Sashe 43
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hajiya kina barci ne zaka kwaso maki dangin arna matsayin surukarki? D'iyar Elizabeth ce kuma Wallahi matan zumunta cike da gidan har da zancen zuwa wajen Pasto domin ayiwa ita matar _Khalil_ d'in wankan zunubi." "Wankan Zunubi?" Hajiya ta fad'i cike da mamaki tana kallon K'anwar tata Marwanatu. "Wallahi tallahi Hajiya kar ki yarda da wannan aure idan ba haka ba akwai mummunar matsala. Wannan wani irin bahagon gida ne haka." Fad'in Inna Marwanatu. Amma abunda ya matuk'ar d'aure mata kai da bata mamaki shine ganin hajiya tayi murmushi tare da cigaba da ware anko da take yi wanda ta sayawa y'an uwa da abokan arziki. "Hajiya dariya fa kika ki. Na fad'a maki irin wannan magana mai d'aga hankali shine kike murmushi mai makon ki fusata ki kira waya a fasa wannan aure." Ajiye kayan da ta d'auko tayi tare da kallon Marwa sannan tace, "To ai ni ban fahimceki bane Marwa. Shin laifin uwar ne zai shafi y'ar ko kuwa? Ba ita bace arniyar idan rrtkq a kina magana akan a fasa auren. Ko da kuwa itace, ai addininmu bai haramtana mana kawo su cikin mu, mu dai matsayin mata addini bai amince mana da mu zauna dasu ba. Kuma wannan yarinyar da _Khalil_ zai aura, bayan binciken da marmari yayi, na saka anyi min nawa da kai na a kanta. Don haka ita kad'ai zamu kawo cikin gidan nan ba ba mahaifiyarta ko kuma matan zumunta ba. Idan aka kawo ta cikin gidan kowa ga watse ai shikenan ko? Don Allah Marwa bana son in k'ara jin wannan maganar, ya tsaya tsakanin mu kawai." Da sauri Marwa tace, "Amma Hajiy....." "Dan girman Allah ki bar wannan maganar haka Marwanatu." Tsit Marwa tayi bata kuma cewa komai ba sai ma juyawa da tayi ta bar d'akin. Tana fita Hajiya ta jingina da gado tare da fad'awa duniyar tunani don fisabilillahi ta daure ne kawai a gaban Marwa ta kare surukar tata da gobe amma ba wai don bata firgita da labarin da taji ba. "To ko dai in d'auko yarinyar nan ne har sai anyi biki? To kuma ai ba'a tab'a haka ba a al'adar hausawa. Kai Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allah kana gani, kafi kowa sanin dalilin wannan had'i. Allah kasa alkhairi ne albarkacin soyayyar da kakewa fiyayyan halitta." A bayyane tayi magana tare da jan dogon ajiyar zuciya. "Baba, shawara zan baka, ka saka a kwaso duka kayan can na waje, idan ba haka ba wallahi duk yawon kayan can Sarah baza ta tafi da abun arziki ba." Na'ima ta fad'i ba tare da ta damu da kukan da ta iske baban nayi ba. D'agowa Baba yayi ya kalli Na'ima, bai tab'a d'auka za'a samu wacce zata iya wannan maganar hankalin a cikinsu Na'imar ba. "Na'ima kuje ku kwaso kayan tsaf ku kai gidan liman Muhammadu mahaifin k'awar Saratu. Ku kira yara su kwashe kayan zan biya kud'in." Da to Na'ima ta amsa tare da fita dama kamun tazo d'akin Baba ta saka su Nuratu sun saka idanunsu sosai a kai gudun y'an sibaren na ayye. Cikin abunda bai wuce mintuna ashirin ba, Na'ima ta had'a kan yaran anguwa da almajirai sun kwashe kayan tsaf an tafi dasu gidan mahaifin Muneeba. Lokacin Lami na d'aki ita da k'awayenta matan