← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 112

Sashe 21

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai kuma Munafuki! Ya muka yi da kai d'azu?" _Khalil_ ko d'agowa bai yi ba, balle ya kalleta har ya amsa maganar ta. "Lami wannan wani irin rashin hankaline haka? Yaya zaki shigo min d'aki babu sallama kuma kin san ina da bak'o! Wannan ai rashin hankaline. Malama fitar min daga d'aki." Harara ta makawa Baba tare da fad'in, "Ba zan fita ba wallahi. Sai anyi komai a idanuna. Wato daga kai sai y'arka ne zaku rik'a cin kud'in ko? To wallahi baza ta sab'u ba bindiga a ruwa!" Karkacewa _Khalil_ yayi ya fiddo da rafar kud'i y'an dubu-dubu ya mik'a mata tare da fad'in, "Gashi. Ni magana nazo muyi da Baba ba wani abu ba." Fizge kud'in Lami tayi da sauri don a zatonta Baba zai kawo hannu ya warci kud'in tana mai sakin murmushin ganin tashin farko an bata dubu d'ari. "Yauwa to ko kaifa. Ai wallahi da baka ban kud'in nan ba, Sarah baza ta k'ara cin ko loma d'aya a cikin gidan nan ba. Kuma duk aikin wahalar gidan nan ita zata rik'a yinsa. Babu ruwana da tana d'auke da k'aramin ciki." Taga gama fad'in haka ta harari Baba tare da ficewa daga d'akin. Da idanu _Khalil_ yabi Lami yana mai tabbatar wa kansa ba ita bace mahaifiyarsu Sarah. Baba kuwa kunya ce ta kama shi kamar k'asa ta tsage ya shige ciki. Da kyar ya iya bud'e baki tare da fad'in, "Dan Allah kayi hak'uri. Haka halin Lami yake. Sam bata da girma sai na jikinta." Kallon Baba _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Baba wacece ita?" Sai da Baba ya sunkuyar da kai don kunya yake ji ainun ya nuna Lami matsayin matarsa uwar Y'ay'ansa. A hankali cike da rauni Baba yace, "Matata ce. Uwar y'ay'ana!" Fad'in Baba hawaye na wanke fuskansa kasancewar mai sauri kuka. "Amma Baba ba ita bace mahaifiyarsu Sarah ko?" Hannu Baba ya kai ya sharce hawayen idanunsa tare da fad'in, "Ita ce. Wallahi samari ita ce ta haifi duk Y'ay'an dake cikin gidan nan." Wani irin ajiyar zuciya mai k'arfi _Khalil_ ya saki yana mai jin matsanaicin mamaki. "Kana mamaki ko? Na san za kayi mamaki Samari. Ba kai kad'ai ba, da yawan mutane basu yarda Lami itace ta haifi su Sarah sabida irin tarbiyan da tayi masu sakamakon son abun duniya. Ita gaba d'aya kallon wad'annan yaran take yi matsayin babban jarinta. Sam ta mance su d'in amane Allah ya bata. Na'ima ita ce y'arta ta fari, sai Nuratu, Lukman, Hassana, Marfu'a, sai auta Aina'u. Duk Y'ay'an Lami ne. Ita ta haife su da cikinta." Hassana ma y'an biyu ne, d'ayan tun a ciki ya mutu. Da yanzu su takwas ne, shidda mata maza biyu." Da tausayi _Khalil_ ke kallon Baba tare da fad'in, "To Baba ya aka yi irin haka yake faruwa a cikin gidanka, amma baka da ta cewa?" Sunkuyar da kai Baba yayi yana mai jin d'aci da k'una sosai cikin zuciyarsa tare da fad'in, "Lami tafi k'arfi ba Samari! Duk yanda zanyi maka bayani, baza ka gane ba. Amma Lami ta raina ni, bata ganin mutunci da darajana tun da na samu karayar arziki. Shiyasa y'ay'ana suma suka taso da d'abi'un da suka ga tana yi min. Guda d'aya ce ta fita zakka. Saratu na tausayina sosai, tana bani girma, tana kula dani kuma