Sashe 83
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaye take a tsakiyar ɗakin tana wani irin dariya mai tafe da hawaye baƙin ciki da kuma farin ciki lokaci guda, domin bayan tsawon shekara ɗaya har da wata uku, jiya da daddare _Hell Ofulafu_ ya dawo mata da makamanta, yanzu tana iya ganin komai ta tsakiyar tafin hannunta, sannan tana iya magana da _Hell_ da wannan mummunar halittar duk ta tafin hannun nata. Tsafinta ya ninku yanzu ta yanda tana iya ganin mutum idan taso har a jikin bango, sannan ta jikin bangon zata iya yi masa duk abunda taga dama, yanzu haka ma, tana kallon Sam'an da Sauban dake tsere a parlour, pampers ne kawai a jikinsu, tuntuni Sarah ke so tayi masu wanka amma da wannan yayi can, sai wancen ya zille yayi can, Khalil na zaune kan kujera sai dariya yake yi mata kuma yaƙi tashi ya taimaka ya kamo mata su, shekaransu ɗaya da wata uku cif, amma wayansu ya zarce tunanin mai karatu, ga magana a bakinsu kamar uwar aku. Idan Sarah ko Khalil suna so su tantancesu, sai su kira suna, misali sai suce Sam'an! To Sam'an ɗin ne zai juyo Sauban kuma harkan gabansa zai cigaba dayi kasancewar ko ita kanta Sarah sai tayi dagaske take bambance su, daga baya kamar sun gane, idan aka ce Sauban ko Sam'an, sai gaba ɗaya su juyo. Khalil ruɗewa yake yi sai ya shiga tambayar Sarah, "Dan Allah wanene Sam'an, wanene Sauban a cikinsu?" Taɓe baki take yi tare da faɗin, "Ka gano da kanka ai kai babansu ne, idan a waje aka tambaye ka yaya za kayi?" Sai Khalil yace, "To ai shiyasa nake son ki bambance min tunda ke kina gane su gudun kar inji kunya watarana!" Idan ya faɗi hakan sai ta nuna su ɗaya bayan ɗaya, ita kanta tana ganesu ne da ɗabi'unsu, Sauban yana da faram-faram kuma yana da dogon fuska, Sam'an kuma bai cika faram-faram ba, kuma fuskansa bata kai ta Sauban ɗin tsayi ba duk da shima dogon fuskan garesa, babu abunda suka ɗauko na Sarah idan ka cire dimple, amma bayan haka kaf kamannin Khalil suka yo. Wani kalan murtuke fuska Aina'u tayi ganin yanda Sarah da Khalil suke wasa suna zagaye parlourn su da ƴan biyun nasu. "Wannan shine ƙarshe farin cikinki a cikin gidan nan, ni Aina'u sai na baƙanta maki fiye da yanda kika baƙanta min, sai na wulaƙanta rayuwarki, sai na saka ki hawayen jini, sai na ruguza zuciyarki, sai na ɓalɓalta rayuwarki dana ƴaƴanki, sai na kashe ki da baƙin ciki, sai nayi kwanciyar aure da mijinki a gaban idanunki, sai na zama kishiyarki, na kuma ƙasƙantar dake. Babu aure tsakanina da mijinki, amma na rantse da Ubangijin mu Yesu Almasihu mai ceto, sai nayi tarayya da mijinki kuma a cikin gidan nan a gaban uban kowa, kuma duk wanda yace zai kawo mi shamaƙi ko shishshigi, sai na kashe shi!" Tana gama faɗin haka ta ɗauko wani icce wanda aka ɗaɗɗaure shi kamar ƴar tsana sannan ta jawo wani tulu daga ƙasan gado mai ɗauke da wani irin baƙin ruwa mai kauri sannan ta ambaci sunan Khalil sau uku sannan ta tsunduma iccen nan har sai da guiwar hannunta ya shige ciki sannan ta fiddo hannun, wani mugun murmushi ta saki tare da saka ɗayan hannunta ta fizgi gashin kanta sannan ta tura a cikin ramin idanun wannan