← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 112

Sashe 107

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da farin ciki Hajiya Mariya tace, "Hajiya Bilki wanene zai ƙi son haɗa jini dake? Ai wallahi ko an tsayarwa Habbooba miji, haƙuri za'a bashi, gida bai ƙoshi ba ba'a baiwa na dawa ba, balle kuma Habbooba bata da wani tsayayye miji. Ba'a jima da kammala degree ɗinta ba. Yanzu ne ta ɗan soma kula samarin ma." Wani ajiyar zuciyar farin ciki Hajiya ta sauke tare da faɗin, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Shikenan tuwona maina, yanzu abunda za'a yi, ki ɗan fara Kwankwasawa Alhj Mutallab da maganar kamun daga nan su Marmari su zo tambayar aure, don so nake kawai da sun zo, har lokacin biki a tsayar. Allah yasa dai kar Habbooba ta bamu matsala!" "Hajiya baki da matsala, Habbooba kuma babu matsala daga wajenta in Sha Allah." Layla dake gefen Hajiya Mariya sai jan gyalen lifayan data naɗe jikinta take yi tana faɗin, "Umm! Umm!!" Ita kuma haj Mariya sai kai mata duka take yi tana bige hannunta, sai da ta gama wayar sannan ta kalleta a fusace tare da soma magana cikin yaren Shuwa, "Mai yasa baki da hankali ne Layla? Kin san da wacce nake magana amma sai takura ni kike yi, baki bari in gama wayar tukun sannan kiyi min duk maganar da zaki yi min!" Turo baki kyakkyawar farar yarinyar tayi tare da faɗin, "Haba Umm, why always Habbooba? Komai Habbooba, duk abunda kika samu, Habbooba, idan kyauta za kiyi, Habbooba is the first person to received before everyone, haba Umm!" Layla ta ƙarisa maganar cikin ɗacin zuciya. "To yanzu kuma me nayi Layla?" Faɗin Hajiya Mariya tana mai zama kusa da Laylan. "Naji lokacin da kuke magana da Aunty Yagana a parlour, shine kika yi sauri kika dawo bedroom ɗinki, and then yanzu kuma kina magana da aunty Bilkin Kaduna, kuma i heard anything you were saying, it all about uniting Habbooba and that son of her's!" Janyota jikinta tayi tare da faɗin, "Haba Layla, ba wai nafi son Habbooba bane a kanki, kin ga you're just 18years, amma ita she's 27years, kin ga dole ita zan so na fara kawaswa a nan gidan tafi gidan nata mijin kamun ke. Be petient, in Sha Allah kema mijinki na nan zuwa soon!" Shuru Layla tayi bata ƙara cewa komai ba. Tayi haj Mariya tayi tare da fita daga bedroom ɗinta ta nufi na Habbooba, tun daga corridor ɗin da zai sadata da ɗakinta take jiyo sautin wakar _Allela Belela_ kamar zai fasa dodon kunnenta, sai data toshe kunnen sannan ta iya ƙarisawa har cikin ɗakin Habbooban sannan ta kai hannu ta zare socket ɗin radion ta jefar. Wata fara tass ɗin budurwa ce kwance a kan gado daga ita sai wani Short kalar baby pink wanda ya tsaya mata iya cinya, sai rigar short ɗin ta kamfanin Armani da ya kawo dai-dai inda short ɗin ya tsaya mata, gashinta baƙi siɗik mai uban tsayi daya barbazu akan gagon, rubutu take yi a kan wani jotter kuma a lokaci guda tana kallon screen ɗin iPhone X ɗinta, jin waƙar da take sauraro ya tsaya cak sai tayi saurin juyowa da sauri, kyakkyawa ce ta bugawa a jarida, gashinta ya watsu baya, wasu kuma suka rufe gefen fuskanta, hannu ta saka ta mayar da