← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 112

Sashe 65

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Una no hear wetin I say before we come here? I tell u say make u no fear if you see anything, because _Hell Ofulafo_ dey look you through here." Yayi mata nuni da ramin hancin gunkin. Ai sai Aina'u ta ƙara kiɗimewa! Wani sautin mara daɗi ciki wani harcen yare ya soma magana a kausashe, take Ugo ya kai ƙasa tare da yin sujada sau uku sannan ya miƙe ya harɗe hannayensa kamar mai neman gafar ya shiga magana cikin yare na kusan sakan sittin sannan ya yuyo ya kalli Aina'u tare da soma yi mata magana da gurɓataccen turanci, "Hell yace ace maki idan baki shirya ba, ki koma gida, idan kuma kika ƙara tsorata anan wajen sai ya maida fuskanki tana kallon ƙeyarki, idan kuma kin shirya kiyi sujada a gaban gunkin nan sau uku." A take Aina'u taji duk wani tsoron da take ji ya fece musamman da ta tuno korar karen da Sarah tayi mata daga gidanta. Zubewa tayi tare da yiwa gunkin sujada sau uku, ana ukun ba tare da ta ɗago ba taji wani irin guguwa mai ƙarfi ya taho ya lulluɓesu, bata kuma buɗe idanunta ba sai a gaban wani garjejen tsohon inyamure jikinsa gaba ɗaya guraye ne, ya kasance irin zabiyan nan ne, domin idanunsa ma basa tsayuwa waje ɗaya. Gaba ɗaya jikinsa yayi ƙuda-ƙuda. Kallo ɗaya yayi wa Aina'u ta soma jin wani irin zawo. Wani mummunar dariya ya ɓarke da ita tare da soma surkulle cikin yaruka daban-daban. Wani ƙatoton tulu ne ya bayyana a gabansa, kallon Aina'u yayi sannan ya kalli tukun sai ga Aina'u cikin tulun, gaba ɗaya komai ya faru ne cikin daƙiƙu biyu. Jan zare ya ɗauko tare da jan mayafi ya kulle tulun tare da ɗauresa. Da sauri Ugo ya miƙe tare da yiwa _Hell Ofulafu_ sujada sannan ya soma tafiya da baya da baya har ya fuce. Sai da Aina'u ta kwana bakwai cikin tulun nan sannan tulun ya face sai gata a watse a ƙasa daga ita sai ɗaurin ƙirji da baƙin zani da jan ɗan kwalin da bai rufe tsakiyar kanta ba. Sai da ta kwashi mintuna talatin tana kwance ko motsi bata yi sannan _Hell Ofulafu_ ya miƙa tare da ɗaga hannu sama sai ga ƙaramin tulu a hannunsa, hannunsa mai tsini ya caka a jikin tulun, take ya soma tsiyayar da jini mai kauri da wari shi kuma ya shiga zagaye Aina'u da tulun sau bakwai. A firgice ta farka tana mai buɗe baki tana shan jinin nan dake tsiyayowa daga cikin tulun. Bayan ya gama wannan ya jawo wata tulun mai ɗauke da wani irin ruwa mai ya ajiye a inda take tare da saka hannu ya fizge zanin jikinta da ƙarfi. Wani abu ya ɗauko mai kama da kofi sannan ya ɗaga hannunsa sama sai ga wata murtukekiyar bulala, idan ya tsiyaya mata ruwan sai ya shauɗa mata bulalan sau biyar a ko ina na jikinta. Sai ruwan nan ya ƙare tas a jikinta, gaba ɗaya jikin nata yayi wani irin ruɗu-ruɗu. Aina'u tayi suma ya kai goma saboda azaba. Ugo na gefe yana kallon komai, kuma dama ya san sai _Hell Ofulafu_ yayi mata hakan, ta hakane yake cire sauran imanin dake jikin duk wanda ya kawo kansa wajensa. Shi da kansa ya barbaɗa mata wani magani a jiki tare da kallon Ugo yace masa ya kaita masaukinta idan ta gama warwarewa sai su dawo ta faɗi buƙatunta. Ugo mai mayar da ita ainahin cikin garin Abia ba saboda nisa, wani bukka ya kaita suna kwana tare, kuma bai barta haka ba kullum sai ya kwanta da ita. Tana