← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 112

Sashe 67

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalil har sai da yayi wani muguwar faɗuwa saboda yanda ya duro daga kan gadon tsabar rikicewa don duk a tunaninsa faɗuwa Sarah tayi a toilet ɗin. Burum ya faɗa bayin yana ware idanunsa, ganinta yayi ita bata duƙa gaba ɗaya ba kuma ita bata miƙe ba, ƙafafunta sai rawa suke yi, "Laf......." Bai ƙarisa cewa lafiyan ba ya waro idanu yana faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Sarah menene wannan haka? Daga ina suke fitowa?" Ya faɗi yana mai ɗage skirt ɗinta sama sosai. Da sauri ya mayar ya sauke gabansa na bugawa saboda yanda yaga tsutsar na fitowa da gudu kamar fitar jini, wasu ma a dunƙule suke fitowan. "Na shiga uku na, Wayyo Allah shikenan mutuwata ce tazo ta haka!" Faɗin Sarah tana mai ɗaura hannu a kai. Janyota jikinsa yayi tare da faɗin, "Haba mine, sai kace ba musulma ba! Menene na ihun da faɗin irin wannan maganar? Idan kika mutu ni kuma inyi yaya? Bafa wani abu bane na tashin hankali, da yawan mata suna samun irin wannan matsalar. Ki kwantar da hankalinki Allah zai warkar dake cikin ƙanƙanin lokaci zaki ce na faɗa maki. Kuma ma kin manta mijinki likita ne?" Ya faɗi hakan yana sakar mata murmushin tare da ɗaukar ƙatuwar butarsu ya taro ruwan zafi sannan ya dawo inda take tana kuka ya duƙar da ita tare da saka hannunsa ba tare da ko ɗigon kyama ba ya dunga wanko tsutsotsin nan suna zuba a ƙasa. Sarah kuwa ganin yanda jajayan mitsi-mitsin tsutsotsin ke zubowa yayin da Khalil ke wanko su dai ta daɗa rikicewa tana kuka sosai tare da damƙe kafaɗunsa. Sai da yaga tsutsotsin sun daina fitowa sannan yayi mata wanka tare da ɗaukota ya dawo da ita kan gadon don har wani mummunar zazzaɓi ya saukar mata. Ya juya zai sauka daga kan gadon domin wanke bayin don tsutsotsin na nan a ƙasa da uban yawa, caraf ta riƙe hannunsa tare da faɗin, "Doctor meke damuna? Zan warke kuwa? Meke kawo tsutsotsi a gaban mace?" Dariya da wani irin mugun tausayinta ne ya rufe shi jin sunan data kirasa dashi da kuma irin tambayoyin data jero masa, zama yayi bakin gadon tare da janyota jikinsa gaba ɗaya ya rungume tare da faɗin, "Ki kwantar da hankalinki Sarah, nace maki wannan ba wani abu bane, ko wata biyu baya da suka wuce naga irin wannan same problem ɗinnan ga wata tsohuwa. Hakan na iya faruwa when Scratching the anus or vagina, or wiping them after going to the toilet. This can cause the eggs to stick to your fingertips or under your fingernails. If you don't wash your hands, the eggs can be transferred to your mouth or on to food or objects, such as toys and kitchen utensils. Amma akwai maganinsa kuma zaki warke in Sha Allah." Sarah dai jinsa kawai take yi amma bata cikin duniyar da yake ciki, ta jima da tsundumawa kogin tunani da tashin hankali. Addu'a ya shiga tofa mata ganin yanda take zabura har bacci ya ɗauketa sannan ya shimfiɗar da ita ya koma cikin bayin, sai da ya saka handglove ya ɗibi tsutsotsin ya saka a wani container sannan ya wanke bayin tass yayi wanka. Yana ƙoƙarin saka riga ya soma jin ƙarar door bell babu ƙaƙƙautawa, da sauri ya ƙarisa saka t-shirt ɗin ya fito daga ɗakin ba tare da ya lura da zaburar da