Sashe 15
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon yaron Sarah tayi, sannan ta maida kallonta izuwa wajen Baba tare da fad'in, "To kuma wanene? Na san dai Farouq ba zai sake dawowa k'ofar gidan nan domin ni ba." Baba yace, "Kije kiga ko wanene ke kiran naki. Allah yasa dai lafiya." B'ata rai Sarah tayi tare da fad'in, "Da kuma so nake na kora yaron yaje yace bazan zo ba." Girgiza kai Baba yayi tare da fad'in, "Ba'a haka Saratu. Ba'a wulak'anta d'an Adam. Kije kiga ko wanene." "Je kace tana zuwa!" Sarah ta fad'i tare da mik'ewa don har yanzu tana ganin jiri-jiri ga kuma yunwar dake kwakwular cikinta. D'aki ta koma ta canzo hijjab d'in jikinta ta saka wani brown wanda ya kai mata har guiwa sannan ta fito tana dafa bango ta nufi waje. Baba na kallonta har ta fice kamun ta ya sunkuyar da kai yana tsiyayar da hawayen tausayinta. Sarah kuwa tana fita taci karo da wata arniyar motar da bata tab'a ganin irinta ba k'irar *_Aston Martin Vulcan_* kalar ash mai duhu. Ba ita kad'ai ba, hatta jama'ar layin fitowa suka yi suna kallon motar. Shi kuwa _Khalilullah_ sai da ya gama k'are mata kallo ta cikin tinted glass d'in motar sannan ya bud'e tare da ziro k'afarsa d'aya. Farar kyakkwar k'afar ta soma bi da kallo kamun taga ya fiddo da gangan jikinsa, tun daga d'an yatsan k'afarsa take kallo har ta sauke a kan fararan manya-manyan idanunsa masu matukar d'aukar ido. Wani irin lumshe idanu tayi jin daddad'an k'amshin turaren *_Imperial Majesty_* da ya bugi hancinta. Sosai take matuk'ar son k'amshi musamman a yanayin da take ciki. Folding hannunsa yayi tare da jingina a jikin motar yana kallonta. Bud'e idanu tayi a hankali ta kuma sauke idanunta a kansa karo na biyu tayi saurin b'ata fuska tare da k'ok'arin juyawa zata koma cikin gida. Cak ta tsaya sakamakon jin abunda yace, "Kul! Kar ki sake ki bar wajen nan idan ba haka ba zan baki mamaki." Juyowa tayi ta watsa masa harara tare da bud'e baki za tayi magana shi kuma ya d'aura d'an yatsansa a kan bakinsa tare da fad'in, "Ssshh! Ko kalma d'aya." Yana fad'in haka ya tako cike da isa ya iso inda take a tsaye tare da fad'in, "Kin yi missing d'ina ko?" Karo na biyu ta kuma watsa masa harara tare da d'an matsawa baya kad'an jin kamar zasu had'e da juna ga kuma wannan mayataccen k'amshin nasa dake naiman sumar da ita a tsaye. "Zan kwakwule idanun nan naki idan suka kuma hararata." Kallon gefe Sarah tayi tare da fad'in, "Menene matsalar ka dani ne? Mai yasa ka addabi rayuwata? Dan girman Allah ka kifa daga rayuwata in samu salama. Ka barni da bala'in daka jaza min dan girman Allah!" Sarah ta k'arisa maganar tare da fashewa da kuka. Kallonta ya dunga yi ba tare da ya ce mata tayi hak'uri ta daina kuka ba. Sai da tayi mai isanta sannan ya saka hannu cikin aljihu ya fiddo da wani d'an ma daidaicin handkerchief ya mik'a tare da da fad'in, "Come on, wife those tiers of yours!" Karb'an handkerchief d'in tayi tana mai watsa masa harara sannan ta kai kan fuskanta, kamun ta share hawayen sai da ta zuk'i k'amshin turaren tukun. "To bani abuna." Ya fad'i yana mai mik'a mata hannunsa. Mik'a masa tayi tare da fad'in, "Ai