iccen da ya koma ƴar tsana amma bana itace ba, sannan ta tsaki saitin zuciyar ƴar tsanar nan har sai da hannunta ya lume tare da ambatan sunanta sau uku sannan ta saki ƴar tsanan cikin tulun ya bata sautin 'tsumbul', sai ta mayar da tulun ƙarkashin gado tare da duƙawa ƙasan guiwowinta ta leƙa ƙarƙashin gadon ta jawo wasu ƴan tsanar guda biyar, ɗaya bayan ɗaya ta riƙa tsaka wani abu mai tsini a ƙahon zuciyarsu sannan ta jefa cikin tulun nan ta miƙe tana jin wani irin matsanaicin farin ciki ganin gaba ɗaya ɗakin ya turniƙe da hayaƙi da kuma wani irin duhu, can kuma bayan mintuna talatin komai ya washe, kuma dama _Hell_ yace idan har hakan ta faru bayan kammala aikinta, to hakan na nufin aikinta yayi! Khalil ya kai hannu zai cafki Sarah dake ƙoƙarin kama Sam'an yaji wani irin abu kamar mashi ya soki zuciyarsa da ƙarfi, wani irin baya yayi zai faɗi Sarah ta kai hannu ta riƙosa amma duk da haka sai da suka kai ƙasa saboda gaba ɗaya jikinsa ne ya saki. A ruɗe ta shiga kiran sunansa tana jijjigasa har hawaye ya wanke fuskanta, ƴan biyu kamar sun san abinda ke faruwa sai suma suka zagaye Khalil ɗin suna jijjiga cikinsa, shi kuwa duk yana jinsu, amma sai ya rasa shin a wani duniya yake, a hankali yaji zafin zuciyar na raguwa, can kuma sai ya soma jin wani baƙon al'amari na shiga zuciyarsa, kuma ya rasa shin farin ciki yake yi ko akasin haka. Zuwa can sai ya miƙe da sauri yana mai riƙe kansa, "Happy lafiya? Mai ke damunka?" Sarah ta faɗi tana mai kai hannu goshinsa, twins ma da gwarancinsu suka haɗa baki suka ce, "apy yafila? (Happy lafiya?)" Murmushi Khalil yayi tare da dungure masu kai yana faɗin, "Dan gidanku, daddy ba apy ba." Murmushi ƙarfin hali Sarah tayi don gaba ɗaya hankalinta bai jikinta, duniya bata ƙaunar Khalil yayi ciwo don bai iya ciwo ba. Kamun yayi yana jimawa, amma kuma idan ya tashi yi, kamar ba zai yi raiba haka yake. Tashi yayi tare da faɗin, "Kaina ne ya ɗan sara min, amma nasan ina shan magani zai tafi, bari naje na ɗan huta kamun lokacin sallah yayi." Gyaɗa masa kai kawai Sarah tayi jiki duk sake. Kumatunta ya kama tare da faɗin, "Smile now! Ba mutuwa zanyi ba, muna nan tare mutuwar ma baza ta raba mu ba, tare zata ɗauke mu." Duk da haka yaƙe kawai tayi, shi kuma ya hau sama ya barsu nan parlour. Jiki a sanyaye Sarah ta wuni, aikin ma dai kawai yinsa take yi. Shi kuwa Khalil, koda ya koma ɗakinsa, bai iya baccin ba, tunani kawai ya riƙa yi, can kuma ya sauko don haka nan yaji yana son zuwa side ɗin Hajiya. Saukowa yayi lokacin Sarah na ɗaya parlourn ita da yara, ba tare da ya neme su ba ya fice abunda bai taɓa yi ba. Ita kuwa Sarah bata san da fitarsa ba, ta ɗauka har a wannan lokacin yana sama a ɗakinsa. Aina'u kuma tana fitowa daga ɗakita, kai tsaye ɗakin Hajiya tayi hannunta riƙe da wani baƙin padlock, ba tare da knocking ba ta murɗa handle ɗin ƙofar da ƙarfi tare da faɗin, "Hajiya!" A razane kasancewar ita nata sihirin _Hell_ yace sai ta firgita tukun zai kamata. A razane Hajiyar ta juyo, cikin sauri Aina'u ta ɗaga padlock ɗin tare da datse shi tana dariyar samun nasara. "Aina'u kina buƙatar wani abu