Sashe 35
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba tare da jin wani kunya ba _Khalil_ ya ciccib'i Sarah yayi waje da ita Lami biye dashi ita da Nuratu da Na'ima. Aina'u kuwa wani irin murmushi jin dad'in hak'arta ta cimma ruwa duk da bata tab'a kawo cewar abunda ya faru da Sarah zai iya faruwa da ita ba sanadiyar fad'uwar da tayi. Ita tayi ne kawai sabida mugunta. A baya ya shimfid'ar da ita, da sauri Lami da su Na'ima suka shiga cikin motar, _Khalil_ kuma ya zagaya ya shiga mazaunin gaba tare da tada motar ya bar unguwar da gudu ganin ba k'aramin jini ke zuba daga jikin Sarah ba. Baba kuwa kamar ya fashe da kuka, gashi babu k'afar bin bayansu. Sai dai abunda yayi matuk'ar bashi mamaki ganin Aina'u tana bin jinin Sarah da ya zuba a k'asa tana wani dariyar k'ata. Kwata-kwata bata lura da Baba dake bakin k'ofa yana kallonta ba. "Aina'u kar dai kece sanadiyar abunda ya samu y'ar uwarki yanzu?" Da sauri ta kalli inda baban yake a tsaye tare da fad'in, "Da aka yi yaya kenan Baba? Shikenan babu damar nayi dariya. To ni dariyata wani abu take nufi can daban." Juyawa Baba yayi tare da komawa d'akinsa don ya dad'e da sanin Aina'u ba k'aramar muguwar yarinya za ayi ba. Sai tace Lami bata yi komai ba a duniya. Amma abunda har yanzu ke bawa Baba mamaki shine, don me za tayi hakan? "Ya ubangijin sammai da k'assai, ga Baiwar ka nan ka jib'anci lamuranta. Allah ka bata lafiya." A bayyane yayi maganar yana mai d'aga hannu sama. A can asibiti kuwa, gudun laifi, tun kafun ya k'arisa ya fiddo baya tare da danna kiran number Hajiya domin shaida mata abunda ke faruwa. Don babu abunda gabansa ke yi sai fad'uwa ganin jiya-jiya suka gama kankara masa warning akan kar ya kuskura yace zai cire cikin dake jikin Saran. Ringing uku Hajiya ta d'aga tare da fad'in, "Assalamu alaikum." "Amin wa'alaikissalam, Hajiya dan Allah ki saka driver ya kawo ki asibitina yanzu. Saratu ce ba lafiya gamu tare da y'an uwanta zuwa asibiti. Fad'uwa tayi kuma jini ya b'alle mata." Da sauri Hajiya ta soma fad'in, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ai babu wani driver da zai kawo ni, tunda ga Muhammad Kabir a gida, bari na kira na fad'a masa abunda ke faruwa sai ya kawo ni." "To Hajiya nagode." Yana fad'in haka ya katse wayar tare da cigaba da driving da gudu yana yi yana juyowa yana kallon Sarah da ta jima da fita cikin hayyacinta sabida irin jinin da take zubarwa. Suna isa asibitin ya fito da sauri tare da bud'e gidan ya kuma ciccib'ota gaba d'aya jinin jikinta ya gama b'ata jikinsa amma ko a jikinsa. Cikin asibitin ya nufa da ita don ko tsayawa nurses su gunguro gadon marasa lafiya bai yi ba. Doctor Hayat, Doctor Nurain da doctor Kamal sune suka amshi Sarah tare da shiga da ita emergency kuma suka hana _Khalil_ shiga sabida ganin yanda ya rud'e, koma ya shigan ba wani abu zai iya yi ba. Mintuna goma tsakani sai ga Hajiya ita da aunty Maryam, aunty Khairat matar ya Barrister da shi kansa Barrister d'in. "Ina uwata take?" Fad'in Hajiya lokacin da ta k'ariso. Waro idanu tayi ganin gaba d'aya jikin _Khalilullah_ ya b'aci da jini. "Subhanallah!" Hajiya suka