zumunta. Sai da ta fito domin d'ibar masu nasu kayan kamar yanda suka yi mata fanfo, sai taga wayam duk da kuwa tana jin hayaniyar yara lokacin da suka zo tafiya da kayan, amma sai tayi tunanin ko y'an ganin kaya ne. Da masifa ta hau tambaya ina kayan. "Suna gidan k'awar Saratu. Can Baba yace a kai sabida yawan mutanen da suke shigowa gudun sata." Fad'in Na'ima. "Kutumar kaza-kazan can......... To wallahi ku fita ku dawo da kayan nan yanzu. Uwar wani ce ta haifar min y'ar da har za'a ce an kai kayan y'ata wani gidan. Wallahi ba liman ba ko sarkin makka ne sai naci kaza-kazansa (Ta wulwulo zagi) idan bai saka an maido mi da kaya y'ata ba." Fad'in Lami. Baba dake d'aki ya kai wuya, bai san lokacin da ya fito daga d'aki ba tare da fad'in, "Lami, na gaji da halinki. Wallahi tallahi idan kika k'ara magana akan wannan kayan sai na sake ki. Haba! Kin takura min kin hana ni shan iskan duniya cikin salama. Kuma wallahi idan y'an iskan k'awayenki basu fito sun bar gidan nan ba, sai na masu itace. Idan kuma sun ce k'arya ne, su k'ara mintuna biyar suga abunda zai faru." Matan zumunta na jin haka suka fara fitowa d'aya bayan d'aya. "Ku koma, babu inda za kuje. Wallahi dai-dai nake da kai Nuhu a cikin gidan nan. Idan ka fasa saki na, Allah ya tsine maka albarka. Kuma kaya sai an dawo dasu gidan nan." A zuciye Baba yace, "Kije na sake ki saki d'aya, bi........" Da wani irin mahaukacin gudu Sarah ta fito tare da jan burki ta kifa guiwarta a k'asa tare da fashewa da kuka tana fad'in, "Kar ka k'arisa, kar ka k'arisa Baba dan girman Ubangiji. Wallahi in har ka saki mama akan kayan akwati na, ba zan tab'a yin auren ba na fasa. Dan girman Allah ba dan halin Lami ba Baba ka mayar da ita. Baba ina wannan hak'uri da ka dad'e kana yi ya tafi? Haba babanmu." Ta k'arisa maganar tana mai fashewa da kuka. "Na gaji ne, na gaji Saratu. Saratu nayi iya hak'urin da zan iya yi da mahaifiyarku. Ta tafi kawai ai tana da dangi." D'aya daga cikin matan zumunta ta soma fad'in, "Yesu almasihu kayi mana tsari da irin wannan mutanan da ka tsine masu." Zabura Baba yayi tare da rarumo wani narkekiyar langen ya rafka mata a tsakiyar baya, sauran kuma yayi kansu. Da gudu har da k'undunbala suka fice daga gidan. D'aya har tana sakin tusa. K'afafunta Baba Sarah ta rik'e tana fad'in, "Baba dan Allah kayi hak'uri ka mayar da Lami." Baba yace, "Kiyi hak'uri Sarah, zamana da Lami akwai cutarwa. Gwara kawai ta tafi." Wani irin kuka Lami ta fashe dashi tare da fad'in, "Azzalumi ka rabo ni da y'an uwana ka kawo ni nan kana cutar dani. Yesu ba zai tab'a yi maka albarka ba. Shiyasa sabida mugun halinka ya maka mummunar tsinuwa ka zama talaka. Kuma ko ka sake ni, ina nan gidan sai dai kai ka fita ka bar gidan." "Haba Lami, kukan me kike yi. Muje na kama maki d'aki ki zauna ki bar masa gidansa." Fad'in Aina'u tana hararar Baba. "Ban yi mamaki ba Aina'u. Banyi ba! Ai kina da abunda kike rabawa maza suna baki kud'i dole kice zaki kamawa mahaifiyar taki d'aki." Su Nuratu kuwa ko uffan basu ce ba. Na'ima kuwa kumbarta take yankewa yayin da Marfu'a ke