tana gudun b'acin raina. Tana sona sosai kuma duk abunda nace tayi, shi take yi, idan na hane ta kuma har abada ta bar abun nan kuma baza ta kusance shi ba." Gyara zama _Khalil_ yayi tare da soma fad'in, "Baba da farko dai hak'uri zan soma baka, dan Allah ka yafe min domin na cutar da kai. Tabbas 'yarka Sarah mutuniyar kirki ce. Kuma duk wani abu da ya faru tsakani da ita, wallahi ba da son ranta bane. Ban san ta yanda zanyi maka bayani ba Baba. Amma wallahi nima ba mazinaci bane. Tsautsayine ya afka mana daga ni har ita Saratun. Kuma wallahi ban d'auka sanadiyar abunda ya faru tsakani da ita ta samu ciki ba. Na jima ina naiman ta, amma ban ganta ba sai yau da Allah ya kawo ta asibitina. Baba dama ni ina son Sarah, kayi hak'uri ya yafe min kar kace zaka hanani ita saboda wannan abu da ya faru, ni nayi alk'awarin Sarah na haihuwa sati baza ta zagayo ba sai da aure na a kanta. Tun daga yau da na san Sarah na d'auke da cikina, d'awainiyarta gaba d'aya ya dawo kai, cinta, shanta da komai nata. Dan Allah Baba kar ka hana ni Saratu." Shuru Baba yayi yana wani tunani a cikin zuciyarsa. Ya jima bai yi magana ba, kuma bai d'ago ba. _Khalil_ kuma addu'a kawai yake yi Allah yasa Baba ya amince. Ajiyar zuciya Baba ya sauke tare da fad'in, "To! Ni bazan ce ban amince ba, matsalar guda d'aya ce. Shin idan kai ka amince zaka auri Saratu, iyayenka fa? Kai da kanka kaga irin gidan da kake neman aure. Kasan su wanene y'an uwan Sarah da kuma mahaifiyarsu. Gaba d'aya unguwarnan anyi masu tambari. Karo na biyar kenan ana fasa auren Saratu saboda bak'in fentin da y'an uwanta suka goga mata. Kud'in goro ake yi masu. Gani ake yi ita ma Saratun yawon banza take yi. Idan kai ka amince, iyayenka zasu amince ka auri Saratu ne?" Sai da _Khalil_ ya d'ago suka had'a idanu da Baba sannan ya sunkuyar da kai yace, "Baba mahaifiyata sam bata da matsala. Mace ce mai fahimta sosai. In Sha Allah baza'a samu matsala da family na ba. Amincewar ka shine kawai nake buk'ata Baba." Fad'in _Khalil_ amma deep down ga san k'arya yake yi, ya san tabbas za'a sha daga da Hajiya, duk da yana da yak'inin zata amince musamman idan ta samu labarin yayiwa Sarah ciki, amma y'an uwan mahaifinsa ne yasan za'a mugu-mugun kai ruwa rana dasu. "To shikenan, Ubangiji Allah ya shige mana gaba yasa muna da tsawancin kwana." Da "Ameen" _Khalil_ ya amsa yana mai jin farin ciki a zuciyarsa. "Baka shaida min sunanka ba." Fad'in Baba. "Sunana Ibrahim Baba." Jinjina kai Baba yayi tare da fad'in, "Ma sha Allah!" _Khalil_ kallon k'afar Baba yayi tare da fad'in, "Baba ka dad'e kana ciwon k'afar nan ne?" Kallon k'afar Baba yayi tare da fad'in, "Shekaru talatin da biyu kenan ina fama da ciwon nan, tun Na'ima na da shakara d'aya a duniya" da mamaki _Khalil_ ya kalli Baba tare da fad'in, "Kuma baka je asibiti ba?" Murmushin Baba yayi tare da fad'in, "A kan ciwon k'afar nan sai da na rasa komai nawa. Da wannan gidan kawai na tsira. Ai da abun yafi muni ma. A hankali Allah ke ta kawo sauk'in." K'urawa k'afar idanu yayi kamun yace, "Allah ya baka lafiya Baba. Zan rik'a zuwa lokacin bayan lokacin. Sannan in Sha Allah zan zo na