← Book details Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 107

Sashe 9

Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya suka kara kwashewa dashi. Rnrde sunsha hira, zuwa yammaci kowa yanufi gidanshi.
[10/30, 3:47 PM] +234 803 727 9133: 🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯
*IN SO CUTA NE* 14
🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯

*HAQURI MAGANI NE* ❤️

Story pruducer and directer SA'ADATU BINTU ABDULLAHI✍🏼 (marubucyr Boyeyyen al'amari)

Writing farhana fahad maman namlah✍🏼
*YAR MUTAN NIGER*

Littafin na kudine game bukatar normal 300 VIP 600 trnsper kou card mtn ,08033368013 . Trnsper 0542703718 saadatu Abdullahi gtbank bank.inkin tura ki nunamin alama ta lambar dake sama.

*ga masu bukatr cigaban littafin Bazan taba sanshi ba suyi rijister din in so cuta ne zasu samu littafin a saukake.* fans kuna nunamin 1love nagode.

BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHIM

FREE PAGE 14

Ranar sunday .byn tadawo daga training. Shiryawa sukayi tsaf dukkaninsu da hijjb ummih na zaune a bayan motar sahura na zaune a gaba janan na cinyarta. Jannarht ce tayima motar key yayin da baba me gadi ketayi musu fatan dawowa lafia.

A wani katon gida tyi hon me gadin na leqowa yaga motarta ya bude mata ta danno kai cikin gidan .parking tayi a tare suka fitou da sahura. Jannarht ce ta budewa ummih ta fitou tana gyara hijjb dinta.

Murmushi ummih tayi tna bin kou wani bangare bangare na gidan da kallo.

Yayin da harabar gidan ke cike da jama'arh masu kawo temako wasu kudi wasu abinci.

Kai tsaya office din shugaba suka nufa alhaji khasim A shureem. Sun isa amma sunga office dinshi a rufe zasu juya kenan su nufi wani office din ya iso inda suke, yace "yau kune a tafe rukayyah da yarta.." mutumin dattijone akwai cikar kamala a tare dashi amma shekarunshi sun ja.

"Eh ranka ya dade..aida da bamu gankaba har zamu shiga office din assistant."

"muna can munata fama da jamaarh aina hangoku.." yy mgnr ynasa key ya bude office din suka shiga ciki akwai kujera 3sttr zazzaunawa sukayi shi kuma yazauna, a kn 1sttr yna fuskantarsu.

Gaisheshi sahura tayi hk jannarht ma zamowa kasa tayi ta tsugunna ta gaisheshi fuska sake ya amsa "lafia lau jannarht allah yayi albarka..muna ganin dawainiya mungode, allah yabada lada kullum cikin hidima kike damu dukda a ynzu baki a tare damu"

Murmushi tayi tace "Abih kadena godia nice ya cancanci inyi muku godia kune nifa tin bnsan Ni waceceba abih ku kuka temaki rywata.."

Murmushi khasim yayi yace "hkne jannarht samunki alkhairine a garemu..Allah yy albarka Allah ya tsare dukiya"

"Ameen suka amsa dashi dukkansu.

"Rukayyah diyar taki ta nijer tana zuwa kuwa.."

"A'ah shugaba.."

Sunkuyar da kai yayi Kasa yace "kada ki damu kinji kou..ita macece seta nemeki a duk inda kike ai diya bata yarda uwarta tazauna lafia.."

"Hkne shugaba shiyasa akace kouda yaya ba nka bane ka rikeshi..seka haifi naka baka moreshiba.. sekaga ka mori na wani..dukdade Hausawa sunce tsintacciyr mage bata mage nide tawa tafiyemin komi a duniya."

Murmushi khasim yayi yace "rukayyah kenan..allah kadai, yasan dalilin dayasa ya jarabceki da soyayyah jannatul fiddausi soyyarta a rnki bazan mantaba tin rnr dakika jita a hannunki"

Murmushi ummih tayi tace"wlhy shugaba, ina sonta fiye da kowa a duniya..dukda bnsan Ni waceceba amma a knta inajina kmr itace kow nawa"

"Hk allah yake lamarinshi..Ke kina can kina jin dadinki .. gatanan kina ganinta, kullum, mukou nan se hkri muketa fama dashi danma, ba a wata sekun kawo mana ziyata.." jim yayi knshi na kasa kna yadaura, dacewa, "kinsan jannarht zuciyace ta kowa dake gidan marayunnan ..bazan fasa gaya mikiba rukayyah wlhy muna cike da kuncin rashin sa jannarht a ido a kullum..ada kinga, munsaba kika rabamu..bansan yaushene zaki gaya mana dalilin hknba." Ya karashe mgnr yana jan dogon numfashi.

