Sashe 72
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
ka tsine masa, a cikin mu'ujizozinka ka cire shaitan ɗin dake kusa da jikana yaaaa Yesu Almasihu mai ceto!" Tana faɗin maganar ne tana wani irin tuma a ƙasa tare da fasa ihu. Da sauri baba dake ɗaki ya fito, tuni Na'ima dake riƙe da Rabo tana kuka ta nufi wajen baba tare da miƙa masa shi tana mai ɗaura hannu a kai tana kuka. Baba kuwa yana amsar Rabo ya fahimci rai yayi halinsa saboda yanda jikinsa ya sake. Shimfiɗar da shi yayi akan tabarma tare da miƙar masa da hannu sannan ya miƙa hannu ya janyo zanin dake kan igiya ya lulluɓesa har kai. Wani irin baya Na'ima tayi ta tafi luuuuuu ta faɗi ƙasa sumamma! Da gudu su Marfu'a suka yi kanta tare da cicciɓanta suka kai ta ɗaki suka shinfiɗe. Lami kuwa sai kururuwa take yi, hakan ya jawo hankalin maƙota suka cika gidan tam. Baba kuma waya ya ɗaga ya kira abokansa su baba Sama'ila, har aka gamawa Rabo wanka Na'ima bata farfaɗo ba, sai can har ana tunanin kaisa kawai sai ta farfaɗo, har ɗaki baba ya shigo yayi mata nasiha tare da ce masa taje tayi masa addu'a, da kyar ta isa zuwa ta zube guiwowinta a ƙasa kusa da gawar, "Ka yafe min, ka yafe min!" Shine abunda Na'ima tayi ta maimaitawa tana kuka. "Ba'a kuka gaban gawa Na'ima, haramun ne!" Faɗin baba Sama'ila. Hassana ce ta kama hannunta suka fita daga ɗakin don har an kawo makara za ayi masa sallah, Gaba ɗayan su babu mai hijab ko ɗaya, a wajan maƙota suka ara sannan suka iya fita aka yi sallar dasu. Na'ima bata kusa haukacewa ba, sai da aka saka Rabo cikin mota za'a wuce, sai da aka turata cikin gida aka kullo ƙofar saboda yanda take wani irin mahaukacin kukan tashin hankali. Baba kuwa babu abunda dake zuwa bakinsa sai Allah yasa mutuwar nan ta zama sanadin shiryuwar ƴaƴan nasa. Bayan an dawo daga maƙabarta baba yayi ta kiran layin Khalil domin ya shaida masa mutuwar amma bai samunsa, layin Sarah kuma har ta gama ringin ba'a ɗauka ba. Can gidansu Khalil kuwa, Aunty Maryam zaune a ƙasa wayarta a hannunta tayi masa ƙuri tana jiran message daga Abdul-Hakeem akan ya saketa, ɗiririn saƙo ya shigo wayar, gabanta ne ya buga da ƙarfi don har sai da ta rintse idanu tana addu'a, dakyar ta iya duba saƙon, sai taga ashe daga bank ɗinta ne suna tayata murnar zagayowar ranar haihuwarta. Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke tare da hamdala a bayyane, daidai nan ya Abdul-Hakeem ɗin ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shigo, da wani irin sauri ta miƙe tana kallonsa gabanta na wani bugawa kamar zai faso ƙirjinta ya faɗo. A hankali ya riƙa takowa ita kuma tana matsawa har suka dangana ga jikin bago. Goshinsa ya haɗe da nata tare da faɗin, "Maryama, tun da na aureki tsayin shekaru biyar kenan, baki taɓa yi min wani abun da naji kamar in rabu dake ba, ko wani aiki nake yi na wahala a wajen aiki, idan na tuna da ke, sai inji farin ciki ya mamaye zuciyata tare da fuskantar abunda nake yi domin inyi in gama in dawo gida na ganki, ki sani shi aure rai gare shi, idan lokacinsa yayi, da daɗi da babu daɗi sai an rabu! Kiyi haƙuri