fad'i a tare ita da au aunty Maryam. Yaya Barrister kuwa cewa yayi, "Garin yaya haka ta faru?" _Khalil_ kuwa sai danne hawayen dake taho masa yake yi tare da fad'in, "Baban ne yace tayo masa kira na yana son magana dani, to naje ko zama ban kai ga yi ba, sai kawai jin talatin ta muka yi. Gaba d'aya muka fito muka taras da ita kwance a k'asa jini na zubar mata." Fuska cike da damuwa hajiya tace, "Kai Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Fad'uwa tayi kenan? Allah ya bata lafiya alfarmar ubangiji. Kai jama'a ni Mai gado!" Fad'in Hajiya tana da zabga tagumi. Can kuma ta kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Ka d'auke kaje gida ka canzo kaya sai ka dawo. Gaba d'aya jikinka ya b'aci da jini." " _Hajiya_ dan Allah kiyi hak'uri wallahi bazan iya yin ko taku d'aya ba har sai naga halin da baiwar Allah nan take ciki." Kallon Hajiya Barrister yayi tare da fad'in, "No, Hajiya kyale shi bari naje gidan na d'auko masa wasu kayan sai ya canza a cikin office d'insa." "Yauwa Allah yayi maka albarka. Maza je ka d'auko masa." Fad'in Hajiya. Aunty Maryam da aunty Khairat so suke su tambayi wacece babu lafiya, amma babu fuska wajen kowa don kowa cike yake da tashin hankali kar ma ace _Khalil_. Har yaya Barrister ya dawo daga gida ya kawo wa _Khalil_ kaya babu labarin Sarah. Sai da Hajiya tayi jan idanu sannan ya karb'i kayan ya nufi office domin canzawa. Sauri-sauri ya wanke jikinsa sannan ya saka kaya tare da fitowa. Duk k'aunarsa da turare yau ya manta anan saka wani abu wai shi turare a jiki. Nufa k'ofar emergency d'in _Khalil_ yayi gadan-gadan don ya gaji da tsayuwar gawon shanu. "kai! Maza dawo nan ka barsu suyi aikinsu. Idan ma ka shiga, mai za kayi." Fad'in Hajiya. Dawowa _Khalil_ yayi dai-dai lokacin da doctor Kamal shi da doctor Hayat. Da sauri ya nufeso tare da fad'in, "Ina Matata? How is she?" Da mamaki gaba d'aya suke kallonsa sabida Kalmar wife da ya kira don sun san bai da wata mata. Amma sai suka shanye mamakin. Doctor Kamal bai yi magana ba, doctor Hayat ne yace, "She's conscious now, amma tana buk'atar jini sabida ta zubar da jini da yawa. Sannan kuma I'm sorry to say, "She loose the baby. Babu cikin!" Zamewa _Khalil_ yayi ya duk'a a wajen tare da rik'e kansa yana nanata Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! "Kai, dakta mai ke faruwa?" Fad'in Hajiya ganin yanda _Khalil_ ya duk'e tare da kama kai yana salati. Barrister ya soma yi mata bayani don yaji komai, "Hajiya ita uwar ta farfad'o, sai dai tana buk'atar jini sabida ta zubar da jini da yawa, sannan kuma an rasa cikin jikinta." "La haula wala quwata illah billahi. To Allah yasa hakan shine alkhairi. Sai ayi gaggawa bata jinin ko. Amma kai dakta, ka tabbatar ba wani abu tasha ba cikin ya zube?" Fad'in hajiya tana kallon doctor Hayat. Girgiza kai doctor yayi tare da fad'in, "Gaskiya Hajiya babu wani abun da tasha wanda yayi sanadin fitar ciki. Mahaifar dama bata yi wani kwari ba. So sanadin mummunar fad'uwar da tayi ne ya jawo hakan." Dogon ajiye zuciya Hajiya ta sauke, don ta riga ta raya a zuciyarta in dai har zubar da cikin nan aka yi, to fa