitowa da gudu jin muryan Sarah tana salati. Ita kuwa Sarah sai cewa take "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, cikina, wayyo Allah cikina." Rintse idanu _Khalil_ yayi da k'arfi ganin zini na gangarowa daga k'afafunta...............
Chapter 33 · 0% Book details