gashin baya tare da turo baki ganin mahaifiyarta ce da wannan aikin. "Habbooba." Mahaifiyar ta kira sunanta a hankali tare da zama a bakin gadon, cikin sauri Habbooba ta kawo kanta ta ɗaura a kan cinyar maman tata, "Ya Rasulullahi, Habbooba na hana ki ƙure sauti a ɗakinki, idan za kiji waka, ki riƙa saka sautin daidai kunnanki dan Allah!" "Umm, idan ban saka volume dayawa ba, waƙar bai min daɗi sosai." Faɗin Habbooba. Ajiyar zuciya Umm tayi tare da faɗin, "Habbooba!" Ɗagowa tayi ta kalli Umm ɗin jin yanda ta kira ta with seriousness, "Na'am, Umm!" "Kin san wannan?" Umm ta faɗi tare da nuna mata hoton Khalil lokacin yana _Las Vegas_, tsaye jikin wani ƙarfe hannunsa biyu sanye cikin aljihun wandonsa yana sanye cikin wata navy blue ɗin bodyhug irin highneck ɗin nan, murmushin kwance a fuskansa wanda ya bayyanar da 2dimples ɗinsa, ba ƙaramin kyau yayi ba. Ƙarɓan wayar tayi a hannun Umm tare da zoomin picture ɗin sosai tana faɗin, "Wow! He look familiar, amma na rasa inda na taɓa ganinsa. Yana da kyau sosai Umm." Wani murmushin jin daɗi Umm tayi tare da karɓan wayar sannan tace, "Future husband ɗinki ne!" Waro idanu Habbooba tayi tare da tashi zaune tace, "Umm, are you for real? Like da gaske kike Umm?" Dariya Umm tayi tare da faɗin, "Ni na taɓa yi maki ƙarya ne? Mahaifiyarsa ce ta buƙaci ya ƙara aure saboda bata son first wife ɗinsa da yake zaune da ita, shine ta zaɓe ki a matsayin matar da zai aura, kuma kin san ko shi ɗin ɗan wanene?" Girgiza kai Habbooba tayi gabanta na faɗuwa jin yana da mata, don it's obvious Shuwa basu ƙaunar kishiya! "Ɗan _late CJN Nurudden Muhammad_ ne, kuma kin san dai CJN Nurudden Muhammad mijin cousin ɗita ce, don da mahaifin haj Bilki, da Mahaifiyata, ubansu ɗaya, uwa ce kowa da tasa." Jinjina kai Habbooba tayi tare da faɗin, "Na tuna, na tuna inda na taɓa ganinsa, lokacin da muka je ta'aziyar mahaifinsa ne na taɓa ganinsa, he's a medical doctor ko?" Jinjina kai Umm tayi tare da faɗin, "Tabbas shine, kin gane sa." A sanyaye Habbooba tace, "Umm I love him, but yana da mata kika ce." Ta ƙarisa maganar cike da rauni. Kamo hannunta Umm tayi tare da faɗin, "Come on, sai kace ba Shuwa ba, Kar ki bani kunya mana, Shuwa ba'a san mu da tsoran kishiya ba, kishiya ko wacece ita bata bamu tsoro. Ni dama kuma amincewarki nake so, kuma baki san wani abu ba, ita matar tasa ma, sakinta za ayi don ita mahaifiyar tasa cewa tayi dole ya saki first wife ɗinsa, kuma da zarar anyi auren, _Las Vegas_ zaku wuce acan za kuyi zaman ku." Wani irin runguma Habbooba tayi wa Umm tare da faɗin, "Na amince Umm, zan aure shi kuma ni dama tun ganin da nayi masa na farko naji ina matuƙar sonsa." Shafa kanta Umm tayi tare da miƙewa fuskanta cike da murmushi ta bar ɗakin. Bayan kwana biyu! "Khalil ka san mai yasa nayi kiranka a gaban ƴan uwanka gasu gaba ɗaya?" Faɗin Hajiya tana yin nuna gasu, ya Abdullah, ya Abdul-Hakeem, ya Barrister, da kuma Aysha. Girgiza kai Khalil yayi, don shi da badan ritsa shi da aka yi ba, da yanzu haka yana hanyar Nassarawa wajen matarsa, "Yauwa, to na kiraka ne in kuma jaddada maka maganata akan sakin matarka, Ibrahim