Sashe 71
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mine, Nafeesa ta samu ƙaruwa ɗazu." Ya faɗi maganar yana mai jan skirt ɗinta sama ya zage zip ɗin. Out of excitement tace, "Dan Allah! Alhamdulillah Allah ya raya, don Allah ka ɗauko min picture ɗin babyn in ganta." Kallon fuskanta Khalil yayi, babu abunda yafi kyau da fuskanta irin fara'arta, sai yaji kamar kar ya faɗa mata babyn ta koma. "Ya naga kayi shuru Happiness?" Faɗin Sarah. Ajiyar zuciya Khalil ya sauke tare da kau da kansa daga kallonta yace, "Allah ya amshi abunsa, babyn ta koma." Zaro idanu Sarah tayi tare da faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ina Nafeesan yanzu? Wani hali take ciki?" Sarah ta faɗi hawaye na zubar mata. Hannunta biyu ya kama tare da faɗin, "Ta ɗauki dangana, ta san cewar Allah da ya amshi rayuwarta ya fita son yarinyar, ta amshi ƙaddararta ta hanyar dangana da fauwalawa Allah komai." A hankali Sarah tace, "Allah ya ƙara mata haƙuri da dangana." Miƙewa yayi tare da faɗin, "Haka ake son duk musulmi da ɗaukar ƙaddara mai kyau da mara kyau idan har ya yarda shi ɗin cikakken musulmi ne, shiyasa nake so kema ki fauwalawa Allah komai ki daina koke-koken nan, in Sha Allah zaki samu lafiya. Bari naje zana'idar in dawo sai mu tafi asibitin, kina buƙatar wani abu?" Girgiza kai Sarah tayi tare da faɗin, "Babu abunda nake buƙata, kayi tafiyarka, Allah yasa mai ceto ce. Nima zan gwada miƙewa inje can wajen Hajiya yanzu tunda ka saka min pampers tsutsotsin baza su zubo ma." Kallonta yayi tare da faɗin, "Idan har kin ga baza ki iya ba, kiyi zamanki gaba ɗaya sun san baki da lafiya. Ki kular min da kanki, sai na dawo." Yana gama faɗin haka ya fita ya bar ɗakin. Hannu Sarah ta ɗaga tare da faɗin, "Ya Ubangiji ga mijina nan, ka kare min shi daga dukkanin cutuwa, ka ƙara masa so da ƙaunata a cikin zuciyarsa, ni kuma bani lafiya mai amfani ta yanda zan bauta masa wajen yi masa biyayya har in dawo gareka. Allah ka bani lafiya alfarmar annabi sallallahu alaihi Wasallam." Ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka. Can cikin gida kuwa, har mijin Nafeesa da danginsa sun ƙariso, mahaifiyarsa ita tayiwa babyn wanka tare da yi mata sutura, shi kuma Qasim mijin Nafeesa sai lallashinta yake yi yana bata haƙuri akan in Sha Allah zasu samu wani nan kusa. Kamun magrib har sun kai gawan makwancinta sun rufe sun dawo, sai gidan yayi wani irin tsit kowa da irin jimamin da yake yi, yayin da Laure ke wani irin zabura da firgita idan ta kasance ita kaɗai a waje, don babu fuskan da take gani sai na Aina'u da _Hell Ofulafu_ suna tsoratata gashi kuma babu bakin magana. Sarah ta iya fita har side ɗin Hajiya, kallon ɗaya Hajiya tayi mata gabanta ya faɗi ganin wani mahaukacin rama da tayi, don ko ɗazu da safe sun haɗu kamun faruwar komai, "Wannan wani irin cuta ce kamar ta iska?" Hajiya ta faɗi a zuciyarta. Sarah kuwa da bata san halin da Hajiyar ta shiga ba, waro idanu tayi ganin halittarta gaba ɗaya ya canza, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Hajiya haka kika koma?" Aunty Maryam ce tayi saurin tarota ganin zata zube a ƙasa, ta zaunar da ita. Rarrafawa tayi ta ƙarisa wajen Hajiya tare