← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 112

Sashe 96

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 4 min read

na tsutsa da irin kulawar da Khalil ɗin ya bata har zuwan Aina'u gidan, haihuwarta, ciwon Baba (duk da bata faɗa masu sanadi ba don itama bata sani ba) da kuma iskanci da mulkin da Aina'u ta zuba har izuwa sanadin barowarta kaduna duk sai da ta zayyane masu tana kukan fitar hayyaci. Ba ita kaɗai ba, gaba ɗaya ɗakin yara da manya kuka suke yi, "Haka Nuhu yaga rayuwa? Yanzu ƴaƴan Nuhu ne suka yi karuwanci har da ƴaƴan shegu! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!!" Faɗin Nnanne tana mai dafe saitin zuciyarta, ɗaya hannunta kuma yana riƙe da hannun Sarah dake kuka. Gaba ɗaya ɗakin babu wanda bai ji mugun tausayi Sarah ba jin halin bala'in data shiga sanadin ƙanwarta ciki ɗaya! "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Nnanne!!" Ba Lukman ya faɗi da ƙarfi ganin Nnanne zata dungura don suma tayi. Nan da nan suka kwashe ta zuwa asibiti. Sai da Hajiya tayi sati tana jinya kamun aka sallame don jininta ne ya hau sosai, Sarah kuwa taga ƙaryar wani abu wai shi dangi, don kuwa irin jama'ar dake tururuwar zuwa ganinta sunfi ƙarfin a ƙirga, wannnan ya jata riiii zuwa gidansa, sai wancen ma yaja. Ɓangaren Hajiya kuwa, tun bayan tafiyar Sarah da kwana biyu wanda bata ma san bata gidan ba ta tashi tsaye sosai akan roƙon Allah, waya ta buga Maiduguri tare da faɗin buƙatunta wajen wani babban malamin musulunci tace a haɗa almajirai suyi mata sauka zata turo da abun sadaka ta waya, sannan ta kira malamin da yake masu saukar Qur'ani tun lokacin da Alai yake da rai, ta faɗa masa buƙatunta, kasancewar girma yà kama shi sosai, sai ya saka ƴaƴansa da almajirasa suka cika gidan Hajiya da karatu, ranar ba'a gidan Aina'u da Khalil suka kwana ba, ihu ta riƙa masa a kan su bar gidan, sai da aka haɗa kwanki goma ana sauka a gidan tare da buɗe gidan da hayaƙin shaiɗanu. A rana ta goma sha huɗu, Aina'u ta taso Khalil suka dawo gidan, kai tsaye ɗakin Hajiya ta nufa tana kwala kiran, "Bilkisu! Bilkisu!! Ki fito nan tsohuwar munafuka annaminiya" tana tafiya hannunta riƙe dana Khalil har parlourn Hajiya, da sauri Hajiya ta fito tana ƙarewa Aina'u dake riƙe da hannun Khalil kallo, "Menene haka nake gani Khalilullah!" Hajiya ta nuna hannun Aina'u dake riƙe dana Khalil fuskanta ɗauke da mamaki, " _ƙanwar matarka_ ce fa Ibrahim!" Wani wawan harara Aina'u ta jefi Hajiya dashi tare da yin wani irin dariyar ƴan iska sannan wani janyo Khalil ɗin tare da riƙo kansa ta haɗe bakinsu waje ɗaya. Da sauri Hajiya ta rintse idanunta gabanta na wani irin bugawa tana istigfari cikin zuciya. "Wallahi kika ƙara yin magana akan alaƙata da ɗanki, yanzu gabanki zan sutale masa wando kuma kina kallo zai yi amfani dani, wata ƙila na har rabo ya shiga tsakani!" Wasu irin zafafan hawayene suka shiga kwaranyo daga idanun Hajiya har tsikar jikinta na tashi, "Na taso maki da sha'awar shekaru ko? Kar ki damu idan ƙaiƙayi yake maki, inada mutane dai-dai dake da zasu iya biya maki buƙata." Wani irin kuka Hajiya ta fashe dashi mai ƙarfi kuma har wannan lokacin idanunta a rufe suke, "Ibrahim a gabanka, a gabanka _Ƙanwar matarka_ take faɗa min irin wannan maganar amma ka kasa ko tari mai ƙarfi, a gabanka Mu'azzam!!" Hajiya ta faɗi tana kuka. Khalil kuwa tunda ya sunkuyar da kanshi a ƙasa hawaye masu uban gudu suke sauka a akan tiles, ya kasa ko ɗagowa, jikinsa ne kawai ke karkarwa. "Ba kukanki nazo inji a nan ba, zuwa nayi inyi maki kashedi akan kar ki kuskura ki kuma kiran wasu ƴan iska gidan nan suzo suna yin tsaface-tsaface, kinji ko baki ji ba?" Wani irin haske ne ya gilma a fuskan Aina'u har sai da taji shock, Hajiya ta nuna mata ƙofar fita tare da faɗin, "Wa ya haifi ubanki da har zaki shigo cikin gidan ChiefJustice Nurudden kice zaki bawa matarsa order, fita kamun na saka a ƙarar da zuri'ar ku!" Hajiya ta faɗi a tsawace. Baya Hajiya tayi zata faɗi saboda wani gigitacen mari da Aina'u ta ɗauketa dashi tare da faɗin, "Kul! Kika ƙara ɗaga hannunki a jikina. In kwanta da ɗan naki in bashi natsuwa har sai da ya manta sunanki, shine zaki saka min da mari, ƙarya kike yi wallahi!" Hannu dafe da kunci Hajiya ta kalli Khalil da ya tarota tare da zaunar da ita a kan kujera, "Khalil har lalacewaka ta kai haka? A gaban idanunka _Ƙanwar matarka_ ta ɗaga hannu ta mare Ni." Jikin Khalil wani irin rawa yake yi har naman jikinsa na ɗagawa haƙorinsa na haɗuwa dana juna a lokacin guda gashin dake kwance a jikinsa suna wani irin mimmiƙewa, idanunsa kuwa sun koma wani irin abun tsoro saboda yanda suka kaɗa sukai jazur............
Chapter 96 · 0% Book details