Sashe 87
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba ɗaya Khalil ya rasa control ɗinsa, Aina'u ta juye masa kamar Sarah, yunƙurawa yayi tare da juyata ya koma kanta tare da birkice mata, sai sararaba sai da ya samu natsuwa sannan ya koma gefe, Aina'u kuwa cikin zuciyarta cewa tayi, "Na rantse da Yesu Almasihu babu uban da ya isa ya rabamu tunda na ɗanɗani zumanka, shegiya ƴar iska ashe ta san daɗin da take kwasa shiyasa kullum tana naniƙe da kai babu dare babu rana." Da sauri ta tashi zaune tana kallon Khalil da yaja zanin gado ya rufe jikinsa yana shashshekar kuka kamar wani ƙaramin yaro, "Heart, mai ya faru kake kuka?" Ta faɗi tana mai kai hannu jikinsa, wani irin tureta yayi da hannunsa ba tare da ya juyo ba yana mai jin baƙin ciki da dana sani har da na haihuwarsa da Hajiya tayi kasancewar ya kusanci Ƙanwar Matarsa wanda har ga Allah shi bai san yanda aka yi hakan ta faru ba, don gaba ɗaya Aina'u koma masa Sarah tayi, sai tunaninsa gaba ɗaya ya gushe, kuma bai dawo cikin hayyacinsa ba har sai da ya biya buƙatarsa da ita. Wani irin durowa Aina'u tayi tare da duƙawa ƙarƙashin gadon da suke kai, sai taga still tukunyar tsafinta nasan kuma bai canza kala ba, ɗagowa tayi ta kalli Khalil ɗin da har wannan lokacin shashshekar kukan yake yi yayi ruf da ciki, a hankali ta kuma duƙawa ta tura hannunta cikin tukunyar har sa da tsintsiyar hannunta ya shige sannan ta ɗago tare da hawa gadon, tun daga kan ƙeyarsa take shafa masa hannunta har zuwa kan ƙirjinsa, nan take ya mirgino tare da zuba mata idanu, still sai ta kuma rikiɗemasa zuwa Sarah, "Ina matuƙar ƙaunarki, sosai fa!" Ya faɗi yana mai kai hannu ya shafo fuskanta, caraf ta riƙe hannun tana mai jin wani irin sanyi a cikin zuciyarta don da tayi tunanin tsafin da tayi masa ya lalatace, ɗaura kansa tayi a ƙirjinsa tana yi masa tafiyar tsutsa a cikin kunne zuwa bayan kunnansa har bacci ya ɗaukesa, tana ganin haka ta ajiye kansa a kan pillow a hankali tare da sauka daga kan gadon ta kunna hasken ɗakin sannan ta jawo wannan tukunyar dake ƙarƙashin gado ta fito dashi tare da tsoma hannu ta ɗauko wannan mutum-mutumin itacen nan ta hau kan gadon tare da kaisa saitin ƙirjin Khalil, wannan baƙin ruwan ya riƙa ɗiga akai, sai da ruwan ya mamaye ƙirjin sannan Aina'u ta zaro wani abu mai kama da mashi ta ɗaga tare da cakawa da ƙarfi a ƙirjin wannan mutum-mutumin sai da Khalil dake bacci yayi wani irin zabura tare da dafe ƙirji, amma yana arba da fuskan Aina'u sai ya sakar mata murmushin tare da miƙa mata hannu alamar tazo garesa duk da yana kallon abinda ke hannunta amma bai iya ko ƙare masa kallo ba balle ya tanka. Sauka tayi ba tare da ta isa wajensa ba ta mayar da komai cikin ƙarƙashin gadon sannan ta kashe wutan ɗakin ta hau kan gadon ta shige jikinsa, a cikin daren nan sai da ta ƙara naiman Khalil sau uku sannan tayi bacci. Ɓangaren Sarah kuwa, raya darenta tayi da kuka, don yanda taga rana haka taga dare, idanunta yayi luhu-luhu, ji tayi sam baza ta iya jure rashin Khalil a kusa da ita ba, ta riga ta gama yanke shawarar zata cewa Khalil ko ita ko Aina'u, kuma ta san a irin ƙaunar da yake yi