← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 112

Sashe 84

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

zuba maki?" Ɗaga idanu sama tayi tare da faɗin, "Wanda kake ci shi zaka zuba min." Jellof rice ɗin ya zuba mata tare da kaza sannan ya ki plate ɗin har gabanta tare da faɗin, "Gashi _Ƙanwar matata_" wani irin ƙululun baƙin cikine ya mamaye zuciyar Aina'u jin sunan da ya kira ta dashi wai _Ƙanwar matata_! "Nafi gaban haka wallahi!" Aina'u ta faɗi cikin zuciya, amma a zahiri sai tayi wani irin murmushi tare da kallon yanayin Sarah ta gefen idanu, abun yayi wa Aina'u daɗi ganin confusion a idanun Saran. Spoon ta saka ta ɗebo abincin tare da sakawa a baki, lunshe idanu tayi jin wani daɗi da ya mamaye kunnuwanta don Sarah gwana ce wajen iya girki duk da ba yi suke yi a gida ba. Aina'u na cin abinci a lokaci guda kuma tana jan Khalil da hira, shi kuma kamar wani wawa ya saki baki sai ɓaɓɓaka dariya yake yi. Sarah miƙewa tayi ta bar wajen zuciyarta na susa, duk da tasan babu aure tsakanin Aina'un da Khalil ɗin idan dai har ba mutuwa tayi ba, sai taji wani irin matsanaicin kishi da damuwa yanda Khalil ɗin ya manta tana wajen, da dane, Aina'u bata ma isa ta ƙariso inda suke ba balle har ta zauna kusa dashi, da bata jin daɗin yanda Khalil ɗin yake ɗaurewa Aina'un fuska ganin su Na'ima yanzu har wani respect yake basu matsayin yayyin matansa, amma kuma ya kasa sabawa da Aina'u, sai ta bar hakan matsayin rashin haɗuwar jini, amma yanzu lokaci guda da taga wannan sauyin duk sai taji matsanaicin damuwa ya kamata. Bayan ta hau sama sai ta canzawa twins pampers tare da saka masu kayan baccinsu sannan ta sayar dasu har bacci ya ɗauke su lokacin ƙarfe tara da mintuna biyar amma har yanzu Khalil bai dawo ba, kwanciya tayi tare da rufe idanu amma sai taji gaba ɗaya baccin yaƙi zuwa, tashi tayi ta sauka a kan gadon tare da fitowa ta tsaya daga nan sama tana hangen Khalil kusa da Aina'u kamar zasu shigewa juna yana nuna mata abu a waya suna dariya. Da sauri ta juya ta bar wajen saboda bata son kawo zargi a zaman aurenta dashi. Ko da ta koma ɗaki, sam bacci ya kasa zuwan mata sai juyi take yi tana saƙe-saƙe a zuciya tare da duba agogo a wayarta, sai da agogo ya buga ƙarfe ɗaya sannan taji buɗe ƙofar Khalil ya shigo ɗakin, tana jinsa ya shiga toilet yayi wanka kasancewar kullum zai kwanta sai yayi wanka, kayan bacci ya saka sannan ya hayo gadon tare da gyarawa twins kwanciya ya mayar dasu ƙarshen gadon ahankali gudun kar su tashi sannan ya jawo Sarah jikinsa ya rungume, duk tana jinsa sai tayi kamar bacci take yi har ta soma jin saukar numfashinsa alamar baccin ya ɗaukesa. Ajiyar zuciya ta sauke domin ta rasa wani irin tunani za tayi, sai wajajen ukun dare bacci yayi gaba da ita. Washa gari da sassafe bata nuna masa komai ba ta haɗa masa breakfast da duk abunda zai buƙata, haka kayan da zai saka bayan ya fito daga wanka. Ita ta taimaka masa ya saka kayan sannan yayiwa twins kiss a kumatu kasancewar basu farka ba sannan suka sauko ƙasa tayi serving ɗinsa ya karya. Sun rabu kamar kullum bayan yayi hugging