Sashe 39
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
A zafafe Uncle Ameeru ya mik'e tare da fad'in, "Na rantse da Allah ba zan tab'a bari ayi auren nan ba. Dole ne muje gidan can yanzu mu saka su a gaba muje mu kwaso duk abunda muka kai gidan. Mun janye maganar auren." Wani murmushi uncle Ridwan yayi tare da fad'in, "Gaskiya baka da hankali Ameeru!" "Rabu dashi mana, ni ai kallon wawa nake masa daga nan zaune. Ko ka manta cewa yayi ba zai auri y'armu ba saboda ta lalace? A gaban idanunmu gaba d'aya babu kunya ya fad'a mana wannan maganar. Har yanzu maganar tana sukar zuciyata. Ai ni wannan abu ba dad'i yayi min wallahi. Naji dad'i sosai da ya zam yarinyar gantalalliya ce. Kun ga kenan mun samu hanya mafi sauk'i da zamu cimma burinmu. Kawai had'a kai za muyi da yarinyar mu kashe d'an iska da ransa, musamman ma Bilkisu da ta hana mu rawar gaban hantsi. Shegiya duk hukumomi ta haifo, daga soja, sai d'an sandar farin kaya da kuma d'an iskan nan Barrister da ya gaji ubansa." Fad'in uncle Zayyanu. Uncle Shamsu kuwa cewa tayi, "Ni wallahi duk cikin y'ay'an Bilkisu nafi tsanar d'an iskan yaron nan _Khalil_ da wansa Abdullah. Kun ga da ace yaron nan soja a Kadunan nan yake, wallahi watarana sojoji zai saka su b'alla k'afafuwanmu. Bakwa ganin yanda yake nuna isa yana wani fankama kawai don ya kasance soja. Ni dama a kashe d'an iska acan wallahi." "Shegu taurin rai garesu kamar ubansu. Wani irin farmaki ne bamu kaiwa Nura ba, amma yana nan kamar kainuwa har sai da lokacinsa yayi. Mun sha wuya wallahi." Fad'in uncle Ameeru. Uncle Shamsu yace, "To yanzu dai mu tsayar da mafita. Mai kuke ganin za muyi? Ta yaya zamu b'ullowa ita yarinyar da zai aura?." Uncle Ridwan ya fad'i. "Ku bar min duk wannan a hannuna." Fad'in uncle Ameeru. "Yauwa Ameeru. Na sanka indai ta wannan fannin ne. Da ace yarinyar nan da ta turo sak'o ta bar wani makama da za mu bibiyeta, da ta cab'a don ta hanyarta zamu samu bayanai masu dama. Don ga dukkan alamu bak'in ciki take yi shiyasa ta tona asirin wancen, watak'ila kuma k'awa ce. Duk da hakan dai kuma za mu bincike gaskiyan labarin da ta bamu a kan gidan sabida mu san ta yanda zamu b'ullowa abun." "Yauwa nima abunda nake so in fad'a kenan." Uncle Zayyanu ya fad'i. Hajiya babu abunda take yi sai shirye-shirye. Gaba d'aya ta gama kiran dangi na kusa da na nesa na shaida masu auren _Khalil_ da za ayi nan da sati biyu. Aunty Maryam kuwa har ta gaji da zuwa kasuwa ita da aunty Khairat, don tun da aka saka bikin Aunty Khairat tazo don tuni har sun koma Kano, sai dai can ta baro Barrister shi sai ana saura 2days biki zai zo sabida aikinsa. Duk da kayan lefen kusan gaba ki d'aya a Dubai suka sayo har da akwatin, don private jet suka bi suka yo sayayyar kasancewar duka bangarori hud'un sun saki kud'i, Yaya Abdullah 5million ya bada, ya Barrister kuma ya bada 3million, ya Abdul-Hakeem ya bada 2.5million, shi kuma mai gayya 10.million ya bada. Hajiya kuma ita ta saya akwati set d'aya mai guda goma sha biyu. Gaba d'aya jimillar kud'in suka kama 20.5million. Dasu gaba d'aya su aunty Maryam, aunty Khairat da wata autar su Hajiya suka tafi Dubai. Sai da suka sayo akwatina set