← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 112

Sashe 4

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 5 min read

nan waje." Gaba d'aya suka k'ame k'am kamar an dasa bishiya. Mintuna kad'an sai ga Lami ta fito hannunta d'auke da iPhone 7plus a hannunta ta mik'awa *Naliliyo* har da d'an duk'awa. Fizge wayar yayi tare da nuna Lami da hannu sannan yace, "Ki hawa kafurin d'an ki kunne, wallahi ko da wasa na k'ara ganinsa ya gitta ta k'ofar gidan mu, to gawarsa ma sai tayi maki wuyar gani." Yana gama fad'in haka ya juya ya fice daga gidan. Na'ima ta saki dogon tsaki tare da fad'in, "Wannan d'an iskan wata rana sai ya jawo mana abunda zai saka a k'ona mu da ran mu a cikin gidan nan. Kullum fa sai kin bashi kud'i amma duk da haka sai ya fita ya jawo mana magana. To gashi nan dai yau ya d'auko mana maganar *Naliliyo* har yana ikirarin zai kashe shi. Wallahi kiyi masa magana Lami ya fita harkan gidan jarababben d'an DABAN nan. Tom!" Kamun Lami tayi magana Lukman (lucky boy) ya fito a fusace yana mai tsira mata hannu tare da fad'in, "Zan ci uwarki a gidan nan idan kika k'ara saka mun baki a cikin al'amura na. Ke uban wanene bai san cewa ke tantiriyar karuwa bace mai y'ay'a har biyu na shegu, dan ma d'ayan ya fad'i ta hannu hagu (Mutuwa) da yanzu y'ay'an ki uku duk shege. Wallahi kika k'ara saka min baki a cikin al'amura na, sai na maki mugun duka a cikin gidan nan. Y'ar iska taxi no garage!" Kallonsa Lami tayi a fusace tare da fad'in, "Kai! Kai Lukman!! Kayi min shuru a wajen nan. Kar in kuma jin bakin ka. Ba yarka bace ita? To ban so ka k'ara fad'in wannan maganar. Ka shiga d'aki ina zuwa akwai wasu kud'i da na ajiye maka." Juyawa Lucky boy yayi yana wani tafiya a b'ankare tare da fad'in, "Karfa ki dad'e kin san ban son jira." Lami kuma mai da dubanta tayi izuwa wajen Na'ima tare da fad'in, "Kin san dai ba hankali bane ya ishe sa, ki rik'a fita harkan sa." Turo baki Na'ima tayi tare da wucewa fuuuu tana fad'in, "Ai ke Lami sam baki son laifinsa, kullum sai dai ki rik'a d'iban kud'i kina bashi yana zuwa yana shaye-shaye dasu." Lami bata ce komai ba ta wuce d'aki domin bawa Lucky boy dubu biyar d'in da tayi masa alk'awari jiya. Sauran y'an matan ma duk suka shige d'aki. Sai da Sarah taji shuru a tsakar gidan sannan ta fito ta nufi pampo ta d'auro alwala saboda kwala kiran sallar isha'i da taji ana yi a masallacin dake gaban gidan su kad'an. Dawowa d'akin tayi ta taras da duka yayyinta a ciki ko wacce sai cab'a kwalliya take yi saboda lokacin fitar su yayi. Dama haka suke yi, wasu idan sun fitan ma, sai suyi kwana biyu, uku har sati basu dawo ba. Wata rana kuma a ranar suke dawo can cikin dare. Darduma Sarah ta shimfid'a ta tada sallar isha'i, don dama ita kad'ai ce a cikin su take yin sallar, to Lamin ma bayi take yi ba balle ta saka su a hanya. Sai bayan ta idar ta sallah ne ta saka doguwar riga irin mai kama jikin nan, sai ta d'aura k'atuwar suwaita a kai sabida sanyin da take ji. Tana cikin zuge zip d'in suwaitar aka kwad'a sallama a cikin gidan nasu tare da fad'in, "Wai ana sallama da Sarah inji Farouq." Ras gaban Sarah ya yanke ya fad'i, don gani take yi kamar tana fita suka hada idanu zai gane akwai ciki a jikinta. Da sauri ta lek'o tsakar gidan tare da fad'in, "Kace tana zuwa yanzu." Tana gama fad'in haka ta dawo d'akin domin d'aukar hijjab d'in da ta cire yanzu bayan ta idar da sallah. "Kanin ubanta yazo, jikinta sai rawa yake yi domin taje ta gaida shi." Fad'in Nuratu tana hararar ta. K'ala Sarah bata ce ba, sai ma hijjab d'inta da ta fara k'ok'arin sakawa. "Shegiya ko irin jan ajin nan baki iya ba. Daga ya turo jikin ki na rawa zaki fita." Fad'in Marfu'a. Sarah kuwa ko kallo basu ishe ta ba, ficewa ma tayi daga d'akin bayan ta gama sanya hijjab d'inta. A k'ofar gidan ta ganshi sanye da wando jeans da blue T-shirt, kansa sanye da facing cap ya jingina da wani k'arfe dake jikin gidan mak'otan su yana kallon d'aid'aikun mutanan da suke fitowa daga masallacin kasancewar ba'a jima sosai da idar da sallah ba. Juyowa yayi tare da zuba mata idanu har ta k'ariso inda yake tare da fad'in, "Sannu da zuwa. Ina wuni?" Kallonta yake yi for almost 2mins kamun ya bud'e baki yace, "Ina kika je d'azu na ganki kin ruwa ya maki duka?" Saurin d'agowa tayi ta zuba masa idanu, sai kuma ta sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa don gani tayi makar zai ga an rubuta _Ina d'auke da ciki_ a kan goshin ta. "Tambayar ki nake yi kin yi min shuru." Farouq ya sake magana a karo ba biyu. Sai a lokacin Sarah ta bud'e baki tare da fad'in, "Asibiti naje." Kallonta yayi tare da maimaita "Asibiti." K'ara d'agowa tayi ta kallesa a karo na biyu, sai kuma tayi saurin kau da kai tana kallon k'asa tare da wasa da zoben dake hannunta. "Are you sick Sarah?" Girgiza kai tayi tare da fad'in, "Dubiya naje yi. Lokacin da na fito kuma ban samu abun hawa ba saboda hadari. Shine ruwan ya duke ni, amma kuma ba fake. Da ruwan yayi sauk'i ne shine na fito shiyasa ka ganni a jik'e." Ajiyar zuciya Farouq ya sauke tare da fad'in, "Amma baki san hakan da kika yi zai iya jawo maki rashin lafiya ba. Mai yasa ma baki kira ni nazo na d'auko ki na dawo dake gida ba? And ina ta kiran wayar ki bakya d'aga wayar." Ya fad'i hakan yana mai folding hannunsa. Ko kamun Sarah tace wani abu an banko k'ofar gidan su, cikin sauri duka su biyun suka juya suka kalli k'ofar gidan. D'an duk'awa Farouq yayi tare da fad'in, "Mama ina wuni?" Harara Lami ta watsa masa tare da fad'in, "Uwar ka ba, ka baro ta can gida. Ni ba mamarka bace. Kaga wacce ta haifa nan." Ta k'arisa maganar tana mai nuna Sarah da hannu sannan ta cigaba da fad'in, "Ba gaisuwa ka na taho nan in amsa ba, zuwa nayi ka fad'a min shin kai ne uban cikin dake jikin Saratu ko kuwa. Don idan kai ne, wallahi na rantse list d'in ka daban ne. Kuma kar kayi tunanin zan yi maka ragi." Hannu Sarah ta d'aura a kai tare da fad'in..................
Chapter 4 · 0% Book details