Sashe 46
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke, bana son hauka! Kaza ce ita da zata b'ata? Ba ke kika kira wayarta ba? Kamun na juyo yanzu ki nemo min matata a duk inda take idan ba haka ba a kaf zuri'arku bana tunanin akwai wanda zan iya kyalewa ko jaririne." Yana gama fad'in haka ya katse wayar tare da yin reverse ya fizgi motar da gudu don har yayi nisa da layin. Muneeba kuwa jikinta ne ya soma wani kakkarwar tsoro zufa na yanko mata. Wayarta ta haska ta soma bin hanya tana kwala kiran "Sarah" ko Allah zai saka ta amsa. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Fad'in Munee tare da saurin d'ukawa ta d'auki takalmi da kuma ledar da _Khalil_ ya ba Saran. Kuka Munee ta fashe dashi tare da fad'in, "Inna lillahi wa'inna ilaihir, Allahumma arji'ini fi musibati. Saratu kina ina? Mun shiga uku, wayyo Allah, Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." Haka ta dunga yin gaba tana dawo baya tare da ambatan sunan Allah. _Khalil_ nayin parking ya nufi hanyar da Sarah tabi a gaban idanunsa, kicib'is suka yi da Muneeba dake kuka tana kiran sunan Allah. "Ke!" Ya daka mata wani irin tsawa tare da fad'in, "Ki bar wannan haukan kukan ki fad'a min ina matata take." Gaba d'aya sai Muneeba ta sake rikicewa saboda yanda yake daka mata tsawar. Takalmin Sarah da ledan hannunta kawai ta mik'a masa jikinta na rawa. Hannu ya kai ya amsa yana kallon ledar da kuma takalmin. Tabbas ledar da ya bata ne kuma takalmin ma nata ne. Ransa ne ya k'ara b'aci, bai iya yi mata wani magana ba sai wayarsa da ya fiddo ya danna number d'in ya Abdullah-Hakeem. Ringing uku ya d'auka yana fad'in, "Ango kasha k'amshi." Shi kuwa _Khalil_ cewa yayi, "Yaya motocin mutanan ku uku nake so yanzu. An sace Sarah. So nake gaba d'aya daga farkon Jos road har zuwa k'arshe a zuba mutanan ku, duk wanda aka yayi kala da rashin gaskiya a kama shi." Tashi zaune ya Abdul-Hakeem yayi tare da fad'in, "An sace Saratu? Wannan ma k'arya ne. Ka kwantar da hankalinka yarinyar nan in Sha Allah baza ta kwana ba. Yanzu zan kira yaya Abdullah domin ya turo mana da sojoji, kuma zan kira abokina ACP Lawal Yakubu domin a bamu police guda talatin. Gamu nan zuwa yanzu. Koma wanene yayi wannan aikin zai san ya tab'o jinin Chief Justice Nurudden Muhammad Ibrahim." Yana gama fad'in haka ya katse wayar tare da soma kiran yaya Abdullah. Yaya Abdullah ya fisa ma d'aukar zafi don kamar zai fito ta wayar. Kuma take yayi waya bariki aka turo motar sojoji har biyar. Tun daga Katsina round about mutanan dake Jos road suke jin jiniyar y'an sanda da sojoji. Matasa gaba d'aya hankalinsu ya tashi. Mutane sai firfitowa suke daga gidajansu suna kallo, wasu kuma suna dannawa nasu gidan sakata. Y'an daba da y'an shaye-shaye kuma sai nemar mab'oya suka soma yi. Tun daga farkon Jos road y'an sanda da sojoji suka samu position suka tsaya fuska babu rahama ko kad'an har k'arshe layin. Su Hajiya Lami kuwa cewa tayi, "Yanzu haka saboda d'aurin auren da za ayi gobe ne aka turo so domin su bamu tsaro." Na'ima tace, "Babu shakka kam!" Baba dake d'aki kuwa hakanan