Sashe 8
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 5 min read
"To sai me idan mun kashe sun? Ai dama ni na jima da sanin ba k'aunar mu kake ba ni da y'ay'ana. Kana d'aka kana jin duk maganganun da matan nan suke fad'a min, amma baka iya fitowa ba, sai da kaji muna d'aukar mataki tukun zaka fito kana wani maganar banza da wofi, yara, ku cigaba da d'umamun su!" Ko rufe baki bata yi ba, su Nuratu suka cigaba da dukansu aunty Halima. Tsabar azaba aunty Luba kuka take yi tana basu hak'ura amma basu saurara ba. Baba kuwa dogaro sandar shi yayi tare da isowa inda suke ya d'aga sandar ya makawa Lami, sannan ya kuma d'agawa ya bugawa Nuratu da Aina'u, ya d'aga zai bugawa Na'ima, tayi caraf ta rike sandar tare da tura shi baya sai da ya kai k'asa k'afarsa ta markwad'e, Aina'u kuwa d'aga k'afa tayi dagangan ta take yatsun k'afarsa har da murzawa. Wani irin salati Baba ya saki tare da fashewa da kuka yana mai kai hannu kan k'afarsa da Aina'un ta mitstsike. Nuratu kuwa hannu ta saka ta dungure masa kai tare da fad'in, "Wallahi kar ka kuma ka kai hannunka jikina." Da mugun gudu Sarah ta iso wajen ta d'auke Aina'u da gigitaccen mari, sannan ta kuma d'aga hannu ta zabgawa Nuratu da Na'ima mari, sannan ta kuma d'auke Aina'u da mari don a idanunta ta mitstsike k'afar mahaifinsun. "Dan uwarki ni kika mara?" Fad'in Na'ima tana mai nuna kanta, Nuratu kuwa muciyar dake k'asa ta d'auka ta bari Sarah dashi a fuska, nan da nan fuskan ya tashi, bakinta kuma ya kumbura ya soma fidda jini don har ta wajen bakinta dukan ya samu. "Allah ya isa shegiya y'ar iska! Kuma wallahi nima sai na rama!" Fad'in Aina'u tare da yin hanyar pamfo da gudu ta d'auko bokitin da aka cika ruwa aka ajiye tayo kan Sarah wacce ke tsugunne dafe da kuncinta da Nuratu ta buga mata muciya. Sai ji tayi shaaaaa an antayo mata ruwan sanyi tun daga tsakar kanta har cikin pant d'inta. Saurin kallon gefenta tayi inda Baba yake saboda jin wani ajiyar zuciya da ya sauke, sai tayi arba dashi a jik'e shataf, don ba ita kad'ai Aina'un ta jik'a ba har da baban. Baba kuwa kallon Aina'u da Na'ima yayi yana fad'in, "Ni! Ni ko? Ina mahaifinku zaku saka hannu ku ture ni har sai da ba kai k'asa ko? Aina'u ni kika kwarawa ruwan sanyi a jiki har mitstsike min k'afa ko!" Sai kuma ya kalli Nuratu ya ce, "Nuratu ni kike saka hannu kina dungurewa kai kamar d'anki ko?" Ya fad'i hakan yana nuna kansa wasu zafafan hawaye na biyo kuncinsa. "Kuje! Duniya zata koya maku hankali." Ya fad'i yana mai fashewa da kuka tare da k'ok'arin mik'ewa. Sarah kuka take yi sosai ganin yanda jikin mahaifinsu ke wani irin rawa kuma yana kuka sosai. "Lami dan ubanki kizo ki bani abinci yunwa nake ji!" Fad'in Safwan d'an Na'ima. Saurin kallon Lami Na'imar tayi tare da fad'in, "Yanzu Lami dama yaran nan basu karya ba? Haba Lami! Haba!! Wannan wani irin wulak'anci ne. Nafa bar komai na abincin yaran nan." Marairaicewa Lami tayi tare da fad'in, "Yi hak'ura Na'ima, dama fitowa ta kenan domin in d'aura masu abincin sai ga wad'annan fitinannun mutanan sun shigo." Kallon su Na'imar tayi tare da fad'in, "Zaku fita ku bar gidan nan ne ko kuwa sai kun sake ji a jikinku?" Babu wanda yayi magana cikinsu sai ma kama junansu da suka yi suka nufi k'ofar gida. "Sake ni Saratu kije ki bud'e masu kwar gidan ki basu hak'uri ki dawo." Fad'in Baba yana mai share hawayen da suka kasa tsayuwa a idanunsa. Sarah bata sake shi ba sai da ta kai shi wajen barandarsa sannan ta nufi k'ofar gida da gudu, nan tayi arba dasu suna ta kiciniyar bud'e gidan. Hannu Sarah ta kai bayan sun bata hanya ta bud'e masu gidan tare da saurin kai guiwowinta k'asa ta shiga fad'in, "Aunty dan girman Allah kuyi hak'uri da abunda y'an uwana suka yi maku. Ku......" Katseta aunty Bilkisu tayi tare da fad'in, "Matsa mana a hanya mu wuce tun kamun nayi ball dake a nan wajen." Aunty Luba kuwa saurin cewa tayi, "Mai ya kawo maganar Ball kuma! Ke jeki gida mun ji mun yi hak'uri. Bamu hanya mu wuce tun kamun shan ruwan mu a duniya ya k'are. Wannan da muka sha ma, ya ishe mu ishara!" Ta fad'i hakan tana mai bud'e gidan. Karaf gaba d'ayan su suka yi ido hud'u da Farouq dake k'ofar gidan. Da sauri Sarah ta mik'e tana kallonsa, kallon irin na bankwana. Najma kuwa tana arba dashi ta fashe da kuka tare da soma labarta masa abunda ya faru. Wani irin yunk'uri Farouq yayi zai fad'a cikin gidan ganin yanda jini ya b'ata gaba d'aya gaban rigar aunties d'insa da k'annan nasa. Saurin rik'osa aunty Luba tayi tare da fad'in, "Bada yawuna ba wallahi ka shiga cikin gidan na, yaran da har mahaifinsu duka suke yi, to uban waye baza su daka ba a cikin fad'in duniyar nan. Farouq dama inda kake nai man aure kenan? Wallahi, tallahi ko da ace yarinyar nan ba ciki bane a jikinta, kai da ita sai dai a lahira idan da rabon auren a can. Sam wannan gidan ba gidan had'a zuri'a dasu bane." Sarah kuwa da sauri ta fito daga cikin gidan ta zube a gaban Farouq, ko kamun ta bud'e baki ya d'aga hannu ya wanke fuskanta da gigitaccen mari tare da nuna ta da hannu yace............