Sarah tayi ba. Da uku-uku yake tsallake steps ɗin har ya isa ƙofar ɗaki ya buɗe Ƙofar, da Aunty Maryam yaci karo hankalinta a tashe tana kuka, "Lafiya Aunty Maryam, meke faruwa ne?" Da hannu Aunty Maryam tayi masa nuni da side ɗin Hajiya tana faɗin, "Khalil, Laure! Laure ce ke ta aman jini guda-guda, kuma maganarta ya ɗauke." Wani waro idanu yayi tare da faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Ya faɗi hakane tare da nufar side Hajiya da saurinsa, yana zuwa ya kuma taras da gigitacen tashin hankali, "Hajiya tayi wani irin mugun kumbura kamar fulawar da aka kwaɓa da fulawa, wuyarta yayi wani abu kamar mai maƙoƙo ya kuma zazzago, haka ma idanunta, naman ƙasan ya zazzago, babu abunda take yi sai jujjuya kai tana hawaye don ita kaɗai ta san azabar da take ciki. "Maryam ina wayarki, kira mijinki yanzun nan yazo, kira shi nace maki" Khalil ya ƙarisa maganar a tsawace. Aunty Maryam da gudu ta fita zuwa ɓangarenta don a can ta bar wayan jikin caji. Khalil sai ya rasa inda zai saka kansa, ga Laure a gefensa na aman jini tana ƙoƙarin yi masa magana amma babu murya, ga kuma Hajiya na malelekuwa a jikinsa kasancewar ya rungumeta sai kiran sunansa take yi tana faɗin ya taimaka ya cire mata ciwon dake jikinta. A can ɗaki kuwa bayan fitar Khalil Sarah ta fara kwararo uban aman jajayan mitsi-mitsin tsutsotsin nan ta baki ta hanci, ga wani uban tusosi da take saki kamar an buɗe masai tsabar wari, gaba ɗaya ta ɗume ɗakin da wari ga kuma tsutsotsi ko ta ina, gadon gaba ɗaya ya zama abun kyama. Sarah ta suma fiye da sau biyar tana farfaɗowa. Cikin abinda bai wuce mintuna sha biyar ba sai ga Ya Abdul-Hakeem a kan bike don gani yayi idan yace zai yi driving lokaci zai ɓata da yawa, ko kamun ya iso Laure ta fita daga hayyacinta ko motsi bata yi, Hajiya kuma cikin hukuncin ubangiji kumburin jikin da kansa ya saɓe amma kuma sai ta dawo kamar ƴar yarinya sannan zazzagowar da idanunta yayi yana nan da wannan abun da ya fito mata a wuya kamar maƙoƙo. Cak Khalil ya ɗauki Hajiya kamar yarinya ya sakata a bayan mota, ya Abdul-Hakeem kuma ya cicciɓo Laure wacce bata da maraba da gawa.. Khalil wajen Aunty Maryam ya nufa tare da faɗin, "Maman Moon dan Allah ki duba min Sarah a ɗaki itama bata da lafiya sosai." Jinjina kai tayi tare da faɗin, "Babu matsala Khalil, Allah ya basu lafiya dukansu." Da "Ameen" ya amsa tare da saurin shiga cikin motar ya Abdul-Hakeem yaja motar suka bar gidan. Suna fita Aunty Maryam ta nufi ɗakin Sarah domin dubata, tunda Sarah tazo gidan bata taɓa shigar mata ko ɗayan parlourn ƙasa ba bare kuma bedroom, yanzu haka ma sai da tayi tsaam kamun ta haura sama, tun daga last step take jin wani irin unbearable wari mai tada zuciya, nan da nan wani irin miyau ya soma taruwa a bakinta dama kuma ita sam bata shiri da wari, bama ita ba, gani take gaba ɗaya zuri'arsu basa ƙaunar wari, haka ma zuri'ar mijinta (Kun san dai mutanan mai duguri wajen ƙamshi 🤪) musamman ma Khalil mai wanka da turare. Haka dai Aunty Maryam ta dunga ɗauke numfashi, don tana ƙara kusanta kanta da ɗakin Sarah, mahaukacin wari na ƙaruwa. Hannu ta saka ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga ɗakin, da mugun sauri ta dawo baya ta dafe ƙirji tare da faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allahumma arji'ini fi musibati!! La ila ha'illallahu Muhammadur Rasulullah, Allahumma la sahala illa maja'altahu sahala!!" Yanda ƙirjinta ke bugawa da sauri-sauri ka ce ƙararrawar mutuwa aka buga mata, sai kawai ta fashe da kuka tare da komawa ɗakin bayan ta saka hannu ta toshe hancinta. Babu abunda Sarah keyi sai miƙa mata hannu alamar ta ceceta, Aunty Maryam kuwa ta kasa ƙarisawa gareta saboda wasu uban tsutsotsin dake mamaye a kan gadon zuwa ƙasa da wuyanta saboda amansu da ta gama yi yanzu. "Sarah meke damunki? Inna lillahi! Wannan wani irin abu ne kuma?" Faɗin Aunty Maryam cikin kuka. "Aunty Maryam mutuwa zan yi!" Sarah ta faɗi tana mai sakin wani irin mahaukacin tusa mai mummunar warin fitar hayyaci tare da wani irin kakarin amai, sai ga aman tsutsotsin nan na fitowa da uban yawa daga bakin Sarah kamar zata mutu, "Wayyoo, wayyoooo Aunty Maryam, Wayyo Allah cikina." Da mugun gudu Aunty Maryam ta fita daga ɗakin don tabbas idan ta kuma minti ɗaya ita ce zata mutun ba Sarah ba, don irin warin da Sarah keyi ba mai misaltuwa bane, tsutsotsin nan banda ta gabanta har ta duburanta fita suke yi, ba suyi mata ƙaiƙayi kuma basu cizonta, amma kuma ganinsu kawai abun tsoro da tashin hankali ne mai girma. Aunty Maryam na fita wuce ɗakinta tana wani irin kukan tausayin halin da Sarah take yi, tunda uwarta ta haifeta bata taɓa ganin kalar wannan cutar ba. Wayarta ta cire daga caji sannan lalubo number ɗin Khalil ta danna masa kira, lokacin shi kuma suna can kan Laure suna ƙoƙarin ceto rayuwarta, sun samu sun tsayar da aman jinin, amma kuma maganarta ya ɗauke gaba ɗaya. Duk irin ihun da za'a yi, ƙarshe ma ko magana aka yi mata a kunne, bata jin komai. Kuma abunda yafi bawa likitoci mamaki, basu ga musabbabin faruwar haka ba. Hajiya kuma suger kawai suka gani sai kuma da kidney wanda Khalil ya san dasu, sai suka bar kumburin jikin Hajiya akan ciwon suger ɗin sanadi, ita kuma Laure babu taƙamaimai musabbabin ciwonta. Haka wayar Khalil dake silent yayi ta ringing yana yankewa. Cikin lokaci ƙanƙani Nafeesa autarsu Khalil, gata da tsohon ciki sai kuka take yi, lokacin da taga Hajiya da kuma yanda halittarta ya dawo, yanke jiki tayi ta suma tana farfaɗowa labour yace gani nazo, dama kuma ashe jiyan kwana tayi da ciwon mara, Kasancewar irin naƙudar Hajiyan suke yi, cikin mintuna talatin ta haifo ƴarta mace. Hankalin Nafeesa bai ɗan kwanta ba, sai da taga hajiyan ta ɗauki jaririyar da kanta tana yi mata addu'a, don Hajiyar bata jin komai a jikinta na ciwo sai damuwar halin da Laure take ciki, yarinya marainiya babu uwa babu uba, dangi sun watsar da ita bata nan bata can kamar wata mota. Da wannan ya karɓa ya gama mora, sai ya turawa wancen, an mayar da ita uwa jaka, dalilin hakane yasa da hajiya ta je Maiduguri bayan rasuwar mahaifinsu Khalil da shekara ɗaya sai ta ɗaukota. Da kakan Khalil da kakan Laure uwarsu ɗaya uba kowa da nashi. "Mu'azzam ka sallame ni na koma gida tunda ni jikina Alhamdulillah, ga kuma Nafeesa da ta samu ƙaruwa, tana buƙatar kulawa sosai kasan haihuwa ce ta fari, kuma daga nan idan mijinta ya amince gida muka yi, sannan kuma ina gargaɗinku da
Chapter 67 · 0% Book details