ɗinta tare da yi mata kiss ita kuma tayi masa addu'ar Allah ya tsare sannan ya tafi. Da sauri Aina'u dake kallon komai a bangon ɗakinta dake shashin Hajiya ta fito cikin uban kwalliya tare da isa inda yake yana ƙoƙarin buɗe mota, "Manyan gari kenan, har za'a fita ba tare da an ganni ba!" Da sauri Khalil ya kalleta tare da faɗin, "I'm so sorry Ai'n, na kusa nayi latti ne shine nake sauri, kin san jiya mun sha hira, abunda ya makarar dani kenan." "Kar inzo yau kenan?" Faɗin Aina'u tana wani kashe idanu. Waro idanu Khalil yayi tare da faɗin, "Wa! Ai ko da har ɗakin Hajiya zan biyo ki, baki san yanda hira dake yake matuƙar sani nishaɗi ba ko? Kar ma ki fara min wannan wasan." Wani shu'umin dariya Aina'u tayi tare da faɗin, "Hakane! To mu fita tare ka ɗan rage min hanya nima dama fitan zan yi." Da sauri ya buɗe mata gaban mota sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver yaja motar suka bar gidan. Sakin labule Sarah tayi tare da jinginar da bayanta jikin window ɗin tana faɗin, "Ya Allah ka tausaya min kasa ba abunda nake tunani bane akan mijina da ƙanwata. Wunin ranar sukuku tayi sa, ƙarfe shida Khalilullah ya dawo kamar yanda ya saba, sai dai kuma tare suka dawo da Aina'u kamar yanda suka fita tare, kasancewar Sarah na ɗakinsa tana fesa airfreshner, sai tayi saurin ɗaga labulan window jin ƙarar motarsa, gabanta ne ya buga da ƙarfi ganin Aina'u ta fito daga motar hannunta ɗauke da wata ƙatuwar leda bakinnan kamar zai yage tsabar washesa da take yi. Sakin labulan tayi tare da saukowa ƙasa sauri, buɗe ƙofar Khalil yayi ya shigo fuska ɗauke da fara'a, ganin yanayin matar tata duk sai jikinsa yayi sanyi, gashi tayi bala'in kyau cikin wani Indian material da tayi ɗinkin straight gown dashi, gashin kanta kuma ta kama shi in a middle ponytail, jelar gar dokin wuyanta, fuskanta yaci makeup mai ɗaukar idanu, "Wife, lafiya naga fuskanki haka?" Maimakon ta bashi amsar tambayarsa, sai cewa tayi, "Ina kuka je kai da Aina'u? You left this house together and you also came back together." Murmushi yayi tare da faɗin, "Wai Aina'u? Rage mata hanya nayi wai zata wajen ƙawarta, luckily kuma sai muka sake haɗuwa shiyasa muka dawo tare." Sarah bata iya cewa komai ba sai kallonsa da ta riƙa yi, "Come on, smile!" Ya faɗi yana mai bata side hug. Yau ma dai irin na jiya aka kuma, Aina'u ta kuma zuwa kuma still sai 1am Khalil ya dawo ɗakin, abun na matuƙar damun Sarah a zuciya, sam bata samun kulawar Khalil yanzu, ya kai yanzu ko kwalliya tayi bai kallo bare ya yaba, girki kuma Aina'u ta koma yi masa, idan Sarah ta zuba masa abinci, sai yace mata Aina'u zata kawo masa, tun Sarah na daurewa kusan sati Uku, har ta zuciya wata rana taje har side ɗin Hajiya ta samu Aina'u a ɗaki bayan Khalil ya wuce asibiti, zaune take tana kallon tafin hannunta, ba kowa bane a ciki sai Khalil dake zaune yana duba petient, bata san da zuwan Sarah ba kasancewar ba ita take kallo ba a wannan lokacin, turo ƙofar da Sarah tayi ne ya dawo da ita cikin hayyacinta tayi saurin kallon ƙofar don tasan Hajiya da Laure ko giyan wake suka sha baza su shigo