Cikin natsuwa ummih tace "Nasan hk shugaba a gafarceni..kuma bazan dena godiyaba daka, zama daya daga cikin wadanda, suka amshi bukatata dawuriba allah yabar zaman, amana..insha allahu shugaba lokacin daza kusan dalilina yana nan zuwa..don allah kuyimin kyakyawar fahimta. Nyi hkn ne saboda soyayyata ga jannarht..Kasan yadda allah yasamin, sonta ga zuciyata."

Murmushi khasim yayi yace "muma muna sonta ai..kullum mgnrki dyace jannarht ce dalilinku na barin gidannan, amma an gaza gaya mna meyasa, jannarht tazam dalilin, ...ehhye rukayyah"

Murmushi ummih tayi tasan koume zatace bazasu fahimcetaba.

Jannarht de tana zaune knta na kasa tanajin maganganunsu a zuciyrta, tace "a lokacin daka wulaknta abu a lokacin wani nemanshi yakeyi, inya sameshi kuwa ze tarairayeshi kmr kwai ..Hmm allah kenan" karamar wayrta dake hannunta tashiga dannawa.

Murmushi khasim yayi yana kallonta yace "Hmmm rukayyah kenan.. shi jibril din kinajin labarinshi"

"A'ah shugaba.."

"Watou de inde jannarht na nan shikenan ke sharr kou.." yy mgnr cike da zolaya.

Murmushi ummih tayi.. "yakamata mu zagaye sauran mu gaisa dasu." cewar ummih. A tare suka mike dashi suka shiga zagaye office din kowa suka gaisa duk inda suka shiga cikin kjin dadih ake amsarsu kai dagani kasan akwai fahimtar juna, a tsakani.

Daga karshe suka shiga zagaye bangaren yara da mnyan dake cikin gidan marayun duk inda sukabi sede kaji ana kama sunansu musammanma jannarht uwar jamaarh. Daga karshe bangaren nakasassu suka nufa cike da tausawa jannarht ke kallonsu hawaye na zuba a idanuwanta tana boyewa tana gogewa gudun kada ummih tagani. Tausayinsu fal cikin ranta tunaninta dayane "suma haka zasu tashi basu san kou su wayeba..basusan meye dumin uwa da uba ba..basu san ya soyayyar iyaye takeba..Hmm" hawaye wani na bin wasu a kuncinta. Sunzo gifta wani gado wata yarinya makauniya ta rikou mata hijjb jin an rike mata hijjb tajuya dan ganin kou wani abune idanuwantane suka sauka a kn yarinyar da tun tana jaririya da aka tsintota ita akabamawa ita tasa mata suna . Yayin da taci sunan ummih a ynzu zatakai 10yrs "mamana.." jannarht tace ta dawo tazauna a kn gadon yarinyar takai hannu tana shafar fuskarta, tce "anty jannarht tin tini nakejin.kamshinki .."

Murmushi Jannarht tayi hawaye na kwaranyowa a idanunta "nice mamana..inata raba idone bngankiba naga an chanza miki gado yau."

"Eh jiya mama salame ta chanzamin..saboda muna fada da fahima ta kusa da gadona kingama ta yakusheni a fuska.." ta karashe mgnr tana lalubar fuskarta, ta nuna mata yakushin da fahima tayi mata a fuska.

"Kai kai kai.." tace yayin dataga uwar yakusar duk ta yakusheta abunka da farin mutum kai kace konewa tayi. nan da nan Tausayinta ya mamaye zuciyarta Se ganin hawaye kakeyi sharr a kn fuskarta, hatta sahura Seda tayi hawaye, allah yaso basa kusa dasu ummih da khasim suna nesa da inda take Sahurace de tsaye kusa da ita. "haba janan banace kidena fadaba." Tayi mgnr still hawaye na safa da marwa a kn kuncinta.

"aini bani, na tsokaletaba."