dama bani na rok'a ba." Amsa yayi tare da yin murmushi ya maida cikin aljihunsa sannan yace, "Kin matuk'ar bani wahala Sarah! Kin san kuwa irin naiman ki da nayi?" Kamar ta shak'e masa wuya haka take ji, wani tsaki tayi tare da fad'in, "Idan abunda ya kawo ka wajena kenan, juya ka bar k'ofar gidan nan yanzu. You're not welcome here. Out of my sight. Kuma yanda ka tarwatsa min farin ciki, kai ma baza ka tab'a samun farin ciki ba." Maimakon maganganunta su bashi haushi, sai yayi wani irin murmushi mai sauti tare da fad'in, "Idan har bazan tab'a samun farin ciki ba, to kema baza ki tab'a samu ba Sarah. Domin an halicceki ne domin ni kawai. Farin cikina yana tare dake, haka kema farin cikinki yana tare dani ne. Sannan kuma ina so ki saka wannan maganar da zan maki yanzu cikin kwakwalwarki, ba ai min tsaki! Kar ki sake." D'ago jajayen idanunta tayi zata saki masifa sai ga keke napep ya tsaya a bayan motar _Khalil_. Aina'u, Nuratu, Na'ima da Hassana a baya, sai Lami dake zaune a gaba ta rik'e k'arfe. Fitowa suka yi gaba d'ayansu suna k'arewa motar _Khalil_ kallo. Lami ce ta riga kowa magana tare da fad'in, "Kun ga wata arniyar mota! Wallahi tunda uwata ta haife ni ban tab'a ganin mota mai kyawu ba irin wannan." Na'ima ta kalli Nuratu tare da fad'in "Kamar fa *_Aston Martin Vulcan_* nake gani." Nuratu tace "Ya kike fad'i da kaya a jikinki! Ai kuwa tabbas ita ce wallahi." Zagayawa suka yi domin su k'arewa motar kallo dakyau. Idanunsu ya sauka akan Sarah dake kallonsu tana addu'ar Allah yasa kar su nuna halinsu _Khalil_ ya raina ta. Sai dai Addu'arta bata karb'u ba domin da sauri Lami ta k'arisa wajen tana k'arewa _Khalil_ da Sarah kallo. "Eh lallai! To yau dai Allah ya tona asirinki kin kawo sa har k'ofar gidanku. Wato saboda kin ga bama gidan ko?" Sai ta maida dubanta ga _Khalil_ tare da fad'in, "Samari kalle ni nan, nice mahaifiyar Sarah." D'an sunkuyar da kai _Khalil_ yayi tare da risinawa yace, "Sannu da zuwa Mama, ina wuni, mun sameku lafiya?" Shan mur Ki tayi tare da waigawa ta k'ara k'arewa motar _Khalil_ kallo sanna ta maido dubanta ga _Khalil_ d'in tare da fad'in, "Bafa lafiya ba. Domin dai yanzu haka daga police station muke ni da sauran y'ay'ana gasu nan kana kallonsu." Tayi nuni da su Nuratu da suka k'ariso suma. Kallo d'aya yayiwa Aina'u ya shaidata, kuma itama ta gane sa. Kau da kai tayi tana tsaki cikin zuciyarta. Shuru _Khalil_ yayi yana sauraran Lami. Ita kuma ta cigaba, "To ni bama duk wannan ba, ashe kai ne uban cikin dake jikin Saratu, amma don tsabar iskanci da mugunta irin nata, sai tak'i fitowa ta fad'a min gaskiya don kar a dangwali arzikin dani, to yau dai Allah yayi sai mun yi foureyes da kai. Don haka akwai list d'in da nake rubutawa in ajiye sabida irin haka. Don fisabilillahi bazan iya ciyar da y'ay'ana kuma in ciyar da nasu y'ay'an ba. A k'a'ida ta zama cikin gidana, a cikin su kaf...." Tayi nuni da su Nuratu tare da cigaba da fad'in, "Duk wacce tayi ciki to kawo saurayin take gidan nan muyi tsada dashi domin d'awainiya da cikin, bayan ta haihu kuma, ni can cigaba da kula da babyn, cinsu, wankansu da duk wani abun da suke