← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 112

Sashe 36

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

mata wani kyauta. Har gida ya sauke su tare da shiga wajen Baba ya kwantar masa da hankali tare da shaida masa in Sha Allah nan da wasu y'an kwanaki Sarah zata warware. Hajiya tana isa gida ta d'aga waya ta kiran number d'in ya Abdullah. Kamar kullum ya yanke kiran tare da kiranta. "Assalamu alaikum, marmari sai kaji abunda ya faru ko?" Fad'in Hajiya. "Wa'alaikissalam, Muhammad Kabir ya kira ni ya fad'a min komai, amma Hajiya an tabbatar da a asibitin ba wani abu tasha ba? Don jiya kamun na bar Kaduna sai da na wakilta wad'anda zasu min bincike yarinyar. Kuma binciken ya iske ni tun a jiyan. Hajiya maganar dai babu dad'in ji, don sai da nayi dana sanin amincewa da wannan maganar auren. Don fisabilillahi gaba gidan tun daga kan uwarsu babu tarbiya. Dama-dama ita yarinyar ma, an samu mutane hud'u zuwa biyar da suka yabi halinta." Shuru hajiya tayi tana sauraran ya Abdullah kamun tace, "To marmari ya za muyi, _Khali_ dai ya riga ya jawo mana magana. Tunda har yaji ya gani, kuma ita yarinyar ta samu shaida ko yaya ne, hakanan za muyi hak'uri ayi auren kawai don nan gaba bamu san wani irin magana zai je ya d'auko mana ba. Kuma maganar ciki, dagaske b'ari tayi amma ba ta hanyar shan magani ba. Allah ne ya kawo hakan ta sanadin fad'uwa da tayi." Ajiyar zuciya ya Abdullah yayi tare da fad'in, "To shikenan Hajiya. Tun da har hakan ya kasance, ba sai an d'au wani dogon lokaci ba, da zarar Yarinyar taji sauk'i, zan zo Kaduna sai muyi magana dasu uncle Ridwan sai aje a kai kud'in auren." "Kaga inda matsalar take kenan. Allah yasa dai kar su tada k'ananun maganganu dai!" Fad'in Hajiya, "Ki kwantar da hankalinki, in Sha Allah baza a samu matsala ba." "To Allah yasa!" Fad'in Hajiya. A can asibiti kuwa, sai da gaba d'aya nurses suka fahimci Sarah budurwar _Khalil_ ce sabida yanda yake nan-nan da ita. Kwanan Sarah uku a asibiti, amma ko sau d'aya Aina'u bata tab'a zuwa dubata ba. A asibitin nan kuwa, wani irin soyayya ce da shak'uwa mai zafi ta shiga tsakanin Sarah da _Khalil_ ta yanda har idan bata ganshi ba, ta dunga kallo agogo tana kuma duban hanya. Da taji motsin bud'e k'ofa take saurin kai idanunta wajen. Satinta biyu aka sallameta, baza ka tab'a cewa daga ciwo ta tashi ba sabida wani irin haske da kyau har da d'an k'iba da ta k'ara. Cike da murya da farin ciki ta isa d'akin Baba tana mai jin kewarsa. Abunda ya bata mamaki ganin Baba a tsaye babu sandar da yake dogarawa. Da mamaki take kallon Baba har da zagaya shi. Dariya yayi tare da fad'in, "Bar mamaki Sarah, mahaifinkin ne dai a tsaye gabanki. Kin ga ikon ubangiji ko? Allah dai ya yiwa _Ibrahim_ albarka domin shi ya zo ya d'auke ni ya kai nj asibitinsa na k'ashi aka duba k'afata. Kuma har gida kullum ake zuwa ana min gashi. Kuma Alhamdulillah k'afar ta soma warkewa don yanzu haka zan iya zagaye tsakar gidan nan babu sanda." Da matsanaicin farin ciki Sarah ta soma fad'in, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!!, Allah mun gode maka. Baba Ashe zaka samu lafiya? Kai Alhamdulillah." Baba yace, "Ki godewa