yaji hankalinsa bai kwanta ba. Aina'u kuwa gaba d'aya ta kasa sukuni sai lek'e take yi tana kiraye-kirayen waya. Muneeba kuwa sai kuka take yi a gaban _Khalil_ tana mashi rantsuwar ba da ita aka had'a baki ba kuma wallahi bata san inda Sarah take ba, bata san ko wa ya sace ta ba. Shikuwa _Khalil_ kwakkwarar motsi ya hanata don cewa yayi bai yarda da ita ba. K'aran jiniyar motocin sojoji da y'an sandan da suka iso inda suke ne ya k'ara hargitsa mata tunani ta saki wani marayan kuka tana k'an'k'ame jikinta. "Ke!" Wani soja ya buga mata uban tsawa sai gata a zube a k'asa ta sume dai-dai lokacin da ya Abdul-Hakeem ya iso wajen. Shi da kansa ya zira hannu ta cikin motar _Khalil_ ya d'auko ruwa tare da yayyafawa Muneeba. A firgice ta farfad'o tana fad'in, "Wallahi bani bace, ban sa wanda ya sace ta ba, kuma wallahi bani na kirata a waya ba." Hannu ya Abdul-Hakeem ya saka a baki tare da fad'in, "Shssh! Kwantar da hankalinki babu abunda za ayi maki a nan wajen. Yi min bayani mai ya faru." Ajiyar zuciya Muneeba ta sauke tare da fad'in, "Sarah tu a gidan mu take kwana tun saura kwana biyar bakinta. Kuma mama ta hana mu fita kuma ta cewa _Khalil_ ya hak'ura da zuwa tad'i har sai an kawo masa ita gida sabida ana mata gyaran jiki. To kullum sai suyi ta damuna su biyu suna cewa suna kewar juna. Shine jiya muka yi waya da shi _Khalil_ akan in taimaka masa in fito masa da Sarah suga juna ko mintuna biyar ne, shine na fito da ita ba tare da sanin mama ba na kawo ta wajensa sai na koma gida domin basu waje suyi magana. To K'anwar Sarah tazo gidan mu tana neman ita Sarah har mama taji shine ta tambaye ni ina Sarah, sai nayi mata karyar tana ban d'aki shine nayi sauri na fito domin in kira ta mu koma gida. To da nazo nan d'in sai naga babu motar _Khalil_ sai nayi ta kiran number d'in Sarah amma ba'a d'agawa, daga k'arshe ma aka kashe. Shine na kira shi _Khalil_ d'in ina tambayarsa Saratu, sai ya fara min ihu wai ai nice na kira ta har ta tsora tace wata k'ila an gane bata gidan ne sai suka yi sallama ta tafi. Kuma ni wallahi, tallahi ban kira ta ba." Haushi ne ya kama _Khalil_ jin rantsuwar da tayi akan bata kira Sarah ba, bai san lokacin da ya d'aga hannu zai wanke fuskanta da mari ba, da sauri Abdul-Hakeem ya tare hannunsa tare da fad'in, "Baka da hankali ne? Ko in barka kayi binciken ne da kanka? Ashe babu amfanin kiran mu da kayi kenan?" Matsawa baya _Khalil_ yayi tare da fad'in "I'm sorry." Kallon Muneeba yaya Abdul-Hakeem d'in yayi tare da fad'in, "Ina wayarki?" Da sauri ta mik'a masa wayar hannunta na rawa shi kuma ya mik'a wani dake gefensa. Cike da ladabi ya amshi wayar sannan ya sara masa tare da koma cikin mota ya kunna computer ya soma danne-danne cikin sauri da kwarewa. Muneeba kuwa da mararta ke cike da fitsari, ihu d'aya za'a kuma buga mata ta saki fitsari. Mintuna biyar sai ga wannan da aka ba waya ya dawo tare da fad'in, "An kira number d'in sau bakwai mintuna goma sha bakwai baya amma ba'a d'aga ba kuma daga baya aka kashe wayar. Lokacin da ake kiran wayar ba'a d'aga ba, nabi diddigin layin, makwamusan