buk'ata. Don haka kai ma zan baka wannan list d'in, na ganka da maik'o a jikinka, don haka list d'inka daban ne." Kuka Sarah ta fashe dashi tare da durk'ushewa a wajen. Lami kuwa da baki ta nuna ta tare da fad'in, "Munafuka! Kiyi kukan jini ma. Wallahi sai na kawo masa list d'in nan kuma sai anci arzikin dani." Turo baki Aina'u tayi tare da watsawa Lami harara tace, "Sai kuma aka ce maki shi yayi mata cikin? To bashi bane!" Ta k'arisa maganar a tsawace. _Khalil_ kuwa mutuwar tsaye yayi yana kallon Lami da sauran y'ay'anta. So yake yaji ana tashinsa ana fad'a masa cewar mafarki yake yi, amma sai tsungulin cinyarsa yake yi ta baya, da yaji zafi sai ya tabbatar fa lallai ba mafarki bane. "Wannan wani irin gida ne na kawo kaina?" Fad'in _Khalil_ cikin zuciyarsa, amma a zahiri bakinsa ko motsi ya kasa yi sai bin Lami da idanu yake yi. Zuciyarsa na tabbatar masa da cewar Lami ba ita bace mahaifiyarsu Sarah. Ga dai y'ay'a nan kyawawa Allah ya bata, amma kuma babu tarbiya. "Jira ni, bari na shige na kawo maka list d'in." Fad'in Lami tare da shigewa cikin gidan. Na'ima kuwa, kallon Sarah tayi tare da fad'in, "Lallai Sarah kinyi babban kamu babu k'arya! Ina jiran nawa kason a cikin jira. K'anina a bata nawa kason ta kawo min." Fad'in Na'ima tare da shigewa. Nuratu kuwa sai kallon motar take yi ita da Hassana suna Santi. Don har hotuna suka yi a jikin motar kamun suka shige cikin gidan. Aina'u kuwa wani kallo tabi Sarah dake duk'e a k'asa tana kuka tayi tare da jan dogon tsaki ta kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Baka dai ji warning d'in da nayi maka ba kenan? Kana wahalar da kanka ne. Don tabbas gidan mu ba'a aure." Tana gama fad'in haka ta fad'a cikin gidan. _Khalil_ ya jima a tsaye mamaki kamar ya kashe sa kamun ya duka ya kalli Sarah cike da dakewa yace, "Mik'e.!" Yanda yayi maganar cike da command ya saka bata san lokacin da ta mik'e tsaye ba. Jiri ne ya kwashe ta tayi baya zata fad'i yayi saurin tarota ta fad'o jikinsa dai-dai lokacin da Lami ta fito hannunta rik'e da wata doguwar paper. Wani dariya tayi tare da fad'in, "Kaiii jama'aa! To ai da shigowa kuka yi daga ciki sabida idanun jama'a. Ka san fa unguwar nan an saka mata idanu." Wani irin kallo ya jefi Lamin dashi, don wani irin tsanarta yaji ya darsu cikin zuciyarsa. "Ungo amshi nan!" Fad'in Lami tana mai mik'a masa paper d'in. Da kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya mik'a hannu ya amshi paper d'in yana kallon cikin idanunta. "Sai na ji sak'on ka, kuma da kanka nake son kazo." Tana gama fad'in haka ta juya ta koma ciki. Da idanunsa da suka rikid'e suka koma jazur yake kallon Sarah tare da daga mata wani gigitaccen tsawa yace, "Mai kike nema? Nace mai kike so da baza ki iya fad'a min ba? Mai yasa kika min haka? Mai yasa kika bawa wani kanki Saratuuu??" Bakinsa har rawa yake yi don har hasaso yanda abun ya kasance yake yi a idanunsa. Kuka Sarah ta fashe dashi don sosai ta tsorata dashi. "Ke! Ba kuka nace kiyi min ba, bayani zaki yi min. Uban wa yayi maki ciki?" Yanda yake maganar da k'arfi da kuma tsananin b'acin rai sai ya sanya jikin Sarah soma wani irin rawa tana