← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 112

Sashe 44

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 4 min read

aiki. "Dole in tafi matakin k'arshe na hana auran nan." Tana fad'in haka ta fiddo wayarta tare da danna wata number tayi magana tsayin mintuna goma sannan ta yanke wayar tana murmushi. Tun daga wannan ranar Aina'u bata k'ara nuna komai ba. Daga k'arshe ma shiga cikinsu Sarah tayi ana ta hidima da ita. Sarah ba k'aramin wani irin tsananin kyau ta k'ara ba. Sosai dilkan da ake mata ya amshi jikinta. Sai wani glowing take yi kamar wata kulb'a. Ana gobe d'aurin aure, mai gyaran jiki tayi mata lalli ja da b'aki wanda ya kuma fito da kyawunta kasancewarta farar mace. Ba k'aramin kyau lallin nan yayi ba. A ranar kuma _Khalil_ ya kasa jurewa ya dunga rok'on Muneeba akan ta taimaka masa ta fito masa da Sarah da dabara ya ganta ko na mintuna biyar ne. Muneeba tace masa kar ya damu bayan Isha zata fito masa da ita. Don tun saura kwana biyar biki Sarah ta koma gidansu Muneeba da zama gaba d'aya. Kamar yanda suka yi alk'awari kuwa, ana idar da isha'i _Khalil_ yayi parking ta bayan gidansu ga kira Munee a waya. Sarah bata san shirinsu ba, kama hannunta kawai Munee tayi tare da ce mata tazo ta nuna mata wani abu. Har gaban motar _Khalil_ ta kaita ta, a jingine ta same sa jikin motar yaci kwalliya cikin wasu k'ananan kayan da suka yi masa matuk'ar kyau. Da kallo kawai yake ta bin Sarah da idanu ganin wani mahaukacin kyau da ta k'ara yi masa. Sai yaga kamar canzo masa ita aka yi. "To gata nan, dan Allah kar ku dad'e kaga mama ta fahimci bama cikin gidan." Sai a sannan _Khalil_ ya kalli Muneeba tare da fad'in, "Godiya nake k'awarmu. In Sha Allah baza mu jima ba." Wucewa tayi ta bar su tsaye suna kallon juna. "Nayi kewarki" a tare suka fad'i. "Ba wani nan kin ba kiyi kewa ta ba tun da baki tab'a cewa mu had'u ko a sace ba." Fad'in _Khalil_. "To ai ni tsoro nake ji kar mama ta gane." Sarah ta fad'i a shagwab'e. Shima shagwab'ewar yayi kamar yanda tayi tare da maimaita tace. Rufe fuska tayi da hijjab d'inta tare da fad'in, "Ni dai bana so." Nan ma ya kuma kwaikwayonta. K'afa ta bubbuga a k'afa tare da fad'in, "Ni dai ka bari." dariya yayi tare da fad'in, "To naji, mu shiga mota naga kamar tsayuwar yana damunki." Da sauri tace, "A'a ni dai na sai na shiga ba. Ai ka ganni, zan wuce kada mama ta gane bana nan." Waro idanu yayi tare da fad'in, "To ai ko mintuna biyar d'in basu cika ba. A hakan d'in ne kike cewa kin yi kewata?" Ko kamun Sarah tayi magana wayarta ta soma k'ara, ganin Muneeba ce duk sai ta rud'e ta shiga fad'in, "Munee ce ke kira na, shikenan na shiga uku watak'ila Mama ta gane bana gidan. Dan Allah zan wuce gida." ta k'arisa maganar tare da marairaicewa. Bud'e mota yayi tare da fiddo leda ya ya kama hannunta tare da fad'in, "Ungo wannan inji Hajiya. Amma dan Allah ki tsaya in miki hoto guda d'aya kawai." ya fad'i tare da fiddo wayarsa yayi mata hoto a jikin motar. Kallonta yayi tare da fad'in, "Haba mana, smile." Yanda ya fad'i smile d'in ne ya bada dariya. Sai hoton yayi kyau sosai don hatta dimples d'inta sai da suka lob'a duka. "Kayi wa Hajiya godiya, bye sai da safe." Ta fad'i hakan tare da saurin juyawa ta soma tafiya. _Khalil_ bai bud'e motarsa ya shiga ba sai da yaga tasha kwana. Taku uku tayi taji an jawota da k'arfi an toshe bakinta tare da shak'a mata wani abu a cikin tsumma. Take ta sune jikinta gaba d'aya ya saki. Cikin sauri maza ukun suka tura ta cikin wani k'atoton buhu suka d'aura akan wheelbarrow tare da turawa har zuwa wajen wata mota golf sannan suka bud'e booth suka jefa ta ciki Sannan suka rufe tare da shiga suka bar wajen..........
Chapter 44 · 0% Book details