Sashe 90
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda Laure ta ɗago fuskanta, jaga-jaga yayi da hawaye saboda kukan da tayi, zama Sarah tayi akan kujera hannunta riƙe dana twins tana ta kallonta har ta idar da sallar. Bayan ta shafa addu'a sai tayiwa Sarah murmushi tana mai miƙawa twins hannu, gaba ɗaya sai suka tafi wajenta, Sarah miƙewa tayi ta nufi ɗakin Hajiya, sai da ta Kwankwasa sannan ta murɗa ta shiga, zaune ta samu Hajiya ta zabga uban tagumi, duk da irin ramar da Sarah tayi, ba ƙaramin tsoro da tausayi Hajiya ta bata ba saboda yanda ta koma ta yanƙwane, "Hajiya ina wuni?" A ɗan tsorace Hajiya ta ɗago tana kallon Sarah don bata ji shigowarta ba. "Lafiya ƙalau Sarah, zauna mana, ina ƴan biyu kyautar Allah?" "Suna parlour wajen Laure." Sarah ta bata amsa hawaye na ciccikowa daga idanunta. Wani ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tare da kallon Sarah tace, "Sarah ban san mai ke faruwa a cikin gidan nan ba, komai ya tsaya cak, babu walwala da farin ciki, zukatu cunkushe suke da baƙin ciki, hasken dake gidan nan gaba ɗaya ya dusashe, ƴaƴana sun manta dani, Marmari bai taɓa yini bai kirani a waya ba, Muhammad Kabir shima bai taɓa kwana ba tare da yaji muryata ba, amma yanzu tsayin shekara ɗaya har da watanni biyar rabon da naji muryansu, ko balle kuma su tako suzo inda nake, na rasa wannan wani irin al'amari ne wannan, uwata!" Hajiya ta ƙarisa maganar hawaye na zubo mata. Gaba ɗaya sai jikin Sarah yayi mugun sanyi ganin tsohuwa na hawaye. Hannunta Sarah ta dafa tare da faɗin, "Hajiya kiyi haƙuri, amma ni a tunanina ba hakannan ba su ya Abdallah zasu ƙaurace maki har na tsawon shekara ɗaya da watanni! Hajiya addu'a da roƙon Allah har da sadaka zaki fara daga yau akan Allah ya karkato maki da dukkan hankalinsu a kanki, in Sha idan muka miƙawa Allah lamuranmu da kyakkyawar yaƙini, in Sha Allah zai yaye mana damuwarmu, Hajiya gaba ɗaya mun mance da Allah shiyasa shima ya mance damu, kuma na tabbata idan muka koma garesa zai amshi buƙatunmu da hannu bibbiyu. Hajiya ban san cewar duk tsawon shekarun nan aikin banza nake yi ba wajen raya darena da kuka ba sai yau da na shigo ɓangaren nan na tarar da Laure na ganawa da ubangijinta tare da ƙasƙantar da kanta tana kuka. Hajiya muyi koyi da Laure in Sha Allah duk matsalolinmu zasu gushe!" Shuru Hajiya tayi tana sauraren Sarah cike da jin kunya da kuma dana sani akan rashin kai kukanta tuntuni zuwa ga mahalicci, sai hakan ya tuno mata da marigayi (Nuruddeen Muhammad) mahaifinsu Khalil, da wani abu ya shige masa duhu ko kuma yana fuskantar matsaloli, nan da nan yake ƙara nau'ikan ibadu akan wanda yake yi, dama kuma azumin litinin da Alhamis ya zame masa jiki da kuma sallar dare, sai ya ƙara ninkawa, almajirai yake tarawa fiye da ɗari kuma ya shiga cikinsu su sauke ƙur'ani sau goma a cikin sati guda, sannan ya shiga sadaka a masallatai tare da gidajen maru, maƙowa kuwa kyautatawarsu daban take, hakan ne ya saka duk tuggun da ƴan uwansa suke binsa dashi yake koma masu. Kuma ƙa'ida ne lokaci da yake raye, tun su Khalil na ƙanana sai ya haɗa kansu har matan sun sauke ƙur'ani duk bayan kwana goma, bayan rasuwarsa da kuma yanayin aikinsu gami da mai da hankali kan tsantsan boko ya saka suka watsar da komi, kuma Lokacin da yake da rai, kullum gidan cikin sauraren karatun Alƙur'ani ake. Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tare da kallon Sarah tace, "Tabbas Saratu duk abunda kika faɗi hakane. Wato lokacin da mahaifinsu Khalil yake da rai, wallahi kullum cikin gidan nan karatun Alƙur'ani ake saurare, sannan duk bayan wani lokaci, Alai sai ya tara almajirai anyi saukar ƙur'ani da sadaka, bayan rasuwarsa ne komai ya watse!" "Hajiya a shawarce, ya kamata komai da ake yi cikin gidan nan ya dawo har abada." Faɗin Sarah. "In Sha Allah, uwata. Nagode maki sosai da tunatarwarki uwata, Allah yayi maki albarka." Faɗin Hajiya. Sarah ta amsa da ameen tare da miƙewa ta fita daga ɗakin, a parlour, su twins na ganin mahaifiyarsu sai suka bar jikin Laure da sauri tare da ƙarisowa wajenta, Sarah tayi-tayi su koma a atafau suka ƙi, haka nan ta koma side ɗinta dasu, babu kowa a parlour sai tayi saurin shigewa ɗaki don kallo kujeran dake parlourn zai iya saka ta faɗi ta mutu, don gaba ɗaya hoton Khalil da Sarah take gani tsirara a kan kujerar. Aina'u kuwa duk abubuwan da Sarah ta tattauna da Hajiya tana kallon komai daga ɗaki, wani ƙuƙulun takaici ne ya tokare mata waya ganin Sarah tun ba'a je ko ina ba tana son lalata mata shirinta. Tashi tayi ta kullo ƙofar kasancewar ko da Khalil ya bar parlourn ɗazu, ɗakin Sarah ya shige ya kulle kansa, sai ta ɗuka ta fiddo wannan tukunyar tare da tura hannun ciki ta ɗauko wannan mutum-mutumin na itace ta matse saitin zuciyarsa da ƙarfi tare da tsundumawa cikin tulun sannan ta kuma cirowa ta ƙara danna ƙirjinsa sannan ta saki daga sama ya faɗa tsumbul a cikin tulun tare da mayar da tulun ƙasan gado sannan ta shafa tsakiyar tafin hannunta sai ga hoton fadwa ƴar wajen Marfu'a, Bobo da Nana ƴan wajen Hassana, mimi ƴa guda da ta ragewa Na'ima, Sai Sultee da haidar ƴaƴan Nuratu. Wani murmushi tayi tare da zana maciji a hannunta, nan take macijin ya soma motsi tare da tafiya da sauri-sauri, ɗaya bayan ɗaya macijn nan ya dunga saransu suna zuba ihu kasancewar gaba daya suna wasa ne a tsakar gidan, yayin da iyayensu suke makarantar dake gaban gidan kaɗan, Na'ima ce kawai bata je saboda fama da ciwon kai da take yi kwana biyu, Lami kuma tana ɗaki ta saki ac tana sharar barci don bata jima da dawowa gidan ba daga gidan Aunty Rose Merry. Da gudu Na'ima ta fito jin wani irin mahaukacin ihu da Mimi ta saki sakamakon saran maciji, dai-dai nan Lami itama ta fito da sauri, a kan idanunsu macijin ya sulale yabi bayan flowers ya ɓace amma su basu ga ɓacewar nasa ba. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" "Lord of Jesus!" A tare Lami da Na'ima suka faɗi haka sannan suka yi kan ƴaƴan da gudu suna jijjigasu, cikin ƙanƙanin lokaci har fatan jikinsu ta sauya kala ta koma green yayin da baƙin kumfa ke fita daga bakunansu suna wani irin jijjiga, kuka Na'ima ta fashe dashi tare da ɗaura hannu a kai, can kuma ta nufi gate da gudu ta fita ko mayafi babu tana kuka tana faɗin a taimaka mata, tare suka dawo da maza biyar cikin gida, inda yaran suke ta kaisu tana kuka, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Mai ya same su?" Gaba ɗaya suka faɗi suna mai isa kusa da yaran tare da taɓa su. "Macijine ya sare