Sashe 29
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 7 min read
ne, idan kuma yace no, tofa ko ana ha maza ha mata babu mai canza shi. Kuma duk gidan tsoransa ake ji. Shine babba kuma zai iya kaiwa shekaru hamsin da biyar a duniya. Daga shi sai yaya Barrister (Muhammad Kabir) kenan, shi yana da sanyi hali. Ba k'aramin abu ke b'ata masa rai ba. Idan kaga yana zafi da magana sosai, to fa a kotu ne musamman idan Shari'a ake yi akan fyad'e. Shi yaci gajiyar Papa don tun yana k'aramin yake fad'in "Papa idan na girma irin aikinka zan yi in rik'a Yankewa mugaye hukunci. Daga Barrister sai Abdul-Hakeem wanda shi kuma SSS ne, (D'an sandar farin kaya). Daga shi sai _Doctor Khalilullah_, sai Aysha, sai auta Nafeesa. "_Khalil_ kana jina kuwa." Fad'in ya Abdul yana tab'a hannunsa ganin yayi zurfi a tunani. "No, babu komai ina zuwa." Fad'in _Khalil_ tare da nufa part d'in Hajiya. Kai tsaye d'akinsa ya shige yana safa da marwa. Kwankwasa k'ofar d'akinsa aka yi, da sauri ya juya yana kallon k'ofar. Hannu ya kai ya danna wani switch sai ga Laure ta bayyana akan screen d'in dake saman k'ofarsa. Ajiyar zuciya yayi tare da nufa k'ofar d'akin ya bud'e, "Yaya _Khalif_ ina kwana?" Saude ta fad'i a sanyaye don tun jiya take jinta wani iri ganin uwar d'akinta babu lafiya. "Lafiya k'alau ya aka yi?" Ya amsa tare da jefa mata tambaya. "Hajiya ce tace in fad'a maka yau kar ka bar gidan nan akwai bak'in da zasu zo anjima." Shuru yayi yana kallon Laure kamar ita ce Hajiyar, can kuma ya nisa tare da fad'in, "Ok, to jeki." Yana gama fad'in haka ya rufo k'ofar tare da zama a bakin gado ya rik'e kai. Gaba d'aya natsuwa ta bar jikinsa. Gabansa sai dukan tara-tara take yi. Bai isa sakawa cikinsa ko ruwan Lipton ba har k'arshe sha d'aya yana nan zaune a d'aki yana sak'awa da warwarewa. Su aunty Maryam da Laure kuwa, sai kaiwa da komowa suke yi a kitchen suna had'awa bak'i abinci. Nafeesa ta riga kowa zuwa kasancewar ita mazauniyar Kaduna ce. Ana tayi aure a kabala shooting range. Hankalinta sosai ya tashi ganin halin da mahaifiyarsu take ciki. Don har a wannan lokacin jiri hajiye take gani, kuma idanunta sunyi luhu-luhu alamar taci kuka. "Hajiya dan girman Allah mai ke faruwa? Idan dai akan su uncle ne, dan Allah ki fitar da damuwarsu a zuciyarki. Har kuka gama zaman ku da Papa bai saka maki ciwo ba, sai y'an uwansa ne zasu buwayeki. Dan Allah Hajiya ki bari." Girgiza kai Hajiya tayi tare da fad'in, "Uhm, baza ki gane ba Nafeesa, bari dai sauran y'an uwanki su iso. Ni ba akan y'an uwan mahaifinku bane. Da sune ne abun da sauk'i." Shuru Nafeesa tayi tana tunani a zuciyarta to mai ya faru idan har ba su uncle bane. K'arfe sha d'aya da mintuna arba'in, yaya Barrister ya iso gidan shi da matarsa aunty Khairat da yayansu uku, Sam'an, Sahla da Nu'aima. Nan aka dunga oyoyo-oyoyo. Ko mintuna goma basu yi da zuwa ba, soja marmari daga nesa, LTG Abdullah ya iso shi da Aysha da kuma tawagar sojojin da suka yiwa unguwar k'awanya. Don gaba d'aya unguwar sai da suka shaida *_Lieutenant General Abdullah Nurudden Muhammad_* ya shigo unguwar. Tun da _Khalilullah_ ya lek'o ta window ta can saman d'akinsa yaga uban sojojin sun gewaye gate d'in gidan, wasu ma har ta cikin gidan yaji kamar an cire lakar dake jikinsa. Laure gaba d'aya ta rud'e don har wani zawo-zawo take ji sabida ba k'aramin tsoro da shakkar _LTG Abdullah_ take yi ba. Don shi fuskansa ma bata cika fara'a ba. Kai tsaye gaba d'aya suka wuce d'akin Hajiyar ban da _Khalil_ da ko lek'owa parlor bai yi ba. Har k'asa k'asa ya _LTG_ ya duk'a gaban gadon da take tare da fad'in, "Hajiya ina wuni, mun same ku lafiya? Ashe baki ji dad'i ba. To menene amfanin _Ibrahim_ a cikin gidan nan da ba zai iya kai ki asibiti ya duba ki ba. Wallahi wani irin iskanci ne. Ina yaje?" Hawaye Hajiya ta soma yi tare da