mata, itan zai zaɓa. A kunnanta akai kiran sallah, saukowa tayi daga kan gadon ta nufi bayi ta ɗauro alwala tare da tada sallah, bayan ta idar da sallar, sai ta miƙe ta hau gado saboda wani irin bacci dake fuzgar kasancewar bata samu bacci ba. Tana kwanciya baccin yayi gaba da ita. Can cikin baccinta taji ihun kukan Sam'an, da sauri ta tashi zaune tare da jawosa jikinta ta hau shayar dashi, shima Sauban kamar an tsikaresa sai ya tashi. Ko data gama shayar dasu, wayarta ta jawo ta kunna, da sauri ta diro daga kan gadon ganin bakwai da mintuna arba'in tare da faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Breakfast ɗin Happiness." Tana gama faɗin haka ta fice ko sauraran su twins dake kuka saboda ta fita bata yi ba, jawo ƙofar tayi tare da soma saukowa daga steirs ɗin da sauri, saura steps huɗu ta sauko gaba ɗaya ta tsaya turus tana kallon ikon Allah, zaune Khalil yake a kan dinning, Aina'u kuma cikin wani irin shigar ɗaukar hankali tsaye a bayansa ta turo hannayenta ta saman kafaɗansa tana saka masa Irish a plate, daga nesa ma zaka ɗauka rungumesa tayi. Sarah har wani jiri taji yana neman yar da ita tayi saurin riƙe ƙarfen dake gefenta tana maimaita, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Cikin zuciyarta. "Ka cinye tass, ban so ka fita da yunwa." Faɗin Aina'u cikin kunnen Khalil ɗin har da ɗan cizon fatar saman kunnensa, shi kuma Khalil wani irin yaji yaja tare da cafko hannun Aina'un ya zagayo da ita tare da jan kujeran baya ya ɗaurata a kan cinyarsa sannan ya zagayo hannunsa ya rungumeta tare da faɗin, "Abincin kike so inci kuwa? Bari dai in baki tukwuicin daɗin da kika bani jiya!" A firgice suka juya gaba ɗaya suna kallon Sarah data kwatsatsa wani irin ihuuu tare da gungurowa saboda ƙafarta da ya kasa riƙeta sakamakon abunda taji ta kuma gani. Da sauri Khalil ya ture Aina'u dake jikinsa tare da ƙarisawa wajen Sarah har da haɗawa da gudu, jijjigata ya soma yi yana kiran sunanta da ƙarfi, Aina'u kuwa folding hannunta tayi tana kallonsu takaicin na neman kasheta, "Wato kai kana da taurin kai ko? Har yanzu tana maƙale a zuciyarka kenan! To zanyi maganin ka tabbas." Faɗin Aina'u cikin zuciya. Sarah kuwa tunda ta faɗo ƙasa ta fita daga hayyacinta, taimakon gaggawa Khalil ya soma bata ta hanyar bata numfashin bakinsa bayan ya toshe hancinta, wani irin numfashi taja tare da wawware idanunta, sai da ta kwashi second ashirin kamun ta saki wani ajiyar zuciya ta kuma zubawa Khalil idanu ko kyaftawa bata yi, "Mine!" Ya kirayi sunanta a hankali, caraf ta riƙe hannunsa tare da ƙanƙamesa ta shiga faɗin, "Mafarki Happiness! Mafarki nayi wai Aina'u tazo gidan nan tana neman shiga tsakaninmu. Ba gaskiya bane ko Happy?" Sarah ta faɗi tana fatan Allah yasa abunda taji ta kuma gani duk a mafarki ne. Aina'u najin haka ta ƙariso wajen tare da faɗin, "Na'am, mai kike cewa Aunty Sarah! Naji kamar kina kiran sunana." A firgice Sarah ta ɗago daga kan ƙirjin Khalil tana kallon Aina'un, can kuma ta miƙe da sauri tana kallon Khalil ɗin dake ɗuke ya kasa ko ɗago idanu balle ya kalleta saboda wani irin kunyanta da yake ji. Wasu irin ruwan hawaye Sarah ta shiga zubarwa tare da duƙawa akan guiwowinta ta shiga faɗin, "Happy, mai na rageka dashi a cikin gidan nan? Ta ina na gaza? Shin ka taɓa nemana a shimfiɗa na ƙaurace maka? Ƙanwata Khalil! Ƙanwata uwa ɗaya uba ɗaya kake nema Khalil!! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!!! Ka cuce ni ka cuci rayuwarka, da iliminka, da matarka da ƴaƴanka da komai kake aikata zina! Wallahi tallahi baka yi min adalci ba." Ta ƙarisa maganar tana mai rushewa da kukan baƙin ciki, can kuma ta ɗago ta kalli Aina'u tare da faɗin, "Ke kuma asararriya wulaƙantacciya, watsatstsiya azzaluma muguwa mai shiga tsakanin mata da miji, anya kuwa ke jini nace Aina'u? Anya kuwa ba canje akai wa Lami a asibiti ba? Zo ki fice ki bar gidan nan ko wallahi inyi ajalinki, bazan taɓa bari kici galaba akan mijina ba!" Sarah na gama faɗin haka ta kwasa da gudu ta nufi kitchen tare da ɗauko wuƙa ta fito da gudu tayo kan Aina'u tana faɗin, "Fita ko in kashe ki sai dai nima a kashe ni!" Da sauri Khalil ya shiga tsakani tare da kwace wuƙar a hannun Sarah yana faɗin, "Baki da hankali ne Mine?" A zafafe tace, "Eh bani da shi! Tun ranar da ka fara naniƙewa Aina'u na rasa hankalina, kuma bazan taɓa dawowa cikin hankalina ba sai ranar da ka rabu da ita." Hannu biyu yasa ya riƙo damatsanta tare da faɗin, "Ki dawo cikin tunaninki Sarah, ni da Aina'u babu abunda ke tsakanin mu sai wa da ƙanwa, ita ɗin fa ƙanwarki ce, Aina'u Ƙanwar matata ce kawai." "Ƙarya ne, ni ba ƙanwar matarka bace kawai, ka faɗa mata gaskiya kawai tunda yanzu ta san komai, idan zata iya haƙuri, to! Idan kuma baza ta iya ba, hanya a buɗe take, amma maganar ni ƙanwar matarka ce kawai wannan ba haka yake ba, ka gama kwanciya dani a ɗaki jiya kana min ihun daɗi da sambatu, har kana faɗin baka taɓa samun natsuwa a jikin Maman twins ba kamar yanda jiyan ka samu a jikina, ohh duk ka manta da wannan kenan?" Zaro idanu Khalil yayi don ya san wallahi shi bai ce haka ba. Itama Aina'un zaro masa idanun tayi tare da faɗin, "Ko ba haka bane!" "Ya ke Kuma anan son kashe wuta kina ƙara rurawa!" Ko kamun su ankara Sarah tayi kukan kura ta wanke fuskan Aina'u da maruka hagu da dama tare da shaƙar mata wuya tana faɗin, "Sai na kashe ki yau a cikin gidan nan!" Da kyar Khalil ya janye Sarah a jikin Aina'u sai aika mata da maruka da naushi take yi, Aina'u kuwa wani irin zuciya ne ya yunƙurota, take ta danna yatsarta tsakiyar tafin hannunta sannan ta murza da ƙarfi. Nan take wani zuciya ya yunƙurowa Khalil ya ɗaga hannu tare da wanke fuskan Sarah hagu da dama sai da tayi taga-taga zata faɗi, da mugun mamaki take kallonsa hannunta dafe da kunci hawaye na tsiyaya. Khalil kuwa jawo Aina'u yayi ya rungume har da jijjigata kamar baby yana faɗin, "Akwai inda ke yi maki ciwo muje asibiti?" Girgiza kai Aina'u tayi tana wani narkewa tare da faɗin, "Ka ɗaukeni muje ɗakinka, tsoro nake ji kar ka fita ta nemi kashe ni, muje ɗaki kar ka fita ko ƙofa yau!" Cak ya ɗauketa tare da saɓata a kafaɗa ya gitta Sarah da tayi mutuwar tsaye. Aina'u kuwa wani irin gwalo rayiwa Sarah mai tsayawa a zuciya sannan taja hannunta wajen wuyanta alamar zan kashe ki sannan