Maryam, zan ƙara maimaita maki, baki yi min komai ba sai alkhairi, kiyi haƙuri da abunda zai fito daga bakina yanzu," sai dai ya ɗan yi jim yana kallonta sannan ya haɗe hannunta biyu tare da faɗin, "Ki yafe min, na sake ki saki ɗaya Mary......" Bata bari ya kai ƙarshe ba ta fashe da wani irin kuka tare da gittashi da sauri ta haura sama tare da banko ƙofa, shi kansa Abdul-Hakeem ɗin wasu zafafan hawaye ne suka kwaranyo masa daga idanunsa, ya rasa wani irin wutane yake ta ruruwa a zuciyarsa, haka nan ya dunga jin zafi da raɗaɗi, can kuma ya soma jin shi kawai aure ne ya haƙura dashi, kamar ana ingizashi yaji domin yazo ya saki matarsa da a kullum burinta ta kyautata masa. Aina'u bata koma ɗakin Hajiya ba saboda ƙira'ar dake tashi, sai ta koma can baya ta inda baza taji sautin karatun ba ta zauna tana mai jin zafin furucin Nafeesa, "Sai na ɗanɗana maki azababbiyar mutuwa in dai ni ƴar Elizabeth da Nuhu ce!" Ta faɗi maganar tana sakin kwafa. A ɗakin Hajiya kuwa, Sarah tayi kuka kamar zata mutu, bata soma jin salama a ranta ba sai da aka kunna ƙira'ar nan. Zuwa anjima can sai ga Khalil ya shigo ɗakin, shi bai ma ɗauka ta iya zuwa ba nan ɗin ba, sai da ya shiga ɗakinta ya taras bata nan sannan ya dawo nan, "Ya ƙarin haƙuri Nafeesa?" Luhu-luhun idanunta ta ɗago tare da faɗin, "Alhamdulillah!" Kallon Sarah Khalil yayi tare da faɗin, "Mine taso mu tafi yamma nayi." "Ina zaku?" Hajiya ta tambaya, "Asibiti nake so muje na dubata." Gyaɗa kai Hajiya tayi tare da faɗin, "Allah ya ƙara sauƙi, sai kun dawo." Da ameen Khalil ya amsa, ita kuma Sarah ta miƙe ta fito ya biyo bayanta, abunda ya matuƙar bashi mamaki shine, lokacin da take cikin ɗakin Hajiya, babu wannan warin da take yi ko kaɗan, amma tana fitowa warin ya dawo. Bai ce komai ba har suka isa ɗaki, kalonta yayi tare da faɗin, "Za'a canza pampers ɗin ne?" Girgiza kai tayi. Sai ya nufi wardrobe ya ɗauko hijjab ɗin ta ya saka mata sannan suka fito, a cikin mota ma karatun ya kunna, yana kallon Sarah yanda ta kwantar da kanta jikin kujera tare da lumshe idanu. Suna isa ya shiga da ita lab ya ɗibi jininta ya bada ayi gwaje-gwaje sannan suka fito suka nufi X-ray room, nan ma sai da yayi examining Virgina ɗinta sosai. Kusan test kala goma aka yi mata, basu suka dawo gida ba sai past 10, wasu tests ɗin sun fito a ranar, wasu kuma sai bayan 8days zasu fito, wanda suka fito a ranar guda huɗu ne, kuma gama ɗayansu komai normal, guda ɗaya ne ma a ɗan ga yest infection kaɗan shima kuma na ciki ne, babyn cikinta lafiya ƙalau. Suna dawowa gida ya sake yi mata wanka ya canza mata pampers tayi sallar isha'i sannan suka ci abincin da ya tsaya ya saya masu a restaurant. Yana son faɗa mata ɗan wajen Na'ima ya rasu amma bai son hankalinta ya tashi, don sun yi waya da baba daga baya, kuma ya faɗawa baban bata da lafiya sai dai bai faɗa masa asalin ciwon ba, baban yace masa ba sai tazo ba, tayi zamanta kawai zai faɗa masu bata da lafiya. Haka suka kwanta ba tare da ya faɗa mata ba. Bai ji kyamarta ba, yanda suka saba kwana haka suka kwanta kwance a kan ƙirjinsa, can cikin