← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 112

Sashe 55

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 6 min read

ya daki hancinsa, don humran da Hajiya ta bata jiya da kuma _Imperial Majesty_ da oud ta shafa, sai suka haɗu suka bada haɗaɗɗan ƙamshi mai sanya natsuwa a zuciyar wanda ya shaƙi ƙamshin. " _Naaji na gani zan baki lokacina, tunda kinka nuna ƙauna dare da rana, baki nuna so, domin arziki na, kikan tsare mutunci ko bakya gaba na. Ke nake gani, ke nake gani. Ke nake gani, to bani kula kowa_." Yana tafiya ne yana waƙar har ya isa inda take ya kamo hannunta ya bata kiss a goshi. Laure kuwa sake baki tayi tana kallon su. Ganin _Khalil_ ya manta da ita a wajen sai ta soma waƙa ita ma tana faɗin, " _Ga abinci ku, ga abincinku, kuzo ku karɓa, a baani turare in wuce_." Da sauri _Khalil_ ya tare gaban Sarah yana faɗin ku kuke ganinmu ba mu muke ganin ku ba. Anya Laure babu aljanu jikinki kuwa. Wannan irin murya haka kamar na samudawan farko. To tuf-tuf-tuf. Kurwar matata kur. Maye ko aljani yaci kanshi. Ga ƙatuwar murya ga uban kacakoran haƙora." Shigowa sosai Laure tayi tare da dire basket ɗin sannan tace, "Wallahi tallahi halittar ubangiji. Kuma dai nafi matar kyau." Juyowa yayi gaba ɗaya ya kalleta daga sama har ƙasa tare da faɗin, "Eh Lallai babu shakka." Sai kuma ya bushe da dariya tare da faɗin, "Ga shawara idan zaki ɗauka, kije kuyi shawara ke da mai gadi ya samo ƙatuwar keji ya ajiye a ƙofar gate, bayan kin gama aikinki na cikin gida sai ki fita waje ki shiga kejin nan, wallahi ba ƙaramin kuɗi zaki samu ba, don duk wanda ya zo wucewa sai ya ajiye maku kuɗi." Kuka ta fashe dashi tare da faɗin, "Sai kace wata biranya zan shiga keji. Kuma turaren ma ba'a so." Tana gama faɗin haka ta juya Sarah tayi saurin kai hannu zata riƙota _Khalil_ ya riƙe hannun tare da faɗin, "Tsaya ki sha kallo." Sai da ta kai bakin ƙofa sannan ta juyo tare da faɗin, "Baza ka bani haƙuri ba? Ke kuma amarya ko ɗan irin cin-cin ɗin nan ma baza ki bani ba. To wallahi ban fita ko ina sai an bani turarena da cin-cin." Kallon juna _Khalil_ da Sarah suka yi suka fashe da dariya. _Khalil_ yace, "Ahaf, ba na faɗa maki ba. Ai mayya ce! Idan ban bata turaren ba sai ta lashe kurwata!" Murguɗa baki tayi tare da faɗin, "Eh naji ɗin komai zaka ce kace idan har za'a ban turaren." Kiss yayi ma Sarah a kumatu tare da faɗin, "Ina zuwa love, bari na ɗauko mata ta wuce ta bamu waje." Gyaɗa kai kawai Sarah tayi. Yana wucewa Laure ta matso kusa da Sarah tare da faɗin, "Wallahi ke kyakkyawa ce. Kin ganki kuwa? Wane kajuli (Kajol) ta ƙasar hindiya. Gaskiya ya _Khalil_ ya iya zaɓe yasin. Ku wani yare ne?" Murmushi Sarah tayi tare da faɗin, "Babana ɗan Nasarawa ne a wani ƙauye da ake kira _Wamba_" Riƙe haɓa Laure tayi da faɗin, " _Wamba_? Ni ban ma taɓa jin sunan garin ba. To mamanki fa?" Ko kamun ta bata amsa suka ji saukowar _Khalil_ hannunsa riƙe da kwalin turare guda biyu. Washe baki Laure tayi tare da faɗin, Alhamdulillahi ni Laure! Nagode ya Ibrahim" ta faɗi tun kan ya miƙa mata turaren. Taɓe baki _Khalil_ yayi tare da miƙa mata yace, "Sai a sakar min mara inyi fitsari." Amsa tayi bakin yaƙi rufo, haƙoran sunyi cirko-cirko a waje. "To, to a wuce a bani