ubangiji sannan ki godewa _Ibrahim_ Saratu. Domin sanadinsa ne kika ganni a haka yau a gabanki. Saratu don girman Allah, kiyiwa yaron nan biyayya, babu abunda za kiyi ki b'ata min rai Sarah kamar ki k'i yin zaman lafiya dashi. Hakan zai b'ata min rai kuma zan rik'e ki a zuciya domin yaron nan ya gama yi mana dukkan alkhairi shi da iyayensa." Sarah wani irin matsanaicin soyayyar _Khalil_ ne taji yana hud'a ko wani sak'o da lungu na zuciyarta. D'ukawa tayi tare da fad'in, "Baba nayi maka wannan alk'awarin na zama da _Khalil_ da zuciya d'aya, kuma ko da sab'ani ya shiga tsakanin mu wata rana, ba zan tab'a juya masa baya ba. Kuma ba zan tab'a rabuwa dashi ba har sai idan shine ga gaji da zama dani." "Allah yayi maki albarka Saratu. Allah yasa auren da za kuyi mutuwa ce zata raba shi." Sai da Sarah ta saka gyale ta rufe fuskanta sannan tace, "Ameen" tare da mik'ewa ta fita daga d'akin ta koma nasu d'akinsu ta d'auko wannan turaren da _Khalil_ ya bata tare da fesawa sosai sannan ta canza hijjab ta saka wani don a waje suka bar _Khalil_ d'in. Sarah tayi alk'awarin yau zata bayyanawa _Khalil_ baki da baki cewar tana sonsa. A tsaye a k'ofar gidan ta same sa yayi folding hannunsa yana kallon k'ofar gidan. Tana fitowa ya saki ajiyar zuciya tare da fad'in, "Har na k'agu ki fito." Murmushi tayi tare da fad'in, "To ba yanzu muka rabu ba." "To ba kece kika ce kar na wuce na jira ki ba. Na k'agu inji mai zaki fad'a min." Murmushi ta k'ara yi karo na biyu tare da fad'in, "Wai sanyi kake ji?" Harararta yayi tare da fad'in, "K'arshen sanyi, a Atlanta nake." Dariya ta saki wanda ya k'ara bayyanar da bayyannar kyawunta, gaba d'aya kumatunta sai da suka lob'a. "Ban da Allahn musuru, amma ina ji a jikina da d'a ko y'ata ya fito duniya, da dake zai yi kama sak. Ke kyakkwa ce." Rufe fuska tayi da hijjab d'inta tare da fad'in, "Har na kai ka kyau? Kai fa kama kake min da wannan matashin kudancin indian _Ram Charan_" waro idanu _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Haba dai! Ke kuma kin san dawa kike kama, _Aishwarya Rai_, wallahi kin ma fita kyau." Rufe baki Sarah tayi tare da fad'in, "Kar ka yarda Na'ima taji, don ita ce aka cewa suna kama da Aishwarya." "Wa, to ai kin fita kyau wallahi." Dariya tayi tare da fad'in, "Beauty is in the eyes of the beholder." "Eh d'in naji, ko ma dai menene, ke d'in kyakkyawa ce kuma ta musamman. Wani albishir za'a fad'a min ne aka hana ni tafiya gida." Sai da Sarah tayi farr da idanu sannan tace, "Abunda kake muradin ji kullum daga baki na kuma fuska da fuska." Gyara tsayuwa yayi tare da fiddo wayarshi ya danna recording ba tare da ta san me yayi ba. "Gwara in gyara tsayuwa da kyau kar inzo in fad'i in suma don dad'i." Dariya tayi tare da fad'in, "Ba zan bari ka kai k'asa ba zan taro ka. Idan har ina waje, baza ka tab'a fad'uwa ba in Sha Allah!" Da mamaki yake kallonta don bai tab'a tsammani zata iya magana haka ba. "Yanzu kina da k'arfi taro ni?" Ya tambaya yana mata gwalo. "Ba da k'arfin cin tuwo zan rik'o ka ba, zuciyata ce zata rik'o ka. Ka manta kai da kanka ka fad'a an halicceni ne domin kai, kuma kai ma an halicceka ne domin ni? To ai zuciyoyinsu a had'e suke