← Book details Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 107

Sashe 68

Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aah bamu dashi..Amma kwara muje can inba hkba se abih ya mayarda yarinyarnan, kuma hakan barazanace ga rayuwarta..Wlhy nasan halin rabi zata aikata abinda yafi hkn."

Mmn iburahim tyi Jim tna nzarin klmn Ummih kna tace "Aita Allah ba tasuba Ummih.. baride mu isa gidan se muyi shawara..knga me knki baki kimtsaba. "

Suna isa gidan a falo suka zazzauna, zuwa lokacin sahura ta dawo dmn batanan taje siyo alayyahune, tadawo taga bata ga ummihnba,,, se gashi ta gnsu da anty jannarht, zuciyrtace ta bata babu lafia,. "Hada Kayanki sahura nima ki hadamin nawa wanda de kksan zamu bukatar.." cewar ummih, kai dajin yadda tke mgna ksn hnklinta a tashe yake,. Sahurade juyawa tayi tabar falon bynta goyeda janan, ta nufa bedroom din ummih jiki a sanyaye,.

Mmn ibrahim ta numfasa tace "ynzu ina zakuje..aurenfa dake knta.."

Ummih tace "nijer zamuje mmn ibrahim ..shine mafi alkhairinmu, aure kuwa daga bya ma nemi takaddarta..inna zauna a gidannan da matsala.." Ummih ta fada tana zirya a falon.

Mmn ibrahim tace "hkne kuma..ammande se nke gnin nijer ai yy nisa kuma knga ma zamani na coronar Nan, gashi ba kowa kika saniba a can babu wani naku na jini,,,meze hana kuje kano inada yaya a kano batada miji, mijinta ya rasu,. sunanta hajiya saudat sannan yaranta duk sunyi aure se dayar cema aurenta ya mutu kwanan Nan saboda rashin haihuwa bazata wuce age mate din jannarht ba.. hajiya saude batada problem kwata kwata tanada dadihn zama, Dan Allah kuje can kafin komi ya lafa Allah shi yasan yadda zeyi da wadannan mutanen..ayita adduarh."

Ummih taja dogon numfashi tace "hajiya bawai naki shawararki bne Amma dakin bari kawai munje nijer din .."

"Hba Ummih nijer yy nisa wlhy ga kno ai yafi, Kuma knga bama ya zuwa kno ballantana ince kou kina tsoron kada wata rna su hadune ...inbadewai ba a zama daya bane ba tou Ni a tunanina ai anzama daya ummih,.pls kubar mgnr zuwa nijer dinnan kuje kno din Dan Allah.. na roqeki...Komi yy zafi mgninsa Allah..sannansu hajiya rabine kou wacece..basu isaba suyi abinda Allah be hukuntaba...wannanma ai dansu sukasa a bala'i in basu saniba,. Dan Allah ummih kouda kunje kanon ki kwantrda hnklinki ki natsu pls, itama Jannarht din seta samu hnklinta ya kwanta ta wani bangaren Allah yasa mu dace...Dan Allah Ummih na roqeki kada kiyi gaddama kn mgnr zuwanku kanon nan pls kice Tou kawai insha allahu hakanne alkhairi.."

badan Ummih tasoba mmn ibrahim ta kasheta da kalamai dole ta amince da zuwa kanon, Nan da nan mmn ibrahim ta kira hajiya saude ta sanar da ita, cewar baki suna tafe kuma zasu zauna for the long time, hajiya saude tanadason mutane tce "alhmadulillah...Allah ya kawosu Lafia.."kna suka katse wayr,.

Ummih tace "ai nauyin zeyi musu yawa hajiya gani ga jannarht ga sahura ga janan..aikou knga munada yawa..."

Mmn ibrahim tce "hbade ba wani nauyi..sunada Halifa sosai sannan yaranta yawanci duk mazane..in kuna ganin bakusan zama gidan inada gida a kano seku zauna can.."

Ummih tace "bakomi zamu zaunadin hajiya mungode da karamci Allah yabar zaman tare,. "

"Ameen ummih.. bkm ai anzama daya se haquri kuma..Allah de ya kawo sassauci a cikin lmrin..Amma ummih kar a tsananta knsan rabo yna kisa."

Ummih tce "hkne hajia ..mungo mungode Allah ya raya zuriarh."

"Ammen Ummih.." cewar mmn ibrahim.

Jannarht ma tayi mata godia,. Tini aka loda musu kynsu tas a cikin daya daga cikin motocin dake gidan, komi dazasu bukatr sun tafi dashi, suka rufe kou ina a gidan kna suka bama mmn ibrahim din key din gidan. Komi suka bar mata alhaqin kulawa dashi a hannunta,. fitowa harabar gidan sukayi, har bakin motar mmn ibrahim ta rakosu suka shisshiga tayi musu fatan sauka lafia kna dreva yaja motar sukabar gidan,. Dukkanin masu aikin gidan na alhinin tafiyar tasu da rna tsaka, mmn ibrahim ta dauki nata car din ta nufa nata gidan, zuciyarta fall tausayinsu musammanma jannarht Dan ita tafi bata tausayi, rayuwarta na cikin garari,ta dade ba aure, anyi auren babu kwanciyar hnkli , aure ya zama abinda ya zama,,uwar miji ta hana zaman Jin dadih..Allah wadaran halinta"cewar mmn ibrahim.

Byn sun dau hnya harsun wuce gadar kawo Ummih da jannarht damn suke a zaune a baya, sahura na gaba itada janan, Ummih ta ta kalli jannarht din tace "miqamin wayrki..." Tyi directing dinta, jiki a sukwane jannarht ta mikawa ummih wayr, amsa tayi ta kashe wyr gabaki daya ta sata a hand bag dinta, kna ta maida idonta ga kallon hanya, jannarht kuwa ita ta kureta da ido, kna ta koma tyi Relaxing a kn kujerar tana maida numfashi, hadi da tausayin knta wato itade a hk rayuwarta zata kare cikin tashin hnkli tajima batayi aureba, ynzu tayi auren Amma tana nadamar Daman batayiba, .dukda batasan meke faruwaba Amma tanada tabbacin akwai wani mummunan abu dayasa Ummih taje ta daukkota gashima har zasu bar garin, tasan bkrmin Abu bne zesa Ummih zartar da wannan hukuncin kai tsaye,. Allah take roko kn ya kawo mata sassaucin lamarin,.

Kouda ya shiga side din anwar Nan hira ta kacame tsakaninsu, haka kawai yakejin yawan faduwar gaba a Kai a kai, seya shiga ambaton sunan Allah. Time to Time yna duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunshi, zuciyrshi na kanta,. Bayan sunyi sallarh azahar yayima anwar sallamarh, har bakin car Anwar ya rakoshi seda yaja motarshi yabar gidan kna anwar ya juya ya koma side dinshi,.

Seda ya tsaya yayi musu tsiyayya me tarin yawa na kayan ciye ciye dayake yasan tana period har seda ya biya yase mata pad, kna ya dauki hnyar zuwa gidan,. Kouda yy packