Sashe 102
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 6 min read
suka fashe da kuka jikinsu na rawa jin abubuwan da Aina'u ta aikata daga ciki har da kwanciyar aure da tayi da mahaifinsu. Hassana ce tayi kan Lami tare da yayyafa mata ruwa ta farfaɗo, wani irin kuka Lami ta fashe dashi tare da faɗin, "Ubanmu wanda ke cikin Sama, na tsarkake sunanka, mulkinka shi zo akan abin da ka ke so ayi shi cikin duniyar nan kammar yada ake yinsa cikin sama. Ka gafarta mana laifinmu, kamar yarda muna gafarta ma waɗanda su ke yi mamu laifi. Kada ka kai mu wurin jaraba, amma ka cece mu daga Shaiɗan. Duka mulki, da iko da girma naka ne, har abada. Kada ka kama ni da laifin haihuwar Aina'u ya Yesu Almasihu! Na san ita mai saɓo ce mummana a gareka, saɓo mafi muni shine kwanciya da mahaifin daya haife ka, ya Yesu amintace, bani da laifi akan abinda ƴata ta aikata, kayi mata hukunci amma ka cire mu Ni da sauran ƴaƴana. Mai girma Yesu Almasihu, na duƙa da duka guiwowina a ƙasa ina neman yafiya da yafiyarka, ka amsa min, Amin." Khalil duƙar da kai kawai yayi yana jiran ace masa ga inda matarsa take. Na'ima da su Hassana kuwa kamar zuciyarsu zai fito saboda irin kukan da suke yi, "Mama dan girman Allah Aina'u ƴarki ce? Anya kuwa ba canje aka yi maki a asibiti ba? Ina ina ganin babanmu bashi ya haifi Aina'u ba, ɗan halak ba zai taɓa yin tarayya da mahaifinsa ba." Faɗin Na'iman. Sai da Lami ta fyace majina sannan tace, "Na rantse da girman Yesu Almasihu mai ceto, Ni da mahaifinku Nuhu muka haifi Aina'u, Aina'u ƴata ce, kuma ƴar Nuhu ce, Ni ina ganin baƙin da Mahaifiyata pasto Emanuella tayi min ne yake bina, don ta taɓa tsine min lokacin da zan auri mahaifinku Nuhu. To ni babban tashin hankalina shine, kai Khalil kace ka kori Sarah, to tun yaushe? Don Sarah dai bata zo gidan nan ba." Da sauri Khalil ya ɗago tare da faɗin, "What! Bata zo nan gidan ba? To ina zata je daya wuce nan ɗin." Duk a gigice yayi maganar kuma ya miƙe tsaye. "Gaskiya Saratu bata zo gidan nan ba!" Lami ta kuma faɗi tare da kallon su Na'iman dake kuka tace, "Ko ku kun ganta?" Girgiza kai suka yi dukansu, Khalil yace, "Wallahi yau kimanin kwanaki goma sha bakwai kenan da barin ta gidana, to idan bata zo nan ba, ina zata kenan? Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!! Allah ka tsare min matata da ƴaƴana a duk inda suke." Lami hannu ta ɗauka akai tare da soma kwarara ihu har da kwance zani tana faɗuwa a ƙasa tare da faɗin, "ƴata kina ina, ina kika je kika ɓuya? Yesu Almasihu ka nuna min hanya cikin sauƙi!" Khalilullah fita yayi da sauri tare da barin gidan hankalinsa a bugun tashe, buɗe mota yayi tare da shiga ya ɗaura kansa akan steri yana tunanin hanyar da zai fara neman Sarah. Kwankwasa masa glass yaji ana yi, a hankali ya ɗago tare da sauke glass ɗin motar Kasancewarta tinted, "Muneeba!" Ya kira sunanta da mamaki don rabon da ya sakata a idanunsa tun lokacin data kawo masu ziyara lokacin Sarah na fama da cutar tsutsotsin nan, don shi bai ma san tafiyarta ba, kuma tun daga ranar bai Kum samun labarinta ba. Buɗe mata murfin motar yayi tare da faɗin, "Naji daɗin ganinki, shigo ciki Please." Girgiza kai tayi tare da faɗin, "Kayi haƙuri ba zan iya shigowa ba, domin a yanzu haka maganar da nake faɗa maka idan har Babana ya samu labarin to tabbas zan fuskanci mummunar hukunci mai tsanani don ya haramta min nufa inda kuke ko yin magana da ɗayanku. Kaga wancen makarantar, acan