da ɗaura kanta akan ƙafafun Hajiya ta hau rera kuka, hajiya bata iya cewa komai ba sai shafa bayanta da ta shiga yi tana danne nata hawayen. "Oh Allah! Abu kamar jifa, daga wanda halittarsa ta canza, sai kuma wacce maganarta ya ɗauke gaba ɗaya, da kuma mai aman tsutsotsi! Gaskiya wannan abun dubawa ne. Duk mai bin mu da sharri in Sha Allah sai ya koma masa." Faɗin Nafeesa wacce taci kuka ta ƙoshi, idanun nan sun yi jazur." Wani wawan kallon gefen idanu Aina'u tayiwa Nafeesan a zuciyarta tana faɗin, "Ashe kema zaki bi ƴarki kenan!" Sarah kuwa ɗagowa tayi ta kalli Nafeesa tare da faɗin, "Nafeesa wacece kuma maganarta ya ɗauke?" "Laure!" Nafeesa ta bata amsa hawaye na zubowa. Hajiya ta kalli ɗaya daga cikin yaran dake ɗakin tace, "Namrah kunna rediyon can ki kunna mana karatu zuciyar kowa tayi sanyi." Da jin haka wuff Aina'u ta miƙe ta fita daga ɗakin ta baya gudun a ganta, don yi nayi kamar zata shiga toilet ɗin dake parlourn, Aunty Maryam kuwa tunda ta miƙe take lure da ita, don haka nan taji tana mugun zargin Aina'un, sam tun ranar farko data fara ganinta bata kwanta mata a rai ba. Da sauri ta zaga ta baya ta tsaya bayan flowers, sai da ta kalli gefe da gefe sannan ta fiddo hannunta tare danna tsakiyar tafin hannun, cikin second biyar sai ga _Hell Ofulafu_ ya bayyana cikin suffarsa ta tsoro, gefensa kuma wani gajeren halitta abun tsoro ne mummunan gaske, shi ya daka mata tsawa tare da faɗin, "Menene buƙatarki ta gaba?" "Nafeesa! Ita nake so tabi jaririyar, ba bada jininta matsayin ruwan da Hell zai ɗanɗana, sannan ina so a saka mummunar warin da yafi wanda Sarah keyi a jikin mijinta ta yanda zata riƙa kyamatarsa har hakan ya fusata shi yayi mata wulaƙanci, don na san tabbas idan aka yi haka Khalil zai ji haushinta tunda shi ya jure bai kyamaceta ba duk da tsutsotsin dake fita a jikinta da kuma warin da take yi. Sannan na uku, ina so a ɓatar da kokwanto da shakkun da ke zuciyoyin mata da mijin gidan nan a kai na, ina nufin SS Abdul-Hakeem da matarsa Maryam, sannan Barrister Muhammad Kabir da LTG Abdullah ka mantar dasu suna da family ka Kaduna, ina so su manta da kowa nasu dake Kaduna, ko da wasa kar su waiwayi gida! Abdul-Hakeem ma ayi masa abunda zai jawo a koresa daga aiki, don na tsani ƴan sanda musamman na farin kaya!" Wannan mummunar halittar ya fashe da dariya tare da faɗin, "Aikin ya kammala, sai dai jinin ƙanwar Mijin yayarki yayi kaɗan, dole sai kin ƙara da jinin yaro ƙaramin kuma namiji." Shuru Aina'u tayi tana tunanin ta inda zat dea samu jinin yaro ƙaramin, "Rabo ɗan wajen Na'ima!" Faɗin Aina'u a bayyane tana mai sakin murmushi tare da ƙara faɗin, "Na rage maki wahala Na'ima, a sauka lafiya Rabo!" Ɓat _Hell Ofulafu_ da wannan halittar suka ɓace daga tafin hannunta don sun gama sauraran abunda zasu saurara, tun ambaton sunan Rabo da tayi na farko, har _Hell Ofulafu_ ya janyo kurwarsa tare da haɗiyewa. Aina'u na juyawa suka yi idanu huɗu da Aunty Maryam da ta biyo ta a baya, har fitsarin tsoro ya gama wanke jikinta, gaba ɗaya jikinta sai kakkarwa yake yi. Aina'u kuwa wani murmushi ta saki ba tare da ko ɗar ba don Aunty Maryam ɗin taji komai da take tattaunawa da _Hell