har abada d'anta ba zai auri Sarah ba ko da kuwa _Khalil_ d'in ne ya zubar da cikin. Mik'ewa _Khalil_ yayi tare da shiga cikin emergency d'in don har a lokacin ba'a fitar da ita zuwa ward ba. Kallonta ya dunga yi ganin lokaci k'ank'ani har tayi wani irin mugun rama tayi haske. Da sauri ya juya ya fita tare da nufa lab domin a d'ibi jininsa don jininsa irin wanda zai iya bawa kowa ne idan aka cire O-negetive. Leda biyu aka d'iba a jikinsa. Tuni har an maida Sarah d'akin hutu an kuma d'aura mata jinin _Khalil_. Lami kuwa da y'ay'anta sai tararrabi akan hukunci da za su yanke ganin cikin jikin Sarah ya zube. Lami kwata-kwata damuwarta ba rashin lafiyar Sarah bane. Damuwarta d'aya kada jin dad'in nan da suka soma samu a jikin _Khalil_ ya yanke sakamakon zubewar cikin jikin Sarah d'in. Sam basu gane yanayin Hajiyar ba, don fuskanta babu yabo kuma babu fallasa. Hajiya bata bar asibitin nan ba, sai da Sarah ta farfad'o sosai har tana ina gane kowa da kowa lokacin har anyi sallar magriba. Amma su Aunty Maryam tuni ya Barrister ya maida su gida sabida girkin da za'a kawo nan asibitin. Ya Abdul-Hakeem ne ya kawo abincin a cikin manya-manyan kula masu matuk'ar tsada sannan ya d'auki Hajiya ya mayar da ta gida. _Khalil_ kuwa sallar magriba ce ta fitar dashi, don tun tuni yana gefen Sarah tana yin motsi yake soma tambayarta ko wani wajen nayi mata ciwo. Sarah kuwa tun da ta samu labarin cikin dake jikinta ya zube, wani irin numfashin rahama da natsuwa ta sauke tana mai godewa ubangiji don ita kad'ai ta san halin da take ciki. Sam bata son shiga cikin sahun y'an uwanta na ajiye d'a ko y'ar shege. "Allah na gode maka da ka cire cikin ta hanyar mafi sauk'i. Allah na gode maka." Duk a cikin zuciya tayi maganar. Baba kuwa na can hankalinsa a tashe jin babu wani feedback game da Sarah. Sai da yayi kamar zai yiwa Aina'u kuka sannan ta kira masa Lami kasancewar shi bai da waya. Shi d'in ma sai da ya bata dubu d'aya sannan ta kira. Bayan sun gama waya da Lami ta fad'a masa halin da ake ciki, sai ya mik'awa Aina'u wayar dake tsaye tana jin matsanaicin farin ciki jin ciki ya zube. "Shegiya! Ai nayi wa kaina alk'awarin sai na raba ki da _Ibrahim_. Wallahi ba zan bari ki shiga gidan na ba. Mayya kawai!" Tana gama fad'in haka ta juya ta fice daga d'akin tare da komawa nasu d'akin ta kwanta a kan gado tare da jawo ledar tsire mai kulin da ta siya ta hau jefawa a baki tana tauna tana lumshe idanu. A can asibiti kuwa, wajajen k'arfe tara da rabi, bayan su Lami sun gana hani'an da abincin da Hajiya ta saka su aunty Maryam suka yi, sai _Khalil_ yace masu ya kamata su tashi ya kai su gida, don mutum d'aya aka amince ya kwana da majinyaci. "Lami tunda ga yara a gida, ku tafi kawai ke da Nuratu, ni zan kwana anan da ita." Lami ji tayi kamar ta shak'o Na'ima, amma jin abunda _Khalil_ yace sai tayi shuru. "Eh hakane. Mama ke ki koma gida, ita sai ta kwana da itan. Idan yaso gobe sai ku dawo da safe. Dare nayi. Muje na sauke ku a gida." Fita Lami tayi ba tare da ta k'ara cewa komai ba. Don gani take kamar wani abun dad'in Na'ima zata ci idan ta tafi. Ko kuma _Khalil_ d'in yayi