fad'in, "Ni na hana a kai ni asibitin, don ciwon dake damuna, _Khalil_ d'in ne sanadiyarsa. Marmari, _Khalil_ ya b'ata mana sunan famili. Ya rusa duk wani tarbiyar da muka ginasa akai. So mu had'u mu duka a parlor, bayan anci abinci, sa muyi maganar." Kai a k'asa zuciyarsa na tafasa ganin mahaifiyarsa na hawaye yace, "Hajiya abinci ba zai ciwu ba, har sai naji abunda yake damunki nayi maki maganinsa tukun." Gaba d'aya su Barrister, Aysha da Nafeesa har da yaya Abdul suka ce, "Hajiya abinci tabbas ba zai ciwu ba har sai munji matsalarki." "Ku aika Laure ta kira _Mu'azzam_ a d'akinsa ya fito mu tafi can parlor ayi maganar a can." Mik'ewa Nafeesa tayi tare da nufa corridor d'in da zai sadata da d'akin yayan nata tana mamakin wani irin laifi ya aikata da har Hajiya take cewa ta b'ata masu sunan family. "To ko zubar da ciki yake yi a asibitinsa?" Fad'in Nafeesa cikin zuciyarta dai-dai lokacin da take knocking d'in k'ofar d'akina. Bud'ewa yayi, kallon fuskansa kawai za kayi ka tabbatar yana cikin tashin hankali. Kuma ba komai ke d'aga masa hankalin ba irin fushin Hajiya. "Nafeesa!" Ya fad'i a hankali yana kallonta. "Na'am yaya _Khalil_. Tun d'azu gaba d'aya muka zo amma babu kai a wajen. Hajiya tace kaje parlour duk muna can." Fitowa yayi gaba d'aya tare da kullo k'ofar yace, "Muje Nafeesa. Hankalina ne gaba d'aya a tashe. Har da ya Abdullah ko?" Gyad'a masa kai tayi suna tafiya a jere tare da fad'in, "Yaya _Khalil_ wai don Allah mai ke faruwa ne Hajiya ta kira mu gaba d'aya? Wani abun kayi ne?" Bai ce mata komai ba har suka k'ariso parlourn. Bai iya d'aga kai ya kalli kowa a cikinsu ba. Neman waje tayi daga gefe ya zauna kansa a k'asa tare da fad'in, "Ina wuni ya Abdullah? Sannu da zuwa ya Barrister. Kun zo lafiya?" Babu wanda ya amsa gaisuwarsa. Bai damu ba don dama ya san dole hakan zata kasance. Ya Abdullah kuwa duk ba sai ainahin abunda _Khalil_ d'in ya aikata ba, sai jifansa yake yi da wani irin mugun kallo. Su kad'ai ne a parlor, don ko Barrister da yazo da matarsa, tana can ita da Y'ay'anta a part d'in ya Abdul-Hakeem. Sune kawai isu-isu a parlourn. Don maganar tasu tana buk'atar privacy. "Abdul-Hakeem bud'e mana taro da addu'a." Fad'in Hajiya wacce ke hakimce a kan kujera tana girgiza k'afa. Sai bayan yaya Abdul-Hakeem d'in ya gama addu'ar sannan Hajiya tace, "Na kira ku ne anan wajen ba don komai ba, sai don saboda _Ibrahim_. Na san dukkan ku kun san bak'ak'en maganganu da kuma zagi da nake jurewa daga wajen dangin ubanku. Tun yana da rai suka kafa min k'ahon zuk'a har ila yau da ya kasance babu shi a raye. Kuma kun san cewa iyayenku suna son had'a _Khalil_ aure da Nina wanda shi kuma yak'i bada fad'in kai a cewarsa bata da kamun kai ita mazinaciya ce." Da sauri yaya Barrister yace, "Hajiya idan dai a kan wannan maganar ce ta Nina, to ba wai bane. Don ni da kaina na tab'a ganinta a wani babban hotel a Kano ita da wani sa'an mahaifinta." Da k'arfi Hajiya tace, "Kayi min shuru! Ai ita da _Khalil_ d'in zani ce ta tadda muje." Da sauri _Ya LTG_ yace, "Hajiya ban fahimta ba." Gyara zama tayi tare da fad'in, "Yanzu kuwa zaka fahimta. Kai _Khalil_ yi masu bayani abunda ka aikata." Kansa a k'asa gabansa na fad'uwa ya d'ago ya kalli Ya Abdullah, wata uwar hararar da ya watsa masa ya saka yayi saurin sunkuyar da kai k'asa." Wani mahaukacin tsawar da yayi, ba _Ibrahim_ kad'ai ba, hatta ita kanta hajiyar sai da ta tsorata. "Za kayi magana anan wajen ko sai na taso na taka cinyarka tayi dagwa-dagwa!" A razane _Khalil_ yace, "Hajiya wallahi, tallahi wa billahil azim ba halina bane. Tsautsayine ya saka nayi mata fyad'e har ta samu ciki." A mugun mamakance da bak'in ciki ya Barrister da ya Abdullah suka ce "Fyad'e!" Wani mik'ewa _Lieutenant Abdullah Nurudden Muhammad_ yayi tare da isa inda _Khalilullah_ yake tare da............