Sashe 81
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 2 min read
sallamar su aka yi wani gagarumin taron sunan twins, _Sam'an_ da _Sauban_. Irin kyaututtukan da Sarah ta samu faɗi ɓata baki, a gaban idanun Aina'u akai komai, don ta samu sassaucin azabar, sai jinya jikinta da take yi yanzu, tayi wani irin rama da baƙi, haushi da tsanar kowa take yi a gidan, hotunan Khalilullah dake wayanta kawai take kallo taji sanyi azuciya. Khalil ya maida komai nasa da sunan Sam'an da Sauban, wani irin mahaukacin soyayya yake gwadawa Sarah da ƴaƴanta. Khalil ya bawa su Na'ima miliyan biyu-biyu kowaccen su har da Lami, sannan ya saya masu wani four bedroom flat a Jama'a road, tare da saka dukkansu a islamiyya kuma Alhamdulillah duk sun fara zuwa kuma natsuwa ta soma shiga jikinsu. Hajiya damuwarta ɗaya, ta rasa abunda ke mata daɗi a duniya, wani irin abu take ji ya tsaya mata a zuciya amma ta rasa menene wannan abun, sai ta zauna shuru tana tunani, duk tabi ta rame ita da ya Abdul-Hakeem. Kuma har yanzu ta kasa tambayarsa akan matarsa da kuma zaman gida da yake yi babu aiki. Aina'u kuwa ta warke garas, sai dai tsafinta ba zai taɓa ƙara amfani ba sai nan da shekara ɗaya, haka Hell ya faɗa mata. Baiwar Allah Sarah kuwa, yanzu bata da damuwar komai, ta warke garas kamar bata taɓa ciwo ba, tun da ta haihu bata ƙara ganin tsutsotsin nan ko guda ɗaya daga jikinta ba, sannan wannan warin da mijinta yake yi mata duk babu. Wani irin soyayya suke shimfiɗawa wanda ko lokacin da take amarya basu yi ba. Twins sun shiga wata shidda da haihuwa, yara tubarkalla don har tsayuwa suna yi idan suka kama abu, kamanninsu ya ƙara fitowa sosai da Khalil, ga wayau. Sun san Laure sosai don itace mai taya Sarah raino, amma kuma abunda ke matukar bawa Sarah mamaki shine, ko muryan Aina'u suka ji gaba ɗaya rikicewa suke yi suna kuka, Sam'an shi har wani kakkafewa yake yi..........