← Book details Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 107

Sashe 90

Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai danma bakisan me nakejiba..." Jannarht ta fada a ranta,ta karasa shigewa toilet din da kyar.

Niima tace "wai...wannan shine yankin azaba..." ki takeyi kmr ciwon a jikinta yake. Wayarta ta dauka tayi dealing num din rahma frnd dintace sosai ,bugu daya biyu ta daga, niima ta sanar da ita komi rahama tace gatanan zuwa.

A falon kuwa zuciyar Ummih ta gaza nutsuwa harga Allah Bata aminta dacewar jannarht faduwa tayiba, sannan zuciyarta batayi mata tunanin aihin abinda ya sametaba. Tana nan zaune ne a falon amma hnklinta yna ga jannarht, tasan jannarht nada matukar dauriyar ciwo, tnada tabbacin bakaramin ciwo bane zesa a gane a jikinta. Karara ta hango rama a jikinta. Hajiyace ta lura da tunanin datakeyi tacee "Me kike tunani rukayya.."

Ummih tayi firgigit tace "bakomi..."

Hajiya tace "aah da Komi...gayamin dan Allah ko nyi miki wani abunne.."

Ummih tace "sam sam wallahi hajiya.."

"Tou me kike tunani.."hajiya ta kra tmbyrta a kro na biyu.

Ummih tasauke ajiyar zuciya tace "gani nakeyi kmr ciwonnan na jannarht ba faduwar tayi..knsan zuciya da tunani tunani.."

Hajiya tayi yar dariya batare da komi yazo mine dintaba, Dan a ganinta ai Jannarht ba yarinya bace. "tou meye inba faduwarba...hmm kirabu da faduwar toilet hk natabayi kinga nan guiwar kafata seda akayi gyara.." tyi mgnr tana taba guiwar kafarta.

Ummih tace "wayyo.."

Hajiya tace "hmmm rabu da faduwar bayi, ita nata aidasauki, tinda tana iya tafiya, nifa sede aka daukkoni.."

Ummih tace "Subhanallahi.. wayyo.."

sahura tace "aikuwa hk faduwar bayi take da azaba, se kiga faduwa ba faduwaba kayi targade,...kin mnta nima na taba faduwa a kofar toilet Ummih.."

Ummih tace "au hkne fa...natuna.." Nan Ummih tasawa rnta faduwarne Amma zuciyarta bata gaskata mata hknba.

Yna isa hotel din ya shiga dakin kenan kiran daddy ya shigo wayarshi. Dagawa yayi suka gaisa cikin ladabi. Daddy ya fara masa fada kn ana kiranshi bya dauka, sannan ya kira Anwar yace Wai yna baccine, daddy yayita fada Kan wannan wani Irin baccine yakeyi, hkri ya bama daddy. Uba da da tini daddyn ya haqura. "Babana yaushe zaku dawo.."

Hammad yace "ba ynzuba.."

Daddy yacee "ba ynzuba kmr yaya..kaida akayita fama dakai ka tafi kuma.."

Hammad ya sosa keya yace "daddy garinne yymin dadih.."

Daddy tace "toufa ikon Allah..ammande da a,c kuke kwana Dan weather dinsu beda kyau.."

Hammad yace " ni yymin ddh, .."

Daddy yace "Masha allahu, Amma Ni kuma Anwar yacemin zuwa jibi inkun warware gajiyar biki zaku dawo, yace yauma kunada event ko.."

Shi Hammad bema saniba amma yace "A, daddy.."

"Tare zaku dawo ko.." daddy ya tambayeshi.

Hammad yace "no.."

Daddy yace "why..bazaka dawo kacigaba da zuwa aikinkaba knada iyali kuma ko bkson zuwa aiki.."

Hammad yace "daddy nifa bngaya maka bane amma inada hannun jari a kasashe daban daban, tin ina school zuwa ynzu business dina ya fara bunkasa.."

Cikedajin ddh daddy yace "masha allahu son..kayi dabara Allah yy albarka.."

Hammad yace "ameen sweet dad.."

"Ynzu yaushene zaka dawo tin mamanka bata fara dagamin hnkaliba, Dan yau da safennan taketa fadanta wai inta kiraka baka dagawa ga iyalinka ka bari kuma."

Shi Hammad Yama mnta ynada wata iyali, a nan. "Okay insha allahu zandawo daddy.."

"Okay..ka kira mmnkafa."