su, nima ihunsu naji na fito sai naga macijin da sauri yabi bayan flowers ɗin na." Ɗaya daga cikin su ya nufi bayan flowers ɗin yana dubawa, "Tabbas kuwa! Ga saɓarshi nan a nan wajen!" Ya faɗi yana mai ɗago saɓar macijin. Huɗun da suke kan yaran suka kalli juna bayan tabbatar da babu sauran numfashi a jikin yara, "Yaro yi min bayani, sun mutu ko?" Faɗin Lami tana mai duƙowa tare da taɓa wuyan Mimi dake daf da ita. "Iya sai dai haƙuri, Allah ya riga ya ɗauki rayuwar waɗannan ƴaƴan." "Yesuuuuuu! Wannan azaba da jarabawar ya isa haka! Muna yabonka Ya Allah: mun dauki cewa kai ne Ubangiji. Dukan duniya tana yi maka sujadda, Uba Ma-dauwami. Agareka Malaïku duka suna tada murya, da Sammai da Ikoki duka da ke cikinsu. A gareka Charubin da Sarafin kullayomi suna tada muriya. Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki: Ubangiji Allah Mai-runduna. Samma da kasa cike su ke da Sarautar darajarka. Jama’a masu daraja ta zamaninka tana yabonka. Managarcin zumunta ta Annabawa tana yabonka. Jama’a mai-daraja ta Masu-shahada suna yabonka. Ekklisiya mai-tsarki cikin dukan iyakar duniya tana shaidanka: Ya Uba mai-sarauta mara-iyaka: Danka kuma mai-girma, mai-gaskiya, ma-kadaici: Ruhu Mai-tsarki kuma Mai-taimako. Kai ne Sarkin Daraja: Ya Almasihu. Kai ne Da matabaci na Uba. Sa’anda ka dauka ma kanka ka ceci mutane, ba ka yi kyamar cikin buduruwa ba. Sa’anda ka yi nasara da zafin mutuwa, ka budi Mulkin Samma ga masu-bada gaskiya duka. Kana zaune ga hanun damar Allah (Astagfutullah) a cikin darajar Uba. Muna bada gaskiya za ka zo ka zama mai-shari’anmu. Muna rokonka fa, ka taimaki bayinka: wandanda ka fanshe su da jininka mai-daraja: Ka maishe su a-cikin lissafin tsarkakanka, a-cikin daraja ta har abada. Ya Ubangiji ka ceci jama’arka, ka sa ma gadonka albarka. Ka malke su: ka ɗaɗɗaga su har abada. Yo da gobe muna girmama ka; Muna sujadda ga sunanka kuma kullum ba matuka. Ya Ubangiji da yardarka ka tsare mu kar mu mutu da zunubi. Ya Ubangiji ka yi mana jinkai: ka yi mana jinkai. Ya Ubangiji ka bar jinkanka shi rufto mana: da shike ban gaskiyarmu tana gareka. Ya Ubangiji, a-gareka na bada gaskiya, kada ka bar ni na rude har abada. Wannan yara da suka koma izuwa gareka a yau, ka hura ruhinsu a cikin tsarkinka, ka yafesu a cikin irin yafiya naka, mu kuma ka karemu kar muyi mutuwa irin nasu, Yaaa Yesu Almasihu uba!" Kallon-kallo mutanan nan suka shiga yi, don duk a tunaninsu Lami musulmace duk ganin da suke yi mata, sai yaji da suka ji uban yabo da ta kwararo suka fahimta, "Ashe aljihun baya ce!" Ɗayan ya kalli ƴan uwansa ya faɗi, shi kuma mai riƙe da fatar maciji yace, "To Allah ya ƙara nauyin ƙasa!" A fusace Na'ima tace, "To ba amin ba! Wannan wani irin Magana ce haka kuke yi? Ai ko da ace a cikin addinin Kirista aka haifi su Mimi bai kamata kuce haka ba tunda dai basu san komai ba, kuma ko yanzu a makarantar Annabi Ibrahim zasu tashi in Sha Allah! Balle kuma Ni uwarsu acikin musulunci aka haife ni kuma, na furta kalmar Ashhadu Allah ilaha Illallah, Wa Ashhadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu!" Da sauri mutumin yace, "Allah ya baki haƙuri, kiyi haƙuri dan Allah!" Na'ima bata kuma cewa komai ba sai kukan da take yi. Ita ta riƙa ɗaukar ƴaƴan