"Nasani..ammande kirinka hkri kinji kinga masu sunan nan naki sunada, haquri bakiga ummihnaba"

Hannu takai tacigaba, da shafar fuskarta tace "tou anty jannarht..kullum inajin fuskarki kmr da anty jannarht bakya tsufa..Amma naji kmr Kina kuka"

Murmushi ne ya subucewa jannarht yayin da hawaye yabiyo byn murmushin. "Hkde kikace mamana..Ni ba kuka nkeyiba"

"Hkne mana Anty jannarht..harynzu bakiyi, aureba kou anty jannarht.." cike da tausayawa tyi mgnr.

"Eh bnyiba janan.."

"Tou kiyi adduarh anty nima kullum cikin yi miki nakeyi.."

"Tou janan dina nagode.." tafada hadi da mikewa ta manna mata kiss a goshi tace "ni zan wuce.."

Kamo hannunta tayi ta rike a nata tace "banason ki tafi ki barni"

"Nima banason in tafi, in barki..amma nace kidawo gidanmu kince A'ah"

Sakin hannunta tayi tace "A'ah nafison nan saboda kawayena"

Wani kayataccen Murmushi tasaki, tace "Tou kingani..nide zan tafi swry pls kirinka karatu sosai da sosai"

"Tou anty jannarht allah ya tsareki A duk inda kike"

"Ameen mamana same 2 you."

"Ameen Tnks..Anty jannarht zaki siyomin yar bebih?"

"Eh zansiyo miki janan me gashi ko.."

Murna tashigayi, tace "eh megashi.."

"Tou insha allahu next time zan taho miki dashi.."

"Tou na gode allah ya kara budi. allah ya tsare hnya.."

Amin suka amsa dashi,

tajuya ta tafi tana waiwayonta. sahura ta bata hankacib ta amsa ta goge hawayen dake fuskarta.

Suka iso inda ummih suke kallo daya tayi mata tagane tayi kuka. Girgiza kai kawai ummih tayi.

Byn sun gama zagayen suka dawo office din khasim din. Frij yabude yadauko musu, ruwa mesanyi na faro da peach apple drink.

Ruwan jannarht takai hannu tadauka data kafa kai seda tashanyeshi tas ta ajiye robar. Ta jingina da bayan kujerar idanuwanta a rufe hannunta na kn goshinta. Ummih na kallonta . Peach din mommy ta bude tana kurba kadan kadan. Hk suhurama peach din tashiga sha ita da janan.

Gyaran murya khasim yayi ummih ta dago ta kalleshi, yace "rukayyah yakamata yarki tasan matsaya , muna kyautata zaton zmanku a tare, ba tabarbarewar tarbiyarta bane..A kokarta tin bama zarginki tasamu miji tarufawa knta asiri, tayi aure."

Dogon numfashi ummih taja tace "Tou shugaba insha allahu zamu cigaba da addarh."

"Eh muma munayi Amma ki kokarta."

"Tou shugaba."

Jannarht de a kullum intaji zancennan, takanji wani iri domin tana ganin kmr shugaba yana ganin ummih ce ta hanata aure.

tin safe se yammaci suka fara haramar komawa gida, sallama sukayima kowa suka rakosu bakin motar jannarht tabude but din motar kayane makil bandir bandir din atamfofi da lesis da shaddoji da pantis na yara dana mnya hadda kyn jarirai. Sawa tayi mazan gidan suka fara fitar da kayayyakin suna kaiwa ma'ajiyah . Godiya suka shigayimata taja abih gefe tagaya mishi tayi trnsper din 5million a account dinshi a biyawa marayun bukatunsu dasu abinda babu a asibitinsu tace a siya. Sannan tace abih yadauki 1million nashine.

Godiya abih yashigayimata harda, hawayenshi. Murmushi kawai jannarht tayi a zuciyrta, tace "dazan samu abinda yafi hkn zan kyautata fiye da hkn."

Motarsu suka shiga jannarht taja motar sukabar harabar gidan marayun.

Tunani tunani fal ranta driving takeyi amma hnklinta, na wani gefe daban

Karantarta ummih keyi tsaf tagano inda gizo ke saka . Dman hkn take kasancewa a duk lokacin dasukaje gidan.

"Subhanallahi.." !! Ummih ta furta yayin da sauran kadan motarsu ta shigewa katuwar tifa Firgigit Jannarht tadawo hnklinta tayi saurin kaucewa tifar.dabadan allah ya tsareba yau dasede labarinsu.

Da temakon allah suka iso gidan. Kai tsaye upstairs ta haye a falonta ta yada zango.
Chapter 9 · 0% Book details