wankewa yarinyar ta kashi bayan ta cire mata pampas. "Eh d'in. Da ace ka sauke duk wani hak'k'inmu dake kanka, ai baza mu kasance a yanda muke haka ba. Kai ne mugun daka cutar dam......" Ba tare da ta k'arisa ba Sarah ta sauke mata tagwayen maruka a fuska hagu da dama sai da tayi zaman y'an bori. Dama kuma kamar jira Ainau take ta rarumo wani sanda tayi kan Sarah dashi. Da sauri baba ya shiga tsakaninsu, Aina'u bata yi wata-wata ba ta saukewa Baba sandar a k'agu kasancewar ya d'aga hannu wajen k'ok'orin kare Sarah. "Wasssh Inna lillahi!" Baba ya furta hawayen azaba na sauko masa har kan kuncinsa. Wani irin fuzgewa Sarah tayi ta kai Aina'u k'asa ta hau kai mata wani irin duka ko ta ina a jikinta. Da kyar Lami da Na'ima suka d'aga Sarah a kan Aina'u wacce bakinta bai mutu ba sai auno ashar take yi marasa dad'in fad'e. "Ki kashe ta shegiya y'ar iska. Allah ya tsine maki albarka Sarah. Yesu ina rok'onka a yau ka hana Sarah kwanciyar hankali ita da Nuhu mahaifinta. Ba dai ubanki kika zab'a a kaina ba, to kije yesu ya tsine maki ke da ubanki. Ba dai ya sake ni ba." Ta k'arisa maganar tana mai jan kwafa. Wani irin kuka Sarah ta fashe dashi don ta san illar bakin uwa a wajen y'ay'anta. Da gudu ta k'ara kama k'afafun Baba tare da, fad'in, "Baba kayi min rai ka rufa min asiri kar bakin uwa ya kama ni ka mayar da Lami d'akinta. Dan Allah Baba. Wallahi idan baka mayar da Lami ba, ba zan tab'a zaman aure ba. Ko an d'aura auren sai na gudu na bar gari." D'agota Baba yayi tare da fad'in, "Share hawayenki Saratu. Bakin Lami ba zai tab'a kama ki ba don babu abunda kika yi mata. La'anarta kanta zai koma. Ki bar kuka, na mayar da ita d'akinta sabida ke. Domin ke nayi hakan ke d'aya." Fad'in Baba. "Aikin banza kawai!" Fad'in Aina'u. "Banza yi maki baki ba Aina'u, Allah ya shirye ki." Baba ya fad'i yana girgiza kai. Sarah kuwa wani d'an sauk'i taji a zuciyarta jin Baba ya mayar da Lami d'akinta. Da daddare har d'aki Sarah ta sami Lami tana kuka tana bata hak'uri akan ta janye tsinuwar da tayi mata, amma ko kallonta bata yi sabida ba k'aramin fanfo Aina'u tayi mata ba akan Sarah d'in. Sarah d'aki ta koma ta zari mayafi ta nufi pos ta ciro kud'i har dubu d'ari ta dawo gida ba bawa Lami akan ta karb'i kud'in amma ta yafe mata ta janye batun tsinuwa. Ganin Aina'u bata nan, sai ta amshe kud'in tace mata taje ta yafe mata. Ajiyar zuciya Sarah ta saki, sai a sanan taji hankalinta ya kwanta har ta iya tafiya gidansu Muneeba domin a cigaba da yi mata gyaran jikin da ake mata kullum da safe da kuma daddare. Don yanzu basa had'uwa da _Khalil_ sai dai a waya kawai. Don Mama (mahaifiyar Muneeba) da kanta tayi magana dashi a waya a kan yayi hak'uri ba zai k'ara ganin Sarah ba sai ranar aure. Ya amsa ne kawai don yana jin nauyinta. Amma kullum mak'ale take da waya. Wani lokacin sai mai gyaran jikin ta kwace wayar ta kashe sannan ake yin gyaran a nitse. Aina'u kuwa, kwana d'aya, biyu, uku, bata ji wani motsi daga gidansu _Khalil_ ba duk da gayyato matan zumunta da tayi sabida komai ya rushe. Karo ba uku kenan plan d'inta bai yin