Sashe 62
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
*_MATAR SAYYADEE_*
*Paid book 08128755583*
🦜 *KANWAR MATATA* 🦜
*24*
Wani irin yunƙurowa Sarah tayi zata fizge jikinta tana faɗin, "Happiness ana buga ƙofa." Da hannunsa ya maida ita tare da yin kamar bai ji abunda take cewa ba ya cigaba da birkita tunaninta da salonsa, tuni ta manta da wani bugun ƙofa da ake yi. Aina'u kuwa jin babu alamun za'a buɗe Ƙofar kuma ta tabbatar ana ji, sai wani baƙin ciki ya tokare mata wuya ta cigaba bugun ƙofar da dukkan ƙarfinta. Khalil kuwa bai sararawa Sarah ba sai da ya samu nutsuwa tukun, lokacin har Aina'u ta gaji ta zauna a bakin ƙofar tare da haɗe kai da guiwa. Khalil kuwa sunkutar matarsa yayi tare da shiga bayi suka yi wanka sannan suka dawo suka kwanta ya ƙara masu gudun ac tare ja masu barko ya rungume abarsa suka yi bacci. Aina'u taci kuka kamar ranta zai fita, ba ita ta bar ƙofar ɗakin nan ba sai da taji kiran sallar farko sannan ta koma ɗakinta ta faɗa kan gado tare da rushewa da kuka. Da asubah Khalil ya tashi ya shiga bayi ya ɗaura alwala sannan ya fito ya tada Sarah sannan ya wuce masallaci. Kasancewar ranar asabar ce babu aiki, tun da ya haura sama suka koma bacci shi da matarsa, basu suka sauko ƙasa ba sai sha biyu. Aina'u kuwa ta leƙo yafi sau ba adadin domin ganin ko sun sauko ƙasan amma wayam sai ta gaji har bacci ya ɗauke ta kasancewar bata samu bacci ba. Kitchen ya shiga ya ɗauko mata can fanta ɗinta mai sanyi tare cupcake ya bata kasancewar ta ɗan fara iya cin cake ɗin. Bayan ta gama cin cake da fanta ɗin sai tayi matashi da cinyarsa tare da cire hular kanta shi kuma ya soma warware all back ɗin da Aunty Maryam tayi mata guda goma saboda ya fara tsufa, "Mine, idan mace kika haifa ko, sunanki zan mayar, idan kuma namiji ne...." Tun kamun ya kai ƙarshe tayi saurin faɗin, "Sunanka zaka mayar." Murmushi yayi tare da faɗin, "Mai yasa kika ce haka?" Juyo da kanta tayi tana facing ɗinsa tare da faɗin, "Saboda soyayyar da nake maka ne." Hancinta yaja tare da faɗin, "Nima haka love." Dai-dai nan Aina'u ta leƙo, hango Sarah kwance a kan cinyar Khalil yana yi mata tsifa suna hira cike da nishaɗi, sai taji kamar ta zazzagawa kanta petur ta cinnawa kanta ashana ta babbake. Komawa tayi cikin ɗakinta tana saƙe-saƙen abunda zata ɓullo dashi nan gaba. Tun daga wannan rana Aina'u bata ƙara gigin zuwa buga masu ƙofa ba, sai ta tsiri zama a side ɗin Hajiya da zaran ta tashi daga bacci, bata kuma dawowa side ɗin Sarah sai isha'i. Cikin ƙanƙanin lokaci Aina'u tayi wani irin mugun shiga jikin Hajiya. Sosai Hajiya ta sakar mata ganin yanda take yi mata biyayya don har wanki yi mata take yi duk da kuwa akwai mai wanki a gidan. Tun Sarah na mamakin shaƙuwar Hajiya da Aina'un har ta daina. Babu yanda za ayi Hajiya tayi magana ɗaya biyu bata sako sunan Aina'u ba. Laure baiwar Allah kuwa, tun da Aina'u ta dawo part ɗin hajiyan ta saka ta gaba da harara da baƙaƙen maganganu. A gaban Hajiya kuwa sai ta riƙa janta a jiki, ko aiki Hajiya ta saka lauren, sai tayi saurin tashi tayi tana mai faɗin, "Laure huta, ai wuni kike kina aiki." Laure dai sakin baki kawai take yi tana kallonta. "Ummin Moon, wallahi yarinyar nan ƙanwar matar Khalil da take shishshigewa Hajiya, sam bata yi min ba, kama take min da criminal. Akwai alamun rashin gaskiya a ɗabi'un ta. Baki lura da wani abu ba? Tsoro na take ji, duk lokacin na shiga side ɗin Hajiya da sauri take fita bata kuma dawowa har sai na bar ɗakin. Don Allah ki saka mata idanu kina kallon moves ɗinta kar taje ta cutar da Hajiya." Ajiyar zuciya Aunty Maryam ta sauke tare da faɗin, "Wallahi ka riga