← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 112

Sashe 58

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ya manta da ita a cikin gidan. "Ashe kina nan" shine abunda ya faɗi kawai tare da fita daga parlour. Wani irin kukan baƙin ciki Aina'u ta saki tare da miƙewa a zuciye tayi sama, kamun ta tura ƙofar ɗakin sai da ta tsaya ta goge hawayenta tukun sannan ta tura ƙofar. Juyowa Sarah dake gaban mirror tayi, sai da gabanta ya faɗi ganin Aina'u. "Sarah don nazo gidanki shine zaki min wulaƙanci ke da mijinki? Nagode kuma da izinin Allah ba zan sake zuwa gidanki ba." Tana gama faɗin haka ta juya zata fita. Da sauri Sarah ta miƙe tare da kamo hannunta tace, "Dan girman Allah ƙanwata kiyi haƙuri, wallahi ba wulaƙanci nayi maki ba. Kiyi haƙuri ki yafe min na san ban kyauta miki ba. Dan Allah Aina'u" ta faɗi tana mai haɗe hannunta biyu. "Amma Sarah....." Sarah tayi saurin cewa, "Dan Allah kiyi haƙuri ki bar maimaita magana. Zo ki zauna ina zuwa." Ta riƙo hannunta tare da zaunar da ita a kan gado ita kuma ta isa gaban mirror ta busar da gashin kanta sharp-sharp sannan ta saka riga da skirt English wear sannan ta saka dogon hijjab ta tada sallah. Bayan ta idar da sallar ta cire hijjab tare da nannaɗe dardumar ta ajiye sannan ta zauna kusa da Aina'u tare da faɗin, "Kiyi haƙuri Aina'u, tashi mu sauka ƙasa musha hira." Ta faɗi hakan tare da kama hannun Aina'u wacce ta gama ƙarewa gadon kallo ganinsa a hargitse kuma dama sai ƙarewa gashin Sarah kallo take yi ganinsa jiƙe kamun ta soma busar da kanta. Suna isowa parlour Khalil na shigowa. A gaban Aina'u ya kama kan Sarah tare da sakar mata kiss a goshi tare da faɗin, "Allah ya yi maki albarka!" Sannan ya nufi sama. Baki sake Aina'u ta bishi da kallo har ya ƙule kamun ta zauna tana sakin ajiyar zuciya. Aina'u ba ita ta bar gidan nan ba sai bayan magrib. Washa gari ma ta kuma dawowa, Khalil kamar ya fasa ihu don itace ta soma danna doorbell ko taran safiya bata yi ba kuma sai bayan magrib ta wuce duk ta hana su sakewa. A rana ta uku ce Khalil ya kai bango, don yana buɗe ƙofa yaga ita ce ko amsa gaisuwarta bai yi ba ya juya ya koma sama kuma yaƙi faɗawa Sarah tazo, kuma be bar Sarah ta fito daga bedroom ba ma balle ta sauko parlour taga Aina'un. Ranar har lokacin tafiyarta yayi bata ga ko ƙeyar Sarah ba, shima Khalil ɗin sau biyu ta gansa, lokacin da ya buɗe mata ƙofa da kuma lokacin da ya sauko zuwa kitchen ya dafa indomie da kwai ya koma saman, kuma ko kallon inda take bai yi ba. Sallah ma azahar da la'asar a ɗaki suka yi tare. Tsabar haushin da Aina'u taji, bata san lokacin da tayi wani irin kwallo da magen Khalil ba sai da ta karye a ƙafa sannan ta fizgi jakarta ta fita daga gidan. Tun daga ranar bata kuma dawowa gidan ba. Khalil kuwa kamar zuciyarsa za tayi bindiga ganin Madhu ɗinsa a karye sai kuka take yi. Haka ya kwashe ta zuwa asibitin dabbobi aka gyara mata ƙafar. Satin Sarah biyu a gidan Khalilullah, sun yi sabo da ƴan gidan sosai, kuma kullum da rana idan Khalil ya tafi sallar azahar a side ɗin hajiya take zama ita da Aunty Maryam har lokacin la'asar sannan kowacce ke komawa nata ɓangaren domin ɗaura girki. Sarah ta saba da nacin Khalil yanzu, kullum suna manne da juna babu daren banza. Ba ƙaramin soyayya suke zubawa ba a gidan. Ɓangaren kuwa, ranar da ta bar gidan Sarah keke napep ɗinsu yayi hatsari ta samu gocewar ƙashi a cinya, kuma babu wanda ya sanar da Saran. Wata ɗaya yazo ya wuce, biyu, har uku, Sarah tayi wani irin kyau da ƙiba da haske. Duk wanda ya ganta ya san tana cikin kwanciyar hankali. Yau da take cikin wata uku da kwana goma a gidan miji, Khalil yayi surprising ɗinta bayan gama nacinta akan tana son zuwa gida taga baba dasu Lami. Kamar an sakata a aljanna saboda farin cikin Khalil yace ta shirya zasu je gaida su baba. Wata lafiyayyiyar shadda ta saka kalar ruwan toka wanda yaji stone work iri ɗaya da na jikin Khalil. Sai da ɗauko farin gyale da farin takalmin vinci ta saka. Kaɗan ta fesa turare saboda Khalil bai so idan zasu fita ta riƙa fesa turare sosai. "Wow! Wife kin ganki kuwa?" Hularsa ƙube wanda Hajiya ta ɗinka masa da kanta ta saka masa tare da jawosa ta koma ta gabansa ta kwanto a jikinsa shi kuma ya ɗaura kansa a kan wuyanta, ita kuma tayi masu