mata ɗaki ba, wani kallon banza ta watsawa Sarah da taga itace a ƙofar ɗakin, a zuciye Sarah ta ƙarisa ɗakin tare da ɗauke Aina'u da mari sannan ta nunata da yatsa tare da faɗin, "Dan ubanki ki tattara kayanki ki bar gidan nan, idan ba haka ba, sai na kakkaryaki, shegiya ƴar iska, na gama gane take-taken ki, so kike ki ɗauke min hankalin miji ko? Don baki da kunya mijina kike so? To wallahi ahir ɗinki! In the first place ma na kasa gane uban da kike yi cikin gidan nan tunda ba gidan ubanki bane, to ki saurareni da kyau, ki tattara ki bar gidan nan tun kan inyi maki watsi da kayanki wallahi. Wawuya shashasha!" Tun da Sarah ta fara magana har ta dire Aina'u ko tari bata yi ba sai ma wani murmushi da take yi, amma deep down ita kaɗai tasan mai take shiryawa cikin zuciyarta. Sarah kuwa fita tayi tare da banging ƙofar. Har akai kwana uku Sarah bata kuma ganin Aina'u ba, sai tayi tunanin ko taji abinda ta faɗa mata ne ta bar gidan, sai dai kuma gaba ɗaya ta kasa gane kan Khalil, don wani lokacin har mancewa yake yi idan zai kirata sai yace, "Aina'u." Sarah gaba ɗaya hankalinta ya tashi ta soma tunanin mai Aina'u tayiwa Khalil haka. A ran kwana na huɗu, kawai sai ganin Khalil tayi ɗauke da akwatin kaya, Aina'u a bayansa shikuma ransa a mugun ɓace, a nan gaban Aina'u ya hau Sarah da faɗa abunda bai taɓa yi ba, "Wannan wani irin haukane da jahilci! Ƙanwar taki kika kora a gidan nan saboda selfishness ɗinkin? Kin bani mamaki Saratu! To yanzu na dawo da ita da kaina, she will stay here with us." Yana gama faɗin haka ya ɗauki akwatin tare da kallon Aina'u yace, "Ai'n, follow me." Da sauri Sarah tasha gabansa tare da faɗin, "Aina'u bata da ɗaki a sama." "Let go of my way Sarah Nuhu! Kar ki ja inyi maki abunda ban taɓa yi maki shi ba a daran nan." Baki sake Sarah ke kallonsa, yayin da Aina'u ke wani irin shu'umin murmushi. A gaban idanunta Aina'u ta bi bayan Khalil suka haura sama. Da daddare bayan Khalil ya dawo ɗakin Sara, don yau sun kai kusan 2am suna hira da Ai'n kamun ya dawo ɗakin Sarah. Sai da ya gama komai ya hawo kan gadon sannan Sarah ta miƙe ta zauna tare da kunna bedside lamp tare da faɗin, "Ka tashi za muyi magana Please!" A raunane tayi maganar yanda zai ji tausayinta, amma ko juyowa bai yi ba don juya mata baya yayi abunda bai taɓa faruwa ba tunda suka yi aure. Ƙara maimaita abunda tace tayi a karo na biyu, a fusace ya juyo tare da faɗin, "Baccin baza ki bari inyi cikin salama ba? Wato kin ɗauko wani hali da ba naki ba kin ɗaurawa kanki ba? Saboda tsabar kishi da rashin sanin ya kamata, shine za ki riƙa kishi da ƙanwarki ciki ɗaya, Aina'u fa ƙanwarki ce, _Ƙanwar matata!_ kin taɓa jin inda miji ya auri ƙanwar matarsa uwa ɗaya uba ɗaya kuma ba mutuwa tayi ba? Ni dalla malama kin isheni!" Yana gama faɗin haka ya fita daga ɗakin tare da bugo mata ƙofar da ƙarfi sai da twins suka firgita tare da tsala ihu. Aina'u kuwa daga ɗakinsa tana kallon komai, daga ita sai wata ƴar iskan rigar bacci da babu komai a ciki ta fito ta tsaya a bakin ƙofa, Khalil na zuwa wajen ta jawo hannunsa
Chapter 84 · 0% Book details