← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 112

Sashe 75

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To sannu ɗan masu gida! Wai kai Khalilullah mai yasa baka da kawaici ne a rayuwarka? Ƙanwar matarka ce fa! Ai ko don uwata ka raga mata. Gaskiya ka ɗauki hakki, kuma ka bata haƙuri." Faɗin Hajiya rai a ɓace. Nuna Aina'u dake riƙe da kunci yayi da hannu tare da faɗin, "Wannan ɗin zan bawa haƙuri? Kiyi haƙuri Hajiya, ban taɓa tsallake umarninki ba, amma yau kam bazan iya abunda kika umarceni da nayi ba. Hajiya hayaƙi ma ba sonsa kike yi na sani, Laure ko ina da tabbacin bata ma taɓa ganin wiwi ba bare ta kai bakinta, yarinyar dake fama da kanta ma ina taga lokacin shan wiwi! Nayi imani da Allah Aina'u ce tasha wiwin nan, kuma a yau ɗin nan kuma ba yanzu ba, sai ta bar gidan nan wallahi!" Da ƙarfi Hajiya tace, "To kuwa za kayi kaffara don Aina'u babu inda za taje wallahi! Wiwi dai ni nasha gama sauranta nan." Faɗin Hajiya ta hau waige-waigen inda zata hango saurin da Aina'u ta har a parlourn, da sauri tace, "Yauwa gashi nan!" A tare suka kai jiki, ita ta kai hannu, shi kuma ya kai ƙafa ya take sauran guntun wiwin don kada Hajiya ta kai hannu ta ɗauka. "Ai Hajiya da sauri kika yi kika rigasa ɗauka, kin ga idan kika kunna kika yi zuƙa ɗaya a gabansa wata ƙila yafi gasgata maganarki." Wani irin shaƙa Khalil ya kai mata tare da faɗin, "Hajiya zan kashe yarinyar nan sai dai nima a kashe ni." Da sauri Hajiya ta taso ta hau kiciniyar kwace hannun Khalil a wuyan Aina'un da har idanunta sun soma firfitowa, "Wallahi idan baka saki wuyar yarinyar nan ba zan tsine maka Ibrahim." Wani irin wurgi da ita yayi sai da kanta ya bugu da Centre table ɗin dake ɗakin ji kake tatsatsatsatsa ya fashe, take jini ya hau tsartuwa a kan Aina'u wacce tuni ta sulale ta sume, hannu Hajiya ta ɗaura a kai tare da faɗin, "La'ilaha illalah, Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam, Khalilullah!" Da sauri Khalil ya bar ɗakin a zuciye, don shi ko a jikinsa duk da uban jinin da yaga Aina'un na zubarwa. Daga nan fita yayi daga gidan gaba ɗaya domin cuku-cukun passport ɗin Sarah. Hajiya kuwa gaba ɗaya ta ruɗe sai kiran sunan Khalil da ya jima da barin gidan take yi, Laure dake zaune itama ko motsi bata yi ba, addu'a kawai take yi a zuciya Allah yasa daga suman da tayi ta wuce barzahu kowa ya huta. Ruwa fridge Hajiya ta ɗauko ta fasa a fuskan Aina'un, a gigice ta farfaɗo tana zazzaro idanu, can kuma ta tashi da sauri jini na ɗiga ta wuce ɗakin dake mallakinta ta rufo ƙofa, bata damu da ciwon jikinta ba ta matsa tafin hannunta da ƙarfi sai ga Khalil ya bayyana a immigration office suna magana da wani, wani irin zaro idanu tayi tare da faɗin, "Barin ƙasar? To ai sai kuyi tafiyar in gani duk da kuwa na san idan asibitocin duniyar zaku zaga, Sarah baza ta taɓa samun lafiya ba." Tafin hannun ta kuma matsawa, sai ga wannan mummunar halittar ya bayyana fuska a ɗaure tare da faɗin, "To uwar ƴan ƙorafi, menene kuma yanzu?" Kallon gefe tayi tare da kai hannu ta ɗauki kwalbar turaren dake kan mirror ta fasa sannan yanki hannunta na dama tare da tsiyaya jinin a fuskan wannan mummunar