uku, na hajiya dozen, sauran biyun kuma mai guda six-six sai dai masu d'an karan tsada kuma gaba d'aya sai da aka cika su da mahaukan kaya masu tsada, don lesses d'in da aka saka babu na k'asa da 200k, kaya dai kamar za'a bud'e shago. Bayan sun dawo gida Nigeria kuwa, haka suka dunga yawon kasuwa suna k'aro wasu abubuwa don sai da suka dawo Hajiya tayi ta fad'a ganin babu kayan uwa da uba. Ana Nigeria suka k'ara had'o set d'in akwatuna guda uku irin mai biyu d'innan da kit. D'aya shaddojine da takalmar maza da turare da huluna masu tsada wanda ya kasance na Baba, sai d'ayan set d'in kuma aka zuba atamfofi da lesses da manya-manyan mayafai da takalma da turare. Shi kuma na Lami, sai d'ayan set d'in akai wa y'an uwan Sarah komai kala biyar-biyar, lesses kowa ta samu biyu, haka shadda da atamfa, sai takalma uku-uku da jakunkunarsu har da sark'a da y'an kunne. Gaba d'aya a parlourn Hajiya aka zube kayan. Sosai Hajiya taji dad'i don gaba d'aya babu k'arya. Yawan kayan ya saka ba komai Hajiya ta iya gani ba daga cikin kayan Sarah don akwatuna har set uku, wanda gaba d'aya jimillar akwatunanta kawai sun kama 24. _Khalil_ kuwa sai dad'a gyara b'angarensa yake yi wanda ya kasance four bedroom a k'asa da wawakeken parlour guda biyu mai d'auke da, dinning sai kitchen da store wanda girmansa da tsaruwarsa ma kawai abun kallo ne. Sama kuma two bedroom da parlour d'aya. Can gidansu Sarah kuwa, Lami da Aina'u ne kawai basa farin ciki da wannan aure da za ayi, gwara ma Lami ita gani kawai take yi idan akai auren shikenan za'a daina kawo mata abun arziki, yayin da Aina'u ita tsabar hassada ce da mugun hali. Babu kuwa kullum bakinsa bai rufuwa sabida farin ciki, sai shirye-shirye yake yi. Don yanzu Alhamdulillah har waje yana iya fita ba tare da sandar ba. Yana zuwa wajen abokansa suna ta shirye-shirye don Baba yace har walima sai yayi. Sarah kuwa babu wacce ke fad'o mata a rai irin K'awarta Muniba, duk duniya ita kad'ai ce k'awarta, gashi kuma tuni iyaye sun raba tsakaninsu. Kamar Baba ya san halin da take ciki, har gida yaje ya samu liman (Mahaifin Muniba) ya bashi katin gayyata sannan kuma ya rok'eshi alfarmar ya bar Muniba tazo wajen Sarah suyi shirye-shiryen biki don duniya bata da wata k'awa sai Muniba. Mahaifin Muniba yaji dad'i sosai jin Sarah za tayi aure kuma yace wa Baba in Sha Allah Muniba zata zo. Sarah na zaune tana sak'awa da warwarewa, don basu jima da waya da _Khalil_ ba yake shaida mata zuwa anjima zai zo suyi maganar shirye-shiryen da za tayi na auren tunda gaba d'aya bikin yanzu ya rage saura kwana bakwai don har anci sati d'aya daga cikin ranakun auren da aka saka. "Assalamu alaikum!" Da mugun gudu Sarah ta fito jin kamar muryan Muniba. "Munibaaaaaaaaaa!" Ta fad'i sunanta da k'arfi cike da farin ciki ta rungumeta tana fad'in, "Wayyooooo Allah na, Muniba kece? Zo mu shiga daga ciki." Ta kama hannunta suka shiga cikin d'aki. Sakin labule Aina'u tayi, don tun jin sallamar Muniban ta d'aga labulen d'akin Lami tana kallon su. Dogon tsaki taja tare da fad'in, "Duk ku gama zumud'inku, wallahi wannan aure ba mai yuwuwa bane. Bamu y'an iska marasa sanin darajar kai irin y'an uwan mahaifin _Khalil_ d'in ma, ace a tura maku irin wannan sak'o amma baza ku tashi kuyi bincike tare da d'aukar mataki ba. Y'an iska kawai!" Duk a zuciya tayi maganar tare da shigewa tana mai yin kwafa tare da fad'in, "Ina da shiri a k'asa mai zafi, duk sai kunci ubanku." "Ke kuma dawa kike kwafa?" Fad'in Lami. A zafafe tace, "Babu ruwanki dani. Tom!" Tana gama fad'in haka ta zari gyale tare da ficewa daga gidan. "K'awata nayi kewarki. Ya aka yi su Baba suka bari kika zo gidan nan?" Sarah ta fad'i bayan ta bud'e d'an k'aramin fridge d'in dake d'akin ta d'auko mata ruwan sanyi da exotic. "Masha Allah! Haka kuka yi gyara a gidan? Wuri yayi kyau. Wannan irin makeken gado haka!" Ta fad'i hakan tare da hawa kan gadon tana shafawa. "It's a long story Munee, naji dad'i da Baba yaje yayiwa babanku magana don wallahi ke kad'ai ce k'awata a duniya gashi kuma d'azu muka gama waya dashi akan zai zo ya sallami k'awayen amarya." Saukowa Munee tayi tare da fad'in, "K'awata wa kika kamo haka? Kwanaki nake ta jin rumours wai kin yi cikin Shege Farouq ya fasa auranki. Ni ina jin maganar ta shiga kunnan hagu ta fita ta dama. Kuma kin san wake fad'awa mutane? Aina'u fa!" Tab'e baki Sarah tayi tare da fad'in, "Uhm, kyaleta. Kin san su suna goyon bayan Lami ne, basu son inyi aure. Ni kuwa zaman mai zan yi a gidan. Ai gwara na tafi nawa gidan nayi bautar ubangiji." Hannu Munee ta bawa Sarah suka kashe sannan tace, "K'awata kenan! To shi angon naki a ina yake." Gyara zama Sarah tayi ta d'an bata labarin in brief saboda ciki ba don abinci kawai aka yisa ba, duk da kuwa ta yarda da Muneeban. "K'awata na taya ki murna wallahi. Allah ubangiji ya sa mijinki ne ya kuma baku zaman lafiya mai d'orewa." "Ameen k'awar arziki." Daga nan suka fad'a hirar yaushe gamo har har lokacin da _Khalil_ yayi kiran Sarah a waya ya shaida mata yana waje. Tare suka fita da Muneeba zuwa wajen _Khalil_ d'in. Lokacin da Muneeba tayi arba da _Khalil_ rud'ewa tayi don b'ata tab'a hasaso haka yake ba. "Wannan itace k'awar tamu?" Fad'in _Khalil_ yana murmushi don tsabar rud'ewa Muneeba ta kasa gaishe shi har sai da Sarah ta d'an tsunguleta a cinya sannan ta dawo hayyacinta. "Kamar mai asibitin _Khalilullah specialist hospital_ ko? Ka tab'a duba ni sau d'aya a asibitin ka." Dariya yayi tare da fad'in, "K'aninsa ne, ba shi bane." Ya k'arisa maganar yana mai kashewa Sarah idanu. Dariya Sarah tayi tana kallon Muneeba dake masa anya kuwa. "Gaskiya kamannin sun b'aci. Kai ne mijin k'awar tawa kenan?" "In Sha Allah!" _Khalil_ yayi saurin fad'in. "Ma sha Allah! To bud'e kunnuwanka da kyau zan baka amana." Hannu biyu _Khalil_ ya saka ya rik'e kunnuwan nasa tare da fad'in, "Ina jinki k'anwarmu." Dariya Sarah ta kwashe dashi ganin yanda yayi tare da bada full attention d'insa wa Muneeba. "Wannan k'awata ce kuma aminiyata. A yau karo ba farko ina mai damk'a amanarta a hannunka, kar inji ko a cikin mafarkina tana kuka, idan ma za tayi, to ya kasance na farin ciki. Sannan a rik'a lallab'ata kamar kwai. Baka da matsala in dai aka zo fannin biyayya, don k'awata akwai biyayya kuma na tabbata za tayi maka biyayya. Yi, nayi, bari, na bari. Duk zata kiyaye su. Kai ne