d'auke zuwa asibitina a duba k'afar sosai." Ya fad'i hakane tare da saka hannu a aljihu ya fiddo rafar kud'i y'an dubu-dubu guda biyu ya ajiye a kan yaloluwar katifar Baba. "Zo-zo-zo, d'auke kud'inka dan girman Allah. Wanda ka bawa Lami ma ya isa haka." D'ukawa _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Baba dan girman ubangijin kada ka k'i karb'an kud'in nan. Ka d'auke ni matsayin dank'a na cikinka. Nasan baza ka k'i karb'an kud'in hannun dank'a ba. Kayi min wannan alfarmar Baba." Ajiyar zuciya Baba yayi tare da fad'in, "To d'auke daya ka bar d'aya dan Allah Ibrahim." Hannu _Khalil_ ya kai ya d'auka tare da fad'in, "Nagode da karamcin ka Baba. Allah ya saka da alkhairi. Sai na sake zuwa." D'aga masa hannu Baba yayi tare da fad'in, "To d'ana nagode nima. Allah yayi albarka." Da ameen ya amsa tare da fitowa daga d'akin. Gaba d'ayansu suna tsatstsaye a tsakar gidan suna kallon k'ofar d'akin Baban, sun k'osa ya fito ya basu nasu rabon don Lami tace kwandala baza ta basu ba. Yana fitowa suka saki murmushi tare da fad'in, "K'aninmu har an fito." Babu yabo babu fallasa yace "Eh" tare da mik'a masu kud'i da Baba ya sashi ya d'auki d'aya tare da fad'in, "Ku raba!" Yana fad'in haka ya fita. Da sauri Lami ta bishi a baya, sai da ya kai k'ofa sannan ya tsaya tare da juyowa, sam baya ganin girmanta matsayinta na surukarsa. Fuska ya tsuke sosai tare da fad'in, "Lafiya?" Murmushin tayi tare da kwance zanintata sake d'aurawa sannan tace, "Dama maganar abincin Sarah ne. Dama na fad'a maka tun farko, ni ban ciyar da y'ay'ana kuma in ciyar da nasu Y'ay'an. Kaga ai yanzu Saratu tana d'auke ne da cikinka, dole ne duk wani abincin da zata ci da duk wani abu da zata nema kai zaka kawo kud'i a sayo. Ko baka duba list d'in da na baka bane?" Fuskan nan a tsuke _Khalil_ yace, "Ban duba ba, amma zuwa anjima za'a kawo komai. Sannan a kula da ita sosai. Duk abunda take buk'ata a kira ni a waya a sanar min. Kar a bari ta sha wani magani idan ba wanda na kawo ba. Idan wani waje nayi mata ciwo, immediately a kira ni a sanar min. Sannan abu na gaba, idan wani abu ya samu ciki na, ba zan kyale kowa ba. Ki turo min ita idan kin koma." Fad'in _Khalil_ tare da bud'e gidan ya fita. Don wani irin haushi da tsanar Lamin yake ji. Sam bata cancanci zama surukarsa ba. Lami kuwa tab'e baki tayi tare bud'e gidan ta kallesa tsaye jikin k'arfen gidan mak'otansu, mik'a masa wayarta tayi kirar Itel tace, "Saka min number d'inka don ban da shi." Karb'an wayar yayi tare da danna digits d'insa ya mik'a mata. Ita kuma ta amsa tare da juyawa ta koma cikin gidan. D'akin su Sarah ta shiga, zaune ta same ta a k'asa hannunta rik'e da kwalbar fantan da Aina'u ta sayo mata d'azu kamun su tafi asibiti. Da fantan ta iya shan maganin da _Khalil_ d'in ya bata. Don ruwa bai wuce mak'ogoronta. "Sai ki tashi ki fita yana jiranki a waje." Fad'in Lami tana kallon Sarah dake maida numfashi. "Waye?" Fad'in Sarah tana kallon Lami. "Ubanki ne. Idan kin fita zaki gansa." Lami ta fad'i tare da juyawa ta bar d'akin. Sarah kuwa turo baki tayi tare da mik'ewa ta saka hijab d'inta da ta cire
Chapter 21 · 0% Book details