halittar sannan ta ɗuka akan guiwowinta tare da faɗin, "Dan tsarkin tsafin _Hell Ofulafu_ ka taimakeni kamar yanda Khalil ya zubar min da jini, ina so shima ya ɗanɗana ɗacin da naji wajen yin kuka da idanunsa, ina son a yau ayi kukan mutuwa a cikin gidan nan, sannan a hana Khalil fita daga ƙasar nan da matarsa, bama ƙasar nan ba, a kasar masa da tunanin nemawa matarsa magani ko da a wajen Kaduna ne!" Ta ƙarisa maganar ne tare da tara kanta dake tsiyayar jini a tafin hannunta, yayin da mummunar halittar nan ya saka harshe yana lashe duk wani jini dake ɗiga a jikinta. Sai da ya gama lashewa sannan ya shiga ɓaɓɓaka mahaukacin dariya tare da turo hannu ya dafa kanta sannan ya ɓace. Lumshe idanu tayi tare da faɗawa bayi don ta san ɓacewar yana nufin buƙatarta zai biya. Khalil yana tsaye yaji kamar an kwaɗa masa guduma akai yayi saurin dafe kan tare da tsugunawa. "Lafiya Khalilullah?" Abokinsa yayi saurin ɗukawa tare da faɗin haka. Bai ce komai ba, amma ya daɗe yana jin wani irin wuuuu a cikin kansa kamun ya miƙe ba tare da yace komai ba ya nufi wajen motarsa, "Ibrahim! Ibrahim!!" Abokinsa yayi kiransa yana bin bayansa, amma ko sauraran bai yi ba ya buɗe motarsa tare da shiga yaja ya bar wajen, sai da yayi nisa da immigration office ɗin sannan ya soma jin wasai a cikin kansa. Aina'u kuwa canza kaya tayi tare da yiwa kanta dressing sannan ta kunna wiwi tasha tare codine saboda zuciyarta da yayi zafi, sai da ta zuƙi wiwi ta fesar sannan tace, "Na rantse da girman Yesu Almasihu, ba don tsananin son da nake maka ba, da wannan marin da fasa kan da kamin ba zai tafi a banza. Da sai na kashe ka a yau ɗin nan, amma duk da haka, You'll pay for it!" Nafeesa na kitchen tana dafa pasta, Qasim na parlour yana kallon Tv kwance akan resting chair dake parlourn yana jiranta ta kawo abuncin, don tun da suka tashi basu ci komai ba, "Honey kin kusa?" Ya faɗi da ƙarfi ta yanda Nafeesan zata ji daga kitchen ɗin, "Soon in Sha Allah!" Faɗin Nafeesa tana mai saka carot da ta gama wankewa, a gigice ta saki ludayin dake hannuta tare da buɗe baki za tayi ihu, cak bakin ya tsaya a buɗe ba tare da ihun ya fito ba, jininta babu inda baya rawa ga fitsarin tsoro dake zirarowo daga jikinta ganin halitta mafi muni a gabanta, harce ya fiddo kamar na maciji ya caki wuyanta ya shiga tsotse jinin jikinta, sai da ya tsotse kaf sannan ta faɗi ƙasa yaraf, shi kuma ya kai hannu ya cire pipe ɗin gas ɗin tare da haɗa gobara a kitchen ɗin sannan ya ɓace ɓat. Da mugun gudu Qasim ya fito daga parlourn jin wani irin warin gas na bala'i, yana tura ƙofar kitchen gas yayi wani irin uban tsalle ya bugi fuskansa, kan kace kwabo gaba ɗaya gidan ya kama da wuta, gas ɗin nan kuwa haka ya dunga tsalle yana faɗawa gidan maƙota. Kasancewar layine na masu kuɗi, tuni har a kira ƴan kwana-kwana na Private, kuma cikin ƙanƙanin lokaci suka iso suka fara aikinsu. Sai da aka fara cire wutan unguwar gaba ɗaya sannan aka shiga kashe wutan, mutane goma sha shida ne suka yi mummunar ƙonewa, daga ciki har da Qasim mijin Nafeesa, gaba ɗaya tun daga kai har tafin ƙafa ya ƙone, ana taɓa jikinsa fata ke biyowa, Nafeesa kuwa tattare dagwargwajajen