kuma tare suke bugawa kuma gangan jikinmu a tare suke sarrafuwa, sabida haka d'aya ba zai tab'a barin d'aya ya fad'i ba. Ka saka hakan a ranka." Mutuwar tsaye _Khalil_ yayi yana jin maganganunta na shiga ko wani sak'o da lungu na jikinsa har sai da tsikar jikinsa ya tashi. Wani irin kallon k'auna ya dunga binta dashi kamar zai had'iyeta. "Ina sonka _Khalilullah_, Ina k'aunarka har cikin zuciyata." Dum yaji wani abu kamar guduma ya bugi dodon kunnensa, wani irin shauk'i na mamaye ilahirin jikinsa. Ji yake dama yana da dama da jawota zai yi jikinsa ya rungume sosai. Aina'u dake lab'e jikin k'ofa tana sauraransu, don tun lokacin da Sarah ta fita ta biyota a baya. Wasu irin ruwan hawaye ne ke gudu a fuskanta. Ji take kamar ta koma cikin gida da gudu ta d'auko kaifaffiyar wuk'a ta soki zuciyar Sarah dashi ta tafi ta bar duniyar. "Sarah, nagode ba wannan alfarma da kika min na sanya ni cikin zuciyarki da kuma bani damar kasancewa dake har mutuwa. Ina so ki sani, zan killaceki a nan, (yayi nuni da zuciyarsa), ba zan tab'a bari kiyi hawayen bak'in ciki ba, idan har za kiyi hawaye, to na farin cikine, nayi maki wannan alk'awarin. Zamu dunk'ule mu zama d'aya Sarah. Zan tarairayeki ta yanda ko bugun zuciya mai k'arfi bazan bari kiyi ba. Zan kula dake fiye da yanda ake ririta kwai. Zan mayar dake sarauniya, sannan in kasance bawanki. Sarah baki ba zai iya musulta yanda zanji dake ba. Allah ya nuna min ranar da zan mallakeki matsayin mata. Wannan ranar kawai nake jira. Zan gwada maki practically abunda ake nufi da k'auna. In Sha ni da ke, _couples for eternity_ ne. Rayuwar aurena dake, babu condition Sarah, unconditional love nake maki Sarah. Ko da zaki zama mara k'afa da hannu, soyayyarki baza ta tab'a canzawa ba a gare ni. Allah yayi mana jagora." Hawayen farin ciki kawai Sarah take yi, bata tab'a tunani ko cikin mafarki akwai wanda zai iya fad'a mata wad'annan kalaman ba. Ashe dai ita ma za tayi farin ciki a rayuwa. "Wallahi idan har ina da rai, ni Aina'u ba zan tab'a bari alk'awarin daka d'auka ya zama cikakke ba, ba zan tab'a bari kuyi farin ciki ba nayi maku wannan alk'awarin." Aina'u ta fad'i cikin zuciya tare da saurin barin wajen tana kuka don kalaman da _Khalil_ ke fad'awa Sarah ba k'aramin k'ona zuciyarta yake yi ba. Sarah da _Khalil_ kuwa basu san da ita ba, sai cigaba da kwararo kalaman love wa junansu suke yi har kusan goma na dare sannan suka yi sallama kamar kar su rabu. Bayan da ta dawo d'aki kuma, _Khalil_ na isa gida suka dasa soyayyar ta waya. Bayan sati biyu da sallamo Sarah, Ya Abdullah ya diro Kaduna, ko sauka gidan Hajiya bai yi ba, kai tsaye ya tafi family house d'in mahaifinsu domin ganawa dasu Uncles d'in nasa akan batun auren _Khalil_ d'in kuma dama tuni sun d'an fara maganar a waya. Kasancewar suna d'an shakkarsa, basu wani tattada jijiyoyin wuya ba, sun tsayar da magana akan zuwa gobe sai suje can gidansu iyayen Sarah a tsayar da magana. Bayan Ya Abdullah ya dawo gidan Hajiya, sai ya sanar mata yanda suka yi da Uncles d'in nasa. Sosai Hajiya taji dad'i jin babu wani tashin hankali da aka yi, duk da ta san dama basu cika yin haukar da suka
Chapter 36 · 0% Book details