nake koyarwa, fitowata kenan na ganka ka fito daga gidan nan shine nace bari na ƙariso mu gaisa." Shuru yayi na wasu ƴan daƙiƙu sannan yace, "Mai ke faruwa ne Muneeba?" Dafa glass ɗin motar tayi tare da faɗin, "Abunda ya wuce ya wuce, amma dai bari na tsungulo maka kaɗan daga halin da na shiga sanadin zuwa gidan ka wancen ranar. Bayan naga halin da ƙawata take ciki, sai na tashi da sauri domin zuwa wajen iyayena su taimaka mata da magungunan karya sammu da kuma addu'o'in da zata riƙe ya zama makaminta don its obvious matarka sammu ne a jikinta. To ina fitowa kawai naji an taɓa ni ta baya, juyowar da zanyi sai muka yi idanu huɗu da ƙanwar matarka, sai ta daki goshina tare da cewa in kalli gabas inyi tafiya kar in kuma dawowa gidan! To tun daga wannan lokacin ban kuma sanin inda kai na yake ba sai tafiya kawai nake ta yi, amma kasancewar iyayena ma'abota ambaton Allah ne haka nima kuma na tashi da wannan ɗabi'a shiyasa Allah ya sauƙaƙa min wahala ban jima ina garari ba aka gano inda nake aka dawo dani gida, sai dai na sha jinya mai tsayi kamun na samu kaina, bayan na dawo cikin hayyacina ne na shaidawa iyayena abunda ya faru, to daga nan ne sukai min iyaka daku, sannan suka ce in dai addu'a ce aduk inda aka yi to da cikin ƙarƙashin ƙasa ne zata karɓu indai anyi ta cikin yaƙini, saboda haka zasu riƙa bin ku da addu'a daga nan inda suke ba sai na kuma takawa inda kuke ba, sannan Babana ya saka min doka mai tsauri akan kar in kuskura ko hanyar gidanku na ƙara bi ta wajen." Shuru Khalil yayi yana mamakin irin mugun hali da rashin imanin Aina'u. "Allah ya saka maki Muneeba, muma Aina'u tayi mana muguwar cutarwa da tafi wanda tayi mai, sai dai kawai Allah yayi mana sakayya!" Rausayar da kai Muneeba tayi tare da faɗin, "Ameen, a gaida Saran, sai anjima." Tana gama faɗin haka ta ɗaga masa hannu sannan ta wuce. Ɗaga glass ɗin sama yayi tare da kunna motar ya bar wajen, a kan hanya sai saƙe-saƙe yake yi ta inda zai fara neman Sarah, ɗilin! Yaji saƙo ya shigo cikin wayarsa, kamar ba zai duba ba, sai kuma ya mika hannu ya ɗauko wayar dake kan seat ɗin gefensa, ganin debit alert daga GTbank sai yayi tsaki ya ajiye wayar, can kuma ya taka wani mahaukacin burki a tsakiyar titi, Allah yaso babu wanda ke binsa a baya, hannunsa na rawa ya ɗauko wayar ya shiga cire key da sauri, 'wrong pin' ya nuna masa kasancewar da sauri yake danna code ɗin. Khalil bai taɓa dana sanin saka pin a rayuwarsa ba sai yau don ƙosawa yayi ya buɗe wayar, ƙara sakawa yayi stil cikin sauri, wannan karan ya bude, shiga message ɗin yayi ya shiga karantawa da sauri, wani irin sanyin Ni'ima ce ta shiga bin saƙo da lungu jikinsa, "Allah Ubangijin mai kowa mai kowai, mai sauƙaƙawa bawa a cikin matsala, Allah Nagode da a wancen lokacin ka bani courage ɗin bata ATMcard ɗina." Faɗin Khalil sakamakon ganin debit alert daga Nasarawa, Lafiya state. "Wamba, unguwar abakwa!" Ya kuma faɗi a bayyane tuno lokacin da yake tambaye Sarah a kan wani yare su har ta faɗa masa sunan garinsu har da unguwar. "Alhamdulillah!" Ya kuma faɗi daidai da lokacin da wayarsa tayi ƙara, ganin Hajiya ke kiran wayar sai da gabansa ya faɗi. Jiki a sanyaye ya ɗaga wayar, "Ka dawo gida tunda ba'a can aka haife ka ba, kuma Marmari ya biyo jirgin sojoji yazo, isowarsa kenan shi da Ayshan. Abu na gaba kuma, kar ka kuskura ka shigo cikin gidan nan idan har ka san akwai igiyar aurenka aka ƴar dangin matsafan nan!"