dare ya jisa sharkaf, cikin sauri ya tashi ya kunna bedside lamp, cike da mamaki yake kallon uban fitsarin da Sarah ta lafta duk da pampers ɗin jikinta ga kuma tsutsotsin nan sun fara fitowa. Tagumi ya zuba yana kallonta tana bacci peacefully bata ma san mai ke faruwa ba, hawaye ne suka gangaro masa na tausayinta, ya jima yana kallonta kamun ya sauka daga kan gadon ya cire boxer ɗin jikinsa don ya jiƙe sharkaf, bayi ya shiga ya wanke jikinsa sannan ya dawo ya soma tashin ta a hankali, miƙa ta soma yi, sai ji tayi hannunta ya sauka a kan lema, da sauri ta ware idanunta tare da tashi zaune tana mai faɗin, "Happiness, fitsari kwance nayi? Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Na shiga uku!!" Tausayi ta bashi sosai, sai kawai ya sunkuceta ya kaita bayin ya ajiye a tub sannan ya fito ya kwashe zanin gadon ya kai bayin tare da ɗauko wani ƙaramin towel da ruwa da liquid soap ya goge katifar sosai sannan ya saki fanka tare da kwasar janin gadon ya shigo dashi bayin ya zuba a bucket sannan ya isa gareta, babu abunda take yi tunda ya ajiyeta sai kuka, "Wallahi tallahi zaki ɓata min rai Sarah! Kanki farau ko ƙarau? Haba! Baki san kukanki na tada min da hankali ba?" Yana gama faɗin haka ya shiga cire kayan dake jikinta, sosai yaji tsoro lokacin da ya cire pampers ɗin jikinta gaba wannan jajayan mitsi-mitsin tsutsotsin sun koma canza colour, wasu sunyi green, wasu yellow-yellow, wasu kuma farare. Bai bari ta gani ba ya ajiye pampers ɗin sannan ya wasa ruwa ya shiga cuɗa jikinta. Sai da ya gama mata wankan sannan ya dawo da ita ɗakin ya ajiyeta a kan gado inda babu lema ya saka mata wani pampers ɗin tare da kayan bacci sannan ya mayar da ita ɗakinsa ya rufeta da bargo ya dawo nata ɗakin ya wanke kayan nan tsaf sannan ya koma ɗakinsa ya kwanta tare da jawota jikinsa. Aina'u dake ɗakin can side ɗin Hajiya tana kallon komai ta tsakiyar tafin hannunta, bata san lokacin da ta jefi mirror da wayarta dake gefensa ba, sai ji kake tatsatsatsatsa! Tafin hannunta ta matsa da ƙarfi, wannan karon _Hell Ofulafu_ bai bayyana ba, wannan mummunar halittar ne ya bayyana tare da faɗin, "Kina da wutar ciki Aina'u, duk abunda muka ce zamu yi, za muyi shi, shin bamu cika maki biyu daga ciki bane? Rabo ya mutu, Abdul-Hakeem ya saki Maryam, yanzu saura warin da za'a turawa Khalil, korar Abdul-Hakeem daga aiki, mutuwar Nafeesa da kuma mantar da LTD Abdullah da Muhammad Kabiru cewar suna da uwa da ƴan uwa a Kaduna. Kar ki ƙara neman mu akan wannan buƙatar, sai dai idan wata buƙatar ke gare ki." Yana gama faɗin haka ya ɓace. Ajiyar zuciya Aina'u ta sauke tare da kwanciya rub da ciki, can kuma ta miƙe ta buɗe zip ɗin jakarta ta ɗauko murɗin wiwi ta saka a baki tare da kunna lighter ta hau zuƙa, sai da tasha murɗi uku sannan ta kora codine kwalba ɗaya sannan ta faɗi yarab a kan gadon ta hau bacci. Bayan kwana uku, sam Hajiya bata lura aunty Maryam bata gidan ba, don tare suka tafi da Moon, ya Abdul-Hakeem kuwa yayi wani irin zugewa, don washa garin ranar da ya saki aunty Maryam aka dakatar dashi daga aiki, Hajiya kuma ta