ni a fili ni kuma na riga ka a zuciya. Laure ta kawo min ƙorafi ba sai ɗaya ba tasha zaginta tana faɗa mata baƙaƙen maganganu, tabi ta kanannaɗe Hajiya ta shiga zuciyata sosai ta yanda baza ta yarda da duk abubuwan da zata aikata idan dai ba hujja ta gani mai ƙarfi ba." Girgiza kai yayi tare da yin kwafa. Bayan kwana uku, gaba ɗaya su Aunty Maryam suna zaune har da Sarah a parlourn hajiya, babu wanda ya lura da Aina'u lokacin da ta zare jikinta ta shiga ɗakin Hajiya. Bayan kwana biyu Hajiya ta tara su tana cigiyar gwala-gwalanta na kusan kimanin 175milions, kowa hankalinsa ya tashi har da Aina'u data zaro idanu tare da dafe ƙirji. Anan dai kowa yayi ta jimami yana tunanin wa zai sace, Aunty Maryam ta kalli Hajiya tare da faɗin, "Hajiya ko dai kin canza masu wajen ɓoyone kika mance?" "Maryamu ban taɓa canza masu wajen ɓoyo ba, duk wanda da ɗauki wannan abu yana sane dashi." Faɗin Hajiya. Karaf Aina'u tace, "Kuma Hajiya kin binciki Laure da kyau? Don naga kaf gudan nan ita kaɗai ke shiga ɗakinki kai tsaye." Da sauri Laure, Aunty Maryam har da Sarah suka kalli Aina'un jin furucinta, "Hajiya shekaru bakwai muna tare, idan ina da wannan hali na ɗauke-ɗauke da kin daɗe da sani tun tuni. Wallahi tun da uwata ta haife ni ban taɓa ɗaukar abun wani ba" faɗin Laure tana mai fashewa da kuka. "A ko wani irin lokaci ɗan adam ka iya canzawa Laure." Faɗin Aina'u tana hararen Lauren. "Ke Aina'u!" Faɗin Sarah a tsawace da sauri Hajiya ta ɗagawa Sarah hannu tare da faɗin, "Bana son in ƙara jin komai daga bakin kowa, ku tashi ku tafi ɗakunan ku. Sarƙa kuma zasu fito domin duk wanda ya ɗauka ba dai ya sayar ba, don duk inda yake sai an kama shi ko kama ta." Gaba ɗaya kowa ya tashi guiwa sage ya bar ɗakin. Suna shiga ɗaki Sarah ta ɗaga hannu ta wanke fuskan Aina'u da mari tare da faɗin, "Wallahi baki isa ki kashe min aure ba, kina hauka ne? Ko baki san Laure ƴar uwarsu bace da har zaki jefeta da wannan mummunar ƙazafin? To bari kiji, ba zan iya da iskancinki ba, ki shiga ɗaki ki tattaro duk wani abu naki kizo ki wuce gida, ina zaune cikin rufin asirina kizo ki tada min hankali, to ba zai yiwu ba. Dama ba wani uban abun kike tsinana min ba, maza tattaro kayanki ga kuɗin mota ki bar min gidana." Hannu akan fuska Aina'u tace, "Ni kika mara Saratu har kina faɗin in bar maki gidanki? To zan tafi, amma sai kinyi nadama mafi muni a rayuwarki! Baki san true colour ɗina ba, amma zan fito maki dashi. Ba dai miji kike taƙama dashi ba, mu zuba mu gani, gaki ga mijin nan." Tana gama faɗin haka ta shige cikin ɗayan parlour ɗin da zai sadata da ɗakinta. Jakarta ta kinkimo ta fito bayan ta canza kaya ta shafa aboniki a idanunta, nan da nan idanunwan suka kaɗa su kai jazur kamar taci kuka ta ƙoshi. Bata taras da Sarah a parlourn ba, sai kawai ta saka kai ta fita daga ɗakin. Sai da ta ajiye akwatinta sannan ta buɗe ta ɗauki wani abu cikin wani ƙatoton box tare da nufa side ɗin Hajiya, Laure ta taras a parlour sai da ta dungure mata kai sannan ta wuce bedroom ɗin Hajiya tare yin knocking haɗe da sallama. Daga ciki Hajiya ta bada izinin shiga, tura ƙofar tayi tare da zama a ƙasa tana kallon tiles ɗin dake shimfiɗe, Hajiya dake tsakiyar gado tana duba wasu kaya ta kalleta tare da faɗin, "Aina'u lafiya?" Kuka Aina'u ta fashe dashi tare da faɗin, "Hajiya kiyi haƙuri, amma yanda kika ɗauke kika riƙe ni tamkar ƴarki ya saka ba zan iya bari a haɗa baki dani a cuceki ba, ga sarƙan ki, Saratu ce ta sace tare da haɗin bakin ƴar aikinki Laure.........."
_Dan Allah kuyi haƙuri bana jin daɗi ne shiyasa kuka jini shuru. Yanzu ma cewa nayi bari nayi naku ko kaɗan ne yafi babu_