wallahi dole ne ka saki yarinyar nan, ƴaƴa kuma ni da kai na zan aika har Nassarawar a ɗauko min su, kar ka damu ba zan barka babu mace ba tunda ka riga ka saba da mata, na zaɓo maka cikin dangi, ba kuma ƴar kowa bace sai ƴar ƙanwata Habbooba, yarinya fara tas kyakkyawa da ita. Don haka idan ba so kake na ɗaga maka nono ba, dole ne ka saki yarinyar nan, ehe. Aure kowa ya san ba dole bane, shikuwa saki surah sukutum aka saukar a kansa, Allah da kansa shi ya halatta sakin aure! Kuma na riga nayi rantsuwa sai ka saki Saratu!" Kan Khalil a ƙasa babu abunda yake zubarwa face hawaye. Ya Abdullah gyaran murya yayi tare da faɗin, "Hajiya, Ta yiwu ɗaya daga cikin dalilan da ya sa ake kiran wannan sura da sunan surar saki (Ɗalak) shi ne irin hukunce hukuncen sakin da suke ƙunshe a cikinta makil, wanda wannan yana nuna mana irin la'akarin da shari'ar musulunci ta yi dangane da al'amarin saki, saboda irin hatsarin da yake da shi, domin abu ne wanda in har ba'a yi da gaske ba, kuma ba'a yi shi yanda musuluci ya zo da shi ba, sai ka samu ya taimaka wajen wargaza al'umma da tarbiyyar iyali, kana da haifar da gaba da kiyayya a tsakanin dangi. Kamar yanda rashin kiyaye hukuncin sakin ke iya haifar da aure kan aure, wanda daga karshe a dinga haife 'ya'ya marasa tabbas ɗin iyaye. Kamar yanda kuma, shi saki ba wani abu ne wanda shari'a ke ƙarfafa gudanar da shi ba, bil hasali ma shi ne halas wanda Allah ya fi ƙi, kamar yanda ya zo a mashahuriyar ruwaya daga Ma'asumai (A.S.) "Babu wani abu da Allah ya halatta kuma yake fushi da shi fiye da saki. Wannan ruwayar ta zo cikin Wasa'ilus shi'ah juzu'i na 15 shafi na 266. Sai dai kuma wani abin tambaya a nan shi ne, mene ne ya sa shari'a ta halatta yin saki ? Amsa a nan ita ce a irin hali na zaman yau da gobe na ma'aurata a wasu lokuta za ka samu cewa akwai wasu halaye waɗanda suke faruwa marasa daɗi wanda in da za'a tilasta ci gaba da zama da juna a tare da waɗannan halayen, sai mu samu rayuwa za ta yi ma wanda yake cutuwa, tsanani da kunci wanda zai iya kaiwa ga halaka da abin da ya yi kama da haka. To saboda Allah ne mahaliccin kowa da komai, kuma asanin abin da zai kai ya kawo, don haka ya kawo magani da mafita a duk lokacin da irin waɗannan matsaloli suka bijiro a tsakanin ma'aurata, wanda wannan magani shi ne saki, duk da cewa ba'a son al'amarin ya kai ga haka, sai ya zama dole. Musulunci addini ne da ya ƙunshi komai da komai don inganta rayuwar ɗan Adam a duniya da Lahira. Bai bar ɗan Adam ya yi amfani da hankali da tunaninsa kawai don tsara wa kansa makoma ba, saboda shi ɗan Adam mai rauni ne, mai son zuciya ne, mai haɗakma ne, mai rowa ne, kai ƙarewa ma mai butulci ne ga wanda Ya halicce shi. To in har zai yi butulci ga Mahaliccinsa, ta yaya zai tsara rayuwar da sauran abokan zamansa za su ji daɗi? Aure daya ne daga cikin ginshiƙan rayuwar al’umma, wannan ya sa Musulunci bai bar shi sasakai ba ƙa’idoji da dokoki ba. Kuma baya ga ƙa’idojin zamantakewa a tsakanin ma’auratan, duk da ba a fata, amma ya tsara yadda za a rabu idan aka kasa samun jituwa ko maslaha a tsakanin miji
Chapter 107 · 0% Book details