ji kuma tana gani amma bata da ƙarfin da zata iya dakatar dashi. Sai da ta kwana goma sha biyu kamun ta samu lafiya. Babu abunda ke huruwa cikin zuciyarta sai wutar ƙiyayyar Sarah da kuma ƙudurin ɗaukar fansa, don duk abunda ya faru da ita a garin Abia kacokan ta ɗaurawa Sarah laifi. Shikuwa Ugo sai sunne-sunne yake yi ya ɗauka Aina'u za tayi bala'i akan kwanciya da ya riƙa yi da ita duk da kuwa ba budurwa ya sameta ba, amma sai ya ga ko kallonsa bata yi ba idan banda ma takura masa da tayi akan su koma wajen _Hell Ofulafu_. Suna shiga ta taras dashi yayi zaman yoga idanunsa a rufe, zama suka yi suna jiran ya gama abunda yake yi, sai da ya kwashi awa guda shi ba a ƙasa ba kuma ba'a sama ba. A tsawace yayi magana da wani yare yana kallon Aina'u da idanunta ke a ƙasa. A kunnanta Ugo ya raɗa mata, "He say make u look his eyes." Ɗagowa tayi suka haɗa idanu dashi, take taji wani zafi mai tafe da raɗaɗi na shiga idanunta. Cikin yare _Hell Ugo_ yace cikin yare, "Naga muradinki a cikin idanunki, surukar yayarki, ƴar aikin gidan, da kuma ita kanta yayar taki, kina so a shiga tsakanin su sannan kuma kina son koma gidan, kuma mahaifiyar mijin yayarki da kika mutu akansa kike so ta buƙaci dawowarki gidan da kanta." A kunne Ugo ya fassara mata. Cikin sauri ta shiga jinjina kanta. "Ajiye rabin miliyan ki tafi." _Hell Ofulafu_ ya faɗi yayin da Ugo ya faɗa mata abunda yace, take ta ajiye masa kuɗin kasancewar tazo dasu. Da hannu ya nuna masu su fita. Bayan sun fita can bukkar suka koma, a ranar ma sai da Ugo ya kuma amfani da ita, washa gari ɗan taxi yazo suka koma can cikin garin Abia, kasancewar ta gaji sosai, bai bata bi motar dare ba, a daren ta yanki tiket ɗin jirgin da zai tashi ƙarfe goma. Yau ya kasance ranar asabar Khalil baya zuwa aiki, zaune suke akan dinning suna cin lunch wanda Khalil ne ya dafa masu wata taliya mai uban romo wai ita Paraguay fried superghetti. "Ni dai tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin fried superghetti da ruwa a jikinta ba." Faɗin Sarah bayan ta kalli plate ɗin dake gabanta. "Daɗina dake baki da fahimta wani lokacin. Ance maki sunansa Paraguay fried superghetti!" Jinjina kai Sarah tayi tare da faɗin, "Eh tabbas nagane!" Yanda tayi maganar da shaƙiyanci ya saka Khalil ya zaburo ita kuma ta miƙe da sauri suka shiga zagaye dining ɗin. Daga ƙarshe dai ya kamata tare da cicciɓanta suka yi sama yana faɗin, "Kin ce taliyar babu daɗi amma har da su kashe kwano." "Nifa bance babu daɗi ba, kawai romon ne yayi yawa." Faɗin Sarah dai-dai lokacin da ya sauke ta tsakiyar gado tare da faɗin, "A taimakawa likita yaji ɗumin matarsa, kwana biyu ana ta yi min rowa." Miƙewa tayi tare da faɗin, "Nima ina son jin ɗumin nawa mijin, bari nayi fitsari na dawo." Shafa cikinta da ya ɗan turo tare da faɗin, "A siyar min da fitsarin" Da sauri ta sauko daga kan gadon tare da faɗin, "Ka san dai fitsarin mai ciki bai riƙuwa ko?" Ta faɗi hakane tare da saurin shiga bayi, yanda fitsarin ya matseta ya saka tana shiga ta ɗuka a ƙasa ta soma fitsarin. Wani irin bugawa zuciyarta yayi tare da zaro idanu tana kallon jajayan mitsi-mitsin ƙananan tsutsotsin dake fitowa daga cikin gabanta, miƙewa tayi tare da kwala wani uban ƙara ganin tsutsotsin kamar tuttuɗosu ake yi.............
Chapter 65 · 0% Book details