Hammad yace "tou..." Sukayi sallahma daddy cike yakeda mamakin yadda hammad din ya sake kmr bashiba, Hamdala yyma allah, dayasa masa hakuri.

Hammad Kam daddyn anwar ya kira suka gaisa, shima yy fadan kin daga wayar da baysyi, hkri kawai hammad ya basu. dasukayi sallahmah ya kira daddynshi na abuja suka gaisa sosai,cikeda so da kauna, kna sukayi sallahma. Batarw daya kira mommah ba ya ajiye wayar, danyasan babu abinda zata tareshi dashi se matsifa. Dan hk toilet ya nufa yy wanka ya fito daure da alwala yy sallah azahar da la'asar inba dolenba byason hada sallah. Istigfari yy kna yy adduarh ya shafa ya koma kn gadon yna murmushi jinshi yakeyi sakayau se dumbin kewarta da begenta da kaunarta. Wayarshi ya jawo yy dealing num dinta seda tayi ringin ta katse kna ya kara dealing shine ta katse, ya kara kira yaji wayar a kashe, Ido yabi wayar dashi, yadesan wayar akwai charji ballantana yace daukewa tayi, "maybe tana baccine..." Dayar zuciyarshi ta fada masa haka. Gaskata hkn yy ya juya ya ruguma pillow zuciya fal tunaninta ji yakeyi dmn itace yake rungume da ita, Nan tunanin dadnta ya cika masa zuciya, harga Allah yaji dadih iya dadih,Irin wannan dadin daze rinka samu akouda yaushe aidashi shar babu hawan jini babu ulcer, da duniya sabuwa, Irin wannan dadih hk a gaskia de yanzu yakejin haushin kanshi da tini ya farke gunnan yayitaci dayasan haka gun yake da dadih, gu Dan mitsitsi amma se niimar dadih a tare dashi. "Kai gaskia jannarht akwaita da ruwa..." Ya fada yna wani lumshe ido, Yna kra rungumar pillow, cikeda tunaninta bacci ya daukeshi me matukar dadih, baccin nashi yna dauke da mafarke mafarkenta.

"Iskancin da yaronnan yakeyimin a garin kaduna ya isheni wallahi tallahi..." Cewar mommah suna zaune a falo itada mama rabi da jawaheer da safara'u, da nasreen.

Mama rabi datake a hasale na yadda hammad yy tafiya be sanar da jawaheer ba sannan jawaheer tasanar da ita Irin cin mutumcin da yy mata, dataje dakinshi. Ai mama rabi dataji mgnr rntane ya kara baci. "Mtwsss...Dan Allah rabani da zancen bnza ace kina uwa amma baki, isa da dankiba..."

Safara'u tace "mama rabi dena ganin lefin mommah wallahi kaidine..."

Mommah tace "nifa gani nakeyi duk duniya bb wanda ya kaini tsanar yarinyarnan, Dan duk itace ta rabani da dana..."

Mama rabi tace "aiko itama ta rabu dashi kenan har abadan abidina...Dan ynzu shida ita sede labari.."

Mommah tace "Amma ai be dena iskncinba mama rabi, tinda yy tafiyarnan kullum Sena kirayeshi Amma saboda raini baya dagawa .... Ni wannan yaron na rasa yazanyi da rayuwata a knshi..."

Safara'u tace "wallahi duk kaidin jannarht ne..."

Mama rabi tace "tsinanniya...Daman zata mutu tsinanniya kowa ya huta...knga bb mgnr asiri kuma, Dan duk asirin datayi masa karyewa zeyi.."

Mommah tace "kuma knce insun rabu..amma knga dasuka rabunma se abinda ya kara yawa bawai ya raguba..."
Daidai nahnah ta shigo falon tnajin dukme suke cewa tsayawa tayi tana binsu da kallo one bye one. suma ita suke kallo Ummih tace "ubanki kikewa wannan kallon.."

Nahnah tace "gaskia mommah Ni natsiha zanyi muku keda mama rabi, duk abinda kuke aikatawa ina ganinku kuma ina sane, Dan hk zanyi muku natsiha, kudena haka, ance hassada game rabo takine, mommah pls ki barsu suyi zaman lafia ita da mijinta, abinda kukeyimata inhar kune akayima yayanku bazakuji dadihba, abinda bakaso ayi maka kada kayima wani, abinda kasan in anyi maka da ciwo kada kayima wani, ki tuna haqqin wani bala'ine garemu, saboda Allah baya yafe haqqin wani, yanzu meye ribarku dakuka tabata da mijinta, na tabbatrde kwalliyarh Bata biya kudin sabuluba.kuji tsoron Allah."