Ofulafu_. Zagaye Aina'u ta shiga yi tare da faɗin, "Makanta, kurmanta, rashin yin magana, mutuwa ɓarin jiki, mutuwar gangar jiki gaba ɗaya, ƙona ki da ranki, wanne kika zaɓa?" Kuka Aunty Maryam ta soma yi tare da faɗin, "Dan girman Allah Aina'u kiyi haƙuri kar kiyi min ko ɗaya daga cikin abunda kika lissafo, na zaɓi da nayi shuru da baki na, babu wanda zai ji wannan maganar nan daga ni sai ke!" Wani dariya Aina'u ta kwashe dashi tare da faɗin, "Kin ga nayi maki kama da wawuya? Ko da yake, ni nayi maki zaɓi, shine barin gidan nan, kuma kin san wani abu, duk lokacin da bakinki yayi kuskuren buɗewa ya faɗawa wani wannan abun da kika ji, baza ki iya faɗin komai ba, kuma daga ranar baza ki kuma magana ko kiji ba har ki mutu! Wuce kije ki fara haɗa kayanki kamun takardar sakinki ya biyo ki!!" Ta ƙarisa maganar a tsawace tana mai nuna mata hanya. Da sauri Aunty Maryam ta riƙo ƙafafuwanta tare da faɗin, "Na roƙeƙi da girman Allah kar ki raba ni da aurena, wallahi nayi maki alƙawarin babu mai jin wannan maganar har sai idan Allah ne yayi ikonsa, ina son mijina da aurena don Allah kar ki raba ni dasu." Wani mugun tsaki ta ja tare da faɗin, "Sai ki zaɓa, rayuwarki, lafiyar jikinki, ko kuma aurenki?" Shuru Aunty Maryam tayi tana wani irin kukan baƙin ciki. Aina'u ta taɓe baki tare da faɗin, "Gidan na kowa sai yaji a jikinsa, na rantse da Yesu Almasihu mai ceto!" Da saurin Aunty Maryam ta kalleta jin abunda ta furta tare da faɗin, "Babu shakka, ashe shiyasa babu ɗigon imani a zuciyarki, in Sha Allah sai kin girbe abunda kika shuka azzaluma kafurar banza!" A cikin zuciyarta. "Ki wuce kije ki soma haɗa kaya, don yau gidan mai dattin hula da ɗan kwali za'a kwana!" Tana gama faɗin haka ta wuce ta bar wajen tana waƙar zumunta. Aunty Maryam kuwa kuka ta dunga rusawa tana tunanin makomarta, ita da babu uwa, babu uba, rayuwa take yi a wahale a wajen dangin ubanta kamun Allah ya kawo mata Abdul-Hakeem har suka yi aure, idan ka ganta gidansu gaisuwa taje ko kai masu abun arziki don suna ba wasu masu arzikin bane, talla tayi su kala-kala irin su kunun gyaɗa da alale, da daddare kuma burabusko da miyan taushe, kuka da kuɓewa! Har zunɗenta ake yi wai don ta auri ɗan masu kuɗi sai fankama take yi tana ƙoƙarin manta asalinta. "Shinekan wahalata ta dawo sabuwa fil, masu fatan irin haka ta faru dani sun samu dama. Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allahumma arji'ini fi musibati wa aklifni khairan minha!!" Haka aunty Maryam tayi ta nanatawa har ta isa ɓangarenta. Cak ta tsaya a parlour tana kallon tanƙameman hotunsu su uku, ita da Abdul-Hakeem da kuma ƴarsu Maimoon. Can gidansu Lami kuwa, Rabo na zaune kusa da ita da roban abinci a hannunsa yana ci, gaba ɗaya suna tsakar gida suna shan iska kasancewar garin akwai zafi, kawai sai suka ga Rabo ya fara wani irin jijjiga idanunsa na sama, hatta robar abincin dake hannunsa jijjiga yake yi, kumfa baƙiƙƙirin ya soma kwaranyowa daga bakinsa, gaba ɗaya da gudu sukai kansa suna kiran sunansa, Lami kuwa wani tsalle ta buga tare da fasa ƙara ta shiga faɗin, "Yesu! Yesu!! Yesu gamu gareka mun bar zunubi, duk wani dodo ko maye ko mugun dake son tafiya da granson ɗina