ne?" Hajiyan ta samu kanta da faɗin haka. Aina'u kuwa domin tabbatarwa sai cewa tayi, "Buɗe bakinki ki tsaya a haka." Nan take Hajiyar tayi kamar yanda Aina'un tace. Wani irin dariya Aina'u ta saki tare da faɗin, "To rufe bakin." Tuf Hajiya ta rufe tana mai bin Aina'u da idanu. Zaro mata idanu Aina'u tayi tare da faɗin, "Bar kallo na!" Da sauri Hajiya ta sunkuyar da kai ita kuma Aina'u ta maka mata harara tare da faɗin, "Da ace lokacin da na kira ki a waya domin ki dakatar da ɗanki ga auren yayata, kin dakatar, da yanzu kina zaune cikin lumana babu tashin hankali, amma tunda baki yi hakan ba, yanzu aka soma wasan!" Tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin tare da fitowa parlour dai-dai lokacin da Khalil ya turo ƙofa ya shigo, idanu huɗu suka yi da juna, wani irin ajiyar zuciya Khalil ya sauke tare da sakarwa Aina'u wani irin murmushi wanda ya kusa sumar da ita. "Aina'u!" Ya kira sunansa cikin wani irin salo, "Na'am Khalilullah mijin Saratu!" Ajiyar zuciya ya kuma saki for the second time sannan ya zauna tare da faɗin, "Zauna mana Ai'n." Yanda ya gajerta sunanta sai taji kamar duk duniya babu wanda ya iya kiran sunan kamarsa, zama tayi daf dashi kasancewar a 2sitter ya zauna, fuskantar yayi tare da faɗin, "Oh, Ai'n kamar ba cikin gidan nan kike ba, ko zuwa wajen ƴar uwarki bakya yi balle a haɗu a gaisa." Wani farrrrr da idanu tayi tare da faɗin, "To ai ku ɗinne love bird, sam baku buƙatar irin mu masu hana ruwa gudu kusa daku, kullum kafi son ganinka naniƙe jikin matarka." Kau da maganar yayi tare da faɗin, "To yanzu dai muna gayyatarki shashinmu domin taya mu hira." "As you wish, your excellency!" Dariya Khalil yayi tare da faɗin, "Sai kace wani gomna. Mu dai muna jiranki, na miƙa maki katin gayyata kullum da daddare kike zuwa kina taya mu hira!" Faɗin Khalil. "An gama ranka ya daɗe." Faɗin Aina'u. Daga nan Aina'u ta riƙa jansa da hira, sai ga Khalil har da kyakyatawa. Kamar yanda Khalil ya buƙata, da daddare sai ga Aina'u cikin wani irin mahaukacin kwalliyar ɗaukar hankali, gaba ɗaya suka kan dinning suna cin abinci ta murɗa handle ta shigo, Khalil ne ya fara juyawa fuskansa ɗauke da murmushi yana mai faɗin, "Ƙariso nan Aina'u ayi dinner ɗin dake. Sauban na riƙe a wajensa, jin muryan Aina'u duk sai ya rikice yana neman guduwa wajen uwarsa, Sam'an dake wajenta riƙe hannunta yayi gaam jikinsa na rawa. Sarah kuwa murmushi tayi tare da faɗin, "Aina'u kenan, kamar ba gida ɗaya muke ba! Ko kin koma gida ne?" Taɓe baki Aina'un tayi tare da faɗin, "Baki so gani na bane kawai." Ta faɗi hakane tare da jawo kujeran kusa da Khalil ta zauna a kai tare da kallon Khalil ɗin tare da narke fuska. tana mai faɗin, "To ayi serving ɗina mana, ko da kaina zanyi." Cikin sauri Khalil ya miƙe tare da ajiye Sauban, shi kuwa dama abunda yake jira kenan da gudu ya nufi gun mamarsa yana kuka, ita kuwa Sarah wani irin maɗaukakin mamaki ne ya rufeta ganin yanda jikin Khalil yake rawa don kawai zai zubawa Aina'u da basu taɓa ga macijiba abinci. Sai kawai ta zuba idanu tana kallon ikon Allah. "Ai'n ga couscous, ga jellof rice, wanne za'a