Mommah dake kallonta up and down tace "inkin Gama zaki iya tafiya..amma nan ba farfajiyar wa'azi bace, ki neme gun waazi sekiyi waazinki dannan kou mgna daya bata samu matsugunniba a zuciyata... jannarht cede na tsanede,bazan taba sontaba seku hadu ku tsireni.."

Mama rabi de tana zaune mamaki ya kasheta na yadda nahnah ta tsaya take gya musu mgnr bnza. "Inyeehh! Lallai yarinya wuyanki ya isa yanka...aise ki gaya mna a bayyane malama ustaziya, dakin bamu a bude, da manyan harufa, sannan da fararen bakaqe, cewa zakiyi mu yan wutane kawai mandiya.." cewar mama rabi tna mgnr tana watsa hannu. Jawaheer Kam se gallarama nahnah harara takeyi.

Mommah tace "bar munafuqa,.."

Nahnah ta girgiza kai cikeda tausayinsu tace "Ni bnce ku yan wuta baneba Dan addinina be bani dmr fadar hknba, nide natsiha nakeyi muku, na fita haqqinku, ku tuna hukuncin me hassada, sannan duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasaba, shi tashi ko zafi bazatayiba...sannaan qaiqayi koma yakeyi Kan mashekiya..."

Mama rabi tadau sallallami. "Knjimin yarinya...to tin kafin a haifeki muka sani, mu namu waiqayin, bin iska yakeyi, baze taba komawa knmuba...watoku yarannan dakunyi aure seku rinka ganin kmr kanku daya da iyayenku ko..."

Mommah tace #a hassle, "da keikashi da masheqiyar duk na hada naci malfar bura ubasu Dan ubanki...zaki ficemin a falo ko Sena miqe naci ubanki..."

Zuciyarta fal tausayin mommah ta juya tabar falon, tana hawaye, harga Allah tafi tausayin mommah, saboda ta jima dasanin ita mama rabi tana amfani ne da mommah kawai dan, biyan bukatunta, da kuma cikar burinta. "Allah ya gnr dake mommah..." Ta fada tana share hawayenta, zuciya cikeda tausayin mahaifiyarsu da kuma kaninta hammadu,hk ta shiga car dinta taja tabar gidan,zuciya cikeda haushin daman batazoba, Amma ta wani fannin zuwan zefi amfani, Dan zata yawaita adduarh a kn lamarin.

Mommah tace "kngani ko...har yayannawa duk tabi ta asircesu..."

Mama rabi tace "ga zahiri na gani...oh Ni rabia'arh...qalu innalillahi wa'inna ilaihirraju'un...wannan mutsiba dame yayi kama..."

Jawaheer ta fasheda kukan munafurci, Wai kowa ya tsaneta. Nan mommah ta dukufa Tana bata hkri, da kyar aka samu tayi shiru tana share hawaye,. Mommah ta kara Kiran num din hammad nanma yaki dagawa seda tayi masa kusan miss call goma Amma be dagaba lokacin mashi bacci yakeyi. A hasale mommah tacee "kungani kou ..na kara kiranka ynzu be dagaba...wanishin bazan tsinewa yaronnanba yabi duniya kowa ya huta..."

"Aaaaaaaa...karki fara, ai ita abun farin cikintane," cewar safara'u.

Mama rabi de ta rafka uwar tagumi ta rasa ta ina zata bullowa lmrn, kwata kwata knta ya kulle. Mommah ma bakin ciki kmr ze faso zuciyarta ya fito fili hk takeji,ji takeyi kmr ta tsine masa yabi duniya, Amma kuma seta tuna ita takeda asara, Komi na rayuwarta ya damalmale, gashi tini daddy ya dena mata komi, baya kulataba shi be saketaba, Amma komi ita take yima knta, hatta da kyn abinci ita take siya da kudinta, se abubuwan sukayi mata yawa, ada tasaba ganin komi enough Amma ynzu shirune lamarin, sede in komi tasiya da kudinta, shi kuma daddy yayi mata hakanne saboda ta gane kuranta, Amma Abu yaci tura.

Tnks for the comments. Grp 1 da grp 2 ngd sosai da sosai, normal ma tnks, comments nasawa ku samu typing dayawa.
Chapter 90 · 0% Book details