waje." Sai da ta kai ƙofa sannan tace, "Aunty Saro, sai nazo dan ya _Khalif_ ya fita." Da ƙarfi Khalil yace, "Kika ƙara kiran matata da wannan sunan sai na cire shegun haƙoran nan. Kuma kar in sake inga ƙafafunki a ɗakina." Dariya Sarah tayi tare da faɗin, "Amma ya kuke da ita?" Sai da ya kulle ƙofar ya saka key sannan ya dawo inda take ya rungume ta sannan ya ce, "ƴar uwa ce, lokacin da Hajiya taje Maiduguri aka haɗo ta da ita domin ta riƙa taimaka mata da wasu ayyukan. Ance dai abokiyar wasan mu ce, ban dai san asalin yanda muke da ita ba." Sarah tace, "Hajiya ƴar Maiduguri ce ko?" Zama yayi a kan kujera ya ɗaurata a kan cinyarsa tare da faɗin, "Mahaifinta Shuwa ne, mahaifiyarta kuma Kanuri, kuma duka tana jin yaren." Kallonsa tayi tare da faɗin, "Kai fa, kana jin yaren?" "Gwada yara min naji ko zan iya mayar maki?" Faɗin _Khalil_. "To ai ni ban iya ba." Sarah ta faɗi. Kwanto da kanta yayi a kan ƙirjinsa tare da faɗin, "Kar ki damu, wata rana zaki san ko inaji ko ban ji." "To baba fa, wani yare ne?" Sai da ya nuna kansa Sannan yace, "Babana?" "Eh babanmu." Ta bashi amsa tana nuna ita dashi. "Sorry babanmu har dake. Shi kuma Mahaifiyarsa bafulatana, mahaifinsa Kanuri." "Kai Kanuri ne kenan?" Faɗin Sarah. "Kwarai da gaske!" Ya bata amsa tare da miƙar da ita zuwa dinning sannan ya ɗauko basket ɗin da Laure ta kawo abinci ya ajiye a kan dinning ɗin sannan ya koma kitchen ya ɗauko kwan da ya soya. "Ni na soya wannan da kaina. Ci kiji?" Faɗin Khalil cike da farin ciki don ya soya kwai. Sarah kuwa tun kallon farko da tayi wa kwan taga tsakiya ya babbake. Hannu ta kai ta ɗan yago gefe inda bai ƙone ba ta saka a baki. Da sauri ta furzo shi jin magi har kwakwalwar kanta. "Ya dai?" Faɗin Khalil bayan yayi saurin zuwa inda take. Bata ce komai ba ta yanko ta saka masa a baki. Dakyar ya iya juriya ya haɗiye yana yamutsa fuska. "Wai wai wai! Daɗi!" Faɗin Khalil yana yin haka👌da hannu. "To maza cinye shi!" Ta faɗi tana masa tuni da plate ɗin da idanunta. "Kiyi haƙuri na kaiwa Madhu itama taci. Don duk abunda na saka a baki itama sai ta ci." "Wacece kuma haka?" Tayi saurin faɗa. Shi kuma yace, "Madhubala wutar kyau, masoyiyata kenan?" Tuni annurin fuskanta ya canza ta tsaya kawai tana kallonsa. Kumatunta yaja tare da faɗin, "Kishi, to mage na ce wacce na ɗauko all the way from Paris. Zaki sota sosai idan kin ganta. Very beautiful." Sai a lokacin ta saki fuska tare da faɗin, "Laa! Kaman ka san ina son mage sosai. Tana ina?" "Tana side ɗin Hajiya. Idan mun gama karyawa zan kai ki, ki gaida Hajiya sai mu ɗauko abun mu daga nan." Ya faɗi hakane tare da soma serving ɗinsu a plate ɗaya. Yana bata a baki tana bashi har suka kammala sannan suka kwashe kayan tare suka kai kitchen yana wanke-wanke tana ɗauraya har suka kammala. Towel ya ɗauko ya goge mata hannu dashi sannan suka fito parlour. "Bari na ɗauka maki babban mayafi sai muje wajen Hajiya." Ya faɗi hakan tare da nufar sama. Mintuna kaɗan ya dawo ɗauke da gyale. Da kanshi ya soma nannaɗa mata gyalen a kai dai-dai lokacin da suka ji door bell. A tare suka kalli ƙofar, sai da ya gama saka mata sannan ya nufi ƙofar ya buɗe. Ido huɗu suka yi da Aina'u tana sakar masa murmushi.
Chapter 55 · 0% Book details