suna dai-dai round about d'in stadium, kuma an kashe wayar ne a dai-dai wajen tare da jefar da waya. Don har yanzu diddigin layin na wajen. Sannan kuma an kira wayar k'arfe bakwai da mintuna arba'in da uku, sai dai har ya gama ringing ba'a d'auka ba." Da sauri _Khalil_ yace "Lokacin muna tare, kuma a wannan ne Sarah hankalinta ya tashi ta wuce gida." Abdul-Hakeem ya kalli Muneeba tare da fad'in, "Kin ce baki kira Sarah ba, kuma gashi bincike ya nuna kin kira da misalin 7:43." Kuka Munee ta saka tare da soma rantsuwa tana fad'in, "Na rantse da ubangijin da ya halicceni ban kira taba, bani na kira ta ba." "To idan baki kira taba, waye ya kira ta? Kin ba wata wayar ne a wannan lokacin?" Shuru Muneeba tayi tana tunanin wa ta ba wayar a wannan lokacin? Kallon Abdul-Hakeem tayi tare da girgiza kai tace, "Ban ba kowa wayata ba a wannan lokacin. Kuma wallahi ban kira ba." "Oga wannan yarinyar fa baza tayi magana ba har sai mun tafi da ita." Fad'in wani police. Tuni Muneeba ta soma sakin fitsarin da ya dad'e da cika mata mara tare da durk'usawa a k'asa tace, "Na rantse da girman Ubangiji da ya halicceni ban sace Saratu ba. Wallahi bani bace. Dan Allah kar ku tafi dani." Yaya Abdul-Hakeem tun kallon farko da yayi wa Muneeba ya san cewar bata da hannu a cikin sace Sarah da aka yi, sai dai tabbas duk wanda yayi hakan yana tare da ita amma ita bata san hakan ba. "Wa kika ce tazo neman Sarah har mamanki taso ta fahimci bata gidan?" Da sauri Muneeba tace, "Aina'u!" Wani harara _Khalil_ ya watsawa Muneeba tare da fad'in, "Aina'un ce za ta sace Sarah?" Girgiza kai Muneeba tayi tare da fad'in, "Ba haka nake nufi ba." yaya Abdul-Hakeem kuwa cewa yayi "Aina'u tayi amfani da wayarki ne lokacin da tazo?" Da sauri Muneeba ta girgiza kai tare da fad'in, "Bata yi ba. Cewa kawai tayi ina Sarah. Ni kuma nayi saurin janta gefe nace tayi shuru kar mama taji don ta hana mu fita ni kuma na saci hanya na kai Sarah wajen _Khalil_. Ita kuma sai ta mik'o min kayan Sarah tace in bata baza ta iya jiran Sara ta dawo ba, don itama jiranta ake yi saurayinta yazo." "Wani irin kaya ta kawo mata, kuma dama Sarah ce tace ta kawo mata kayan?" Fad'in ya Abdul-Hakeem. "Eh ita ce tace ta kawo mata doguwar rigar baccinta da kuma hula." Jinjina kai Ya Abdul-Hakeem tare da fad'in "Jeki gida, zan neme ki idan buk'atar hakan ta taso." Da sauri Muneeba ta juya har da had'awa da gudu ta bar wajen. Shi kuma _Khalil_ a fusace ya kalli ya Abdul-Hakeem tare da fad'in, "Ya ka barta ta tafi? Ita ce suspect d'in fa." Ko kallonsa ya Abdul-Hakeem bai yi ba, sai daga ma d'aga kiran da aka yi masa yayi tare da sakawa a kunne. "Ok kar ku tab'a komai gamu nan zuwa." Yana gama fad'in haka ya yanke wayar tare da kallon _Khalil_ yace, "Shiga mota ka biyo bayan mu." Shi kuma ya nufi motar da ya shigo bayan ya bawa sauran y'an sandan umarni akan kar ku yarda su bar wajen har zuwa gobe shi kuma ya shiga motar da ta kawo sa suka nufi Barnawa inda wanda ya kira yanzu ya fad'a masa. Kasancewar gudu suke yi kuma ga shi dare ne babu mototi akan titi sosai, cikin k'ank'anin