namanta aka yi, don wasu ma dun manne a jikin tiles da wuƙa aka kankaro, babu abunda ke tashi unguwar sai koke-koken mutane. Ƴan uwan Qasim kamar zasu haukace, wasu suka nufi asibitin da aka kai shi, wasu kuma suna tare da dagwargwajajen naman Nafeesa, ya LTG Abdullah suka kira, sai dai number ɗinsa bai shiga don jiya ya bar ƙasan zuwa China. Mayar da aƙalan kiran suka yi zuwa ya Abdul-Hakeem, shikuma ya kashe wayarsa gaba ɗaya saboda tashin hankalin da yake ciki, Khalilullah da driving zai dawo gida wayarsa ta hau ringing, sai da yayi parking saboda bai ɗaga kira idan yana driving sannan yayi picking, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Shine abunda ya dunga maimaitawa har ya sauke wayar a kunnansa, haɗa kai da steri yayi wasu zafafan hawaye na zubo masa daga idanunsa, ya jima yana hawaye kamun yayiwa motar key ya nufi can gidan Qasim ɗin. Tun daga nesa da layin yake hango hayaƙi da ƙauri duk da an samu nasarar kashe wutan, parking yayi ya nufi inda ƴan uwan Qasim suke, maza huɗu ne da mata biyu, matan sai rusa kuka suke yi, mazan kuma sunyi jigum-jigum suna kallon naman Nafeesa. Kai tsaye wajen dagwargwajajen naman yayi tare da duƙawa yana kallo wasu maƙudan hawaye na zirarowa daga idanunsa, jikinsa har rawa yake yi tsabar tashin hankali, "Allah ya jiƙanki Nafeesa, Allah yasa kina cikin rahamarsa, Annabi yasan da zuwanki." Yana kawowa nan ya fashe da kuka tare da saka tafin hannunsa ya rufe fuskansa. Sai da Mukhtar wan Qasim ya ɗagosa tare da janyesa gefe yana bubbuga kafaɗunsa alamar rarrashi. Haɗa kai da bango Khalil yayi, hawaye sun kasa tsayuwa daga idanunsa, dakyar ya iya controlling kansa ya fiddo wayarsa daga aljihu tare da dialing number ya Abdullah, wayar bai shiga, sai ya kira layin ya Abdul-Hakeem, shi kuma switchoff, sai ya mayar da akalar kiran zuwa layin uncle Ameeru, bigu biyu ya ɗaga tare da faɗin, "Tunda naga kiranka nasan ba alkhairi zaka faɗa min ba, don haka nan baka kira ka gaishe mu, balle kuma yanzu da kayi aure kana ganin kanmu ɗaya!" "Allah yayiwa Nafeesa rasuwa ta hanyar gobara, yanzu haka ina can gidanta!" Shine abunda Khalil ya faɗi tare da yanke kiran ba tare da ya bari uncle Ameeru ya dire salatin da ya ɗauko ba. Uncle Ameeru a gigice ya kira sauran ƴan uwansa a waya ya shaida masu, nan da nan suka haɗu suka yo gida wajen Hajiya maimakon su wuce can gidan Nafeesan kai tsaye, Hajiya najin sautikan muryansu yayin tahowarsu taji gabanta ya faɗi don ta san zuwansu ba alkhairi bane, ɗayan biyu ne, ko sun zo neman kuɗi ko kuma tijarar da suka saba yi mata. Babu sallama suka faɗa ɗakin kasancewar ƙofar buɗe take don Hajiya bata kulle ƙofa idan dai ba dare bane. "Bilkisu ashe abunda ya faru kenan? Allah ya jiƙan Nafeesa, oh! Yaushe-yaushe ƴarta ta koma, ashe itama tana tafe." Da sauri Hajiya ta miƙe tana faɗin, "Ban gane ba mai kuke faɗi ba. Nafeesar ce ta mutu? Nafeesa tawa?" Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin su uncle Ameeru, don sun ɗauka ta san da mutuwar, Uncle Shamsu yace, "Kenan baki sani ba, ɗazun nan Khalil ya kira Ameeru yake faɗa masa gobara ta kama a gidan duk sun mutu
Chapter 75 · 0% Book details