hoto. Ba ƙaramin kyau hoton yayi ba. "Wai nace ba, wani yare ne ku? Don nasan ku dai ba Hausawa bane." Yan maganar ne a cikin kunnanta. Sai da ta lumshe idanu sannan tace, "Na faɗa maka mu ƴan Nasarawa ne can _Wamba_. Baba yace sunan unguwarmu layin abakwa. Duk cikin mu babu wanda ya taɓa zuwa. Sunan yaren baba _Nindire_. Kuma yana ji sosai. Don akwai abokansa ƴan can, muna ji suna yi idan sun haɗu." "To ke kina ji?" Girgiza kai tayi tare da faɗin, "Ko zo in kashe ka." Dariya yayi shafa cikinta tare da faɗin, "Ɗana dake nan ko ƴata, za suji Kanuri in Sha Allah, zan riƙa yi musu, kuma Hajiya ma nasan za tayi masu." Kallon cikinta tayi sannan ta kallesa tare da faɗin, "To ai ni bani da ciki." "Ni da nayi cikin ai na sani." Ya bata amsa yana dariya. Kallon cikinta dake a shafe tayi, bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba tana fatan Allah ya amshi bakinsa. "Muje ko Queen" ya faɗi yana mai nuna mata hanya. Fita tayi ya biyota a baya, ji kawai tayi an ɗauke ta cak, bai sauketa ba sai da ya kawota har ƙofar ɗaki. Ɗakin Hajiya taje domin shaida mata zata gida, ba ƙaramin sha tara na arziki ta haɗa mata ba danginsu sabulai, turaruka, shadda da atamfofi har da manya-manyan zannuwar gado guda biyu. Khalil ta parking ta fito da gudu tayi cikin gida, babu kowa a gidan daga Lami sai Aina'u da ƴaƴansu Na'ima. Rungume Lami tayi tana mai farin cikin ganinta, da idanu tabi Sarah dashi, can kuma ta murza idanunta tare da faɗin, "Sarah! Kece haka?" Ta faɗi hakane tare da kaiwa ƙasa ta shiga faɗin, "Yesu Nagode, Nagode Yesu da kaba yarinyana kwanciyar hankali. Almasihu na koma gareka, ka saka albarka a rayuwar ƴata. In to my heart, in to my heart, come into my heart, Lord Jesus, come in to stay, come into my heart Lord Jesus, ameen!" Ta ƙarisa addu'ar tare da rungume Saran. Baba Nuhu kasa haƙuri yayi Sarah ta shigo, sai gashi ya fito yana farin, da gudu ta ƙarisa tare da faɗin, "Babaaa! Kai ne haka? Kaga yanda ka ƙara lafiya da kyau." Dariya baba yayi tare da faɗin, "Albarkacin haihuwarki ne Sarah, ban san mi zan cewa mijinki ba sai dai kawai ince Allah ya bashi Aljanna. Kullum cikin hidima yake mana. Ba'a haɗa cikakken sati bai zo gidannan gaishe ni ba." Zaro idanu Sarah tayi tare da kwaɓe fuska tace, "Amma shine bai taɓa zuwa dani ba sai yau, kuma baya faɗa min yazo." Murmushi baba yayi tare da faɗin, "Nine nan nace masa kar ya yarda ki soma fita sai kinyi wata uku da aure, shiyasa ko kwanciyar Aina'u a asibiti nace kar a faɗa maki." Zaro idanu Sarah tayi tare da faɗin, "Yanzu Aina'u ta kwanta asibiti baba shine ba'a faɗa min ba? Ni wallahi ba'a kyauta min ba." Dai-dai nan Khalil ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Bayan baba ya amsa yace, "Ke dama tare kuke da Ibrahim ɗin shine baki faɗa ba tuntuni saboda sakarci." Turo baki kawai Sarah tayi tana jin haushin rashin faɗa mata kwanciyar asibitin da Aina'u tayi. Har ƙasa Khalil ya duƙa ya gaida baba sannan ya gaida Lami, baba ne kaɗai ya amsa banda Lami don haushinsa take ji tunda Aina'u ta faɗa mata abunda yayi mata ranar ƙarshe da ta ziyarci Sarah. Ɗakin baba ya shige sukayi ta hira, yayin da Sarah ta shiga ɗakin Lami, tayi tayi Aina'u ta kulata amma ko kallonta bata yi ba. Da Lami kawai suka yi hira. Duba hamsin ta bawa Lami da kuma tsarabar da Hajiya ta bata, Lami kamar ta goyata tsabar murna. Baba ma dubu hamsin ɗin ta bashi da shadda ɗaya da zanin gado, albarka ya dunga saka mata. Anan idar da la'asar suka taho gida. Tun daga wannan rana Sarah ta soma wani irin rashin lafiya, gwajin farko da Khalil yayi mata ya nuna ciki, ɗaukarta yayi zuwa asibitin yayi mata scaning, sai ga cikin wata biyu har da sati biyu. Sosai take laulayi mai zafi wanda yaci uban na farko. Sau uku tana kwanciya a asibiti, abinci kuwa ko ƙamshinsa bata so, daga ruwan bohol sai fanta mai sanyi. Komai Khalil ke yi mata, wanka, wanki da gyaran ɗaki. Idan kuma yana asibiti, Laure ko Aunty Maryam ke yi mata. Wata ranar labara, tana kwance a akan kujera tana maida numfashi taji alamun ana murɗa handle ɗin ƙofa, tana ɗago kai tayi arba da ƙatuwar akwati Aina'u naja. Duk da bata jin ƙarfin jikinta bata san lokacin da ta tashi zaune ba tana bin akwatin da kallo............
Chapter 58 · 0% Book details