Sashe 19
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 7 min read
mata ko uffan ba har suka isa k'ofar gidansu Sarah. Parking yayi tare da kashe motar ya juyo ya tsura mata idanu. Tana jin idanunsa na yawo a jikinta amma tak'i kallon wajen. Ledan maganin ya d'auko tare da fiddo da magungunan ciki sannan yace, "Hey, kalle ni nan." Kamar baza ta juyo ba, sai kuma ta juyo ta kallesa tana mai turo baki gaba. Tsurawa kyakkwar bakinta kallo yayi yana tuno ranar da tsautsayin ya afka. "Kin san wani abu? Tsiwarki ita ke ja mutun yayi maki abunda bai yi niyya ba. Ko wancen ranar ke kika ingiza ni har mai afkuwa ta afku. Idan kika b'ata rai ko kuma kika turo baki, wani irin kyawu kike k'ara yi sosai. Sai ki rik'a looking very sexy!" Wani irin kuka Sarah ta fashe dashi jin abunda yace. Bak'in ciki take ji idan yana maganar cikin dake jikinta. "Kin san Allah idan kina kukan nan, wancen ranar ba'ayi na gaske ba, amma ina ganin soon an kuwa zuwa wajen." Hannu ta kai zata bud'e k'ofar taji sa a gark'ame. Kallonsa tayi tare da shagwab'e fuska tace, "Dan girman Allah ka bud'e min, kaji ma kiran sallah ake yi!" Kallon maganin da ta fito dashi yayi tare da fad'in, "Kalli nan, wad'annan guda ukun kullum sau d'aya zaki rik'a sha, wannan kuma safe da dare. Allah ya k'ara maki lafiya Matata. Kiyi min magana da Mama idan kin shiga ciki. And lastly, wallahi kar in k'ara kiranki a waya kik'i d'agawa. Don wallahi komai dare sai nazo, kuma ni kai na ban san mai zai faru ba idan nazo d'in." Yana gama fad'in haka ya cire lock d'in yana kallon fuskanta. Bud'e motar tayi ta fita a hankali ba tare da ta d'auki ledar ba, sai da ta rufe k'ofar sannan ta lek'o ta window kasancewar ya zuge glass d'in tare da fad'in, "Ba zan d'auka ba, dan girman Allah kar ka fasa abunda kace za kayi. Kuma bazan sha maganin ba. Ka tafi da tsiyarka. Kuma cikinka dake jikina, a leda zan juye na watso maka shi a fuska na huta da jaraba." Da wani irin hanzari ya cafki hijjab d'inta ya cukuikuyota da hannu d'aya tare da fad'in, "Maimaita mai kika ce?" A gigice tace, "Na rantse cewa nay na manta ga ledan maganin nan baka mik'o min ba. Kuma wancen farin ma ya ma kace ayi amfani dashi." Dariya ce ta taho masa sosai amma bai yi sai murmushi ya saki tare sa d'aukar maganin da d'aya hannunsa ya mik'a mata. Da sauri ta amsa har da fad'in, "Nagode" shi kuma ya saki hijjab d'in nata tayi saurin barin wajen ta nufi k'ofar gidansu ba tare da ta waiga ba. Tana bud'e k'ofar suka ci karo da Baba ya fito karo na bakwai ko Allah zai sa ya ganta. Don lokacin dasu Na'ima suka baje a tsakar gida babu labarin da suke yi sai na _Khalil_ da irin motar da yazo da ita. Jin hakan sai ya tada hankalin Baba ya soma tunanin ko Sarah ta soma hawa layin y'an uwanta ne. Ya jira kusan mintuna ashirin ko Sarah zata dawo amma yaji shuru, ya daure ya k'ara goma akai, ganin har lokacin shuru sai ya mik'e ya d'auki sandarsa ya fito waje amma wayam. Yana jin sanda su Na'ima suke dariyar ya fita nemo y'ar gwal. "Baba dama dawowa kayi kar ka wahalar da kanka. Don saurayinta yazo sun fita tare." Fad'in Hassana. Bini-bini Baba ke fitowa ya duba ko Sarah ta dawo amma wayam. Sai a karo na bakwai sannan ta turo k'ofar suka yi ido hud'u. Wani ajiyar zuciya Baba ya sauke tare da fad'in, "Saratuuu!" Sai kuma ya fashe da kuka. Da sauri Sarah ta waiga taga motar _Khalil_ na nan, sai taji hankalinta ya tashi don bata son yardar da Baba yayi mata ya rushe. A gigice ta soma magana, "Wallahi Baba ba abunda kake tunani bane. Dan Allah ka daina kuka." Ta fad'i tana mai fashewa da kukan. Da sauri _Khalil_ ya bud'e mota ya fito tare da k'arisowa wajen ya duk'a tare da fad'in, "Ina wuni Baba?" Baba dake matsar hawaye ya d'ago ido ya kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Bawan Allah na rok'e ka da girman ubangijin idan ba alkhairi bane ya kawo ka wajen Saratu kayi tafiyarka Allah ya had'a ka da dai-dai da kai. Ka dubi Allah da annabi kar ka lalata min tarbiyan y'ata guda d'aya da ta fita zakka!" Shuru _Khalil_ yayi na y'an dak'ik'u tare da fad'in, "Baba wallahi alkhairi ne ya kawo ni wajen 'yarka ba sharri ba. Ni da niyyar aure nazo k'ofar gidan nan ba da niyyar yaudara ba." Da sauri Sarah ta kalli Baba tare da fad'in, "Baba kar ka yarda da maganarsa, fatar bakinsa ne fad'i amma cikin zuciyarsa ba haka bane. Shine sanadiyar duk abunda ke faruwa dani yanzu. Shine dalilin rugujewar farin cikina. Shine dalilin fasuwar aure na. Baba wannan dake durk'ushe a gabanka shine uban cikin dake jikina." Ta k'arisa maganar tare da fashewa da kuka. Baba kuwa ji yayi kamar an d'iga masa dalma a kunne. Rintse idanu yayi cike da k'una a zuciya yace, "Bawan Allah mai muka maka? Mai d'iyata tayi maka ka tarwatsa mata rayuwa? Kana ganin kayi min adalci kenan? Ban tab'a b'ata d'iyar wani ba, wannan jarabawace kawai daga mahalicci!" Idanun _Khalil_ gaba d'aya sun kad'a kun yi jazur ya d'ago tare da kallon Baba yace, "Baba, dan alfarmar ubangiji halittu ka saurare ni ko da na mintuna biyar kacal. Wallahi, tallahi rantsuwar musulmi ban zo nan da niyyar cutar kowa ba, zuwa na nan k'ofar gidan nazo ne domin in auri 'yarka." Hakanan baba ya d'an ji _Khalil_ ya kwanta masa. Kallon Khalil d'in yayi tare da fad'in, "Shiga masallaci kayi sallah, idan an idar kayi sallama zan aiko Saratu ta shigo da kai har ciki. Bari na shiga nima nayi sallar." Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar _Khalil_, cike da ladabi yace, "Nagode Baba!" Ya fad'i hakane tare da mik'ewa ya nufi masallacin gaban gidansu Sarah wanda yake daga hannun hagu, yayin da nasu gidan yake daga dama. Baba ma shigewa yayi Sarah na biye dashi kanta a k'asa hannunta rik'e da ledar magungunan da _Khalil_ ya bata. Gaba d'aya suna tsakar gida har da y'ay'ansu. Rabo d'an wajen Na'ima ya kalli Sarah tare da fad'in, "Lami ga Saratun ta dawo daga wajen saurayin nata." A fusace Sarah tace, "Daga wajen ubanka na dawo." Na'ima mahaifiyarsa ta taso a fusace tare da fad'in, "Zan ci ubanki a cikin gidan nan wallahi idan kika ce zaki rik'a takurawa d'ana. Babu ruwana da cikine a jikinki duka zan maki." Harararta Sarah tayi tare da fad'in, "To ai sai ki kashe ni kawai. Banza kawai." Yunk'urawa Na'ima tayi zata taho wajen Sarah karaf Lami ta rik'e ta tare da fad'in, "Barta! Yanzu haka duk salon kar ta bamu abunda ta samo ne daga hannun saurayin nata." Juyowa Baba yayi tare da kallon Sarah yace, "Saratu wuce ciki kinj." Babu musu Sarah ta shige ciki. "Ban gane abunda kake nufi ba Nuhu anyi yamma da kare!" Ko kallonta Baba bai yi ba ya shige d'aki. "Ahafff! Ba na fad'a maki ba Lami. Baba fa ya san duk tsiyar da Sarah take shukawa. Raba kud'in suke yi a tsakanin su shiyasa kike ganin yafi sonta akan mu gaba d'aya." Fad'in Aina'u. "Na ko tabbatar da maganarki yanzu Aina'u. Aikuwa dani suke zancen." Fad'in Lami tana kwafa. Dai-dai nan Sarah ta kuma fitowa ta nufi fanfo Lami na harararta. Alwala da d'auro sannan ta kuma komawa d'aki. Tana idar da sallah ta jiyo muryan Baba yana kwad'a kiran sunanta. Da sauri ta fito ta nufi baranda inda ta ganshi tsaye a bakin k'ofar d'akinsa, "Yi maza gashi can yana kwad'a sallama, je shigo dashi." Da "To Baba" Sarah ta masa tare da juyawa. Na'ima kuwa kallon Hassana tayi wacce itama kallon nata take yi sannan gaba d'aya suka mai da dubansu ga Lami wacce tayi suman tsaye tana kallon Baba cike da mamaki. Mintuna biyu sai ga Sarah tafe, _Khalil_ biye da ita a baya. Bai kalli kowa a cikinsu ba, don har yanzu bai gama tabbatar da cewar Lami ita ce cikakkiyar mahaifiyarsu Sarah ba. Dama kuma tuni baba ya shige cikin d'aki. Sallama _Khalil_ yayi tare da shiga don tuni baba ya amsa tare da bashi damar shiga. Yana shiga Sarah ta bar wajen zata wuce d'aki Lami ta shak'o ta tare da fad'in, "Dan ubanki shine zaki kai sa wajen mahaifinku! Wato kin fi k'aunarsa dani ko? To wallahi baku isa ba komai dani za'a ci." Tana gama fad'in haka ta fad'a d'akin babu sallama lokacin _Khalil_ suna k'ara gaisawa da Baba. "Na rantse da, girman Allah Nuhu baka isa Kaci kud'in nan kai d'aya ba. Ai nice na d'auki cikin Sarah wata har tara na kuma sha wuya nayi nak'uda na haife ta. Fito da duk wani abu da yaron nan ya baka ayi kaso." Sai kuma ta mayar da dubanta ga _Khalil_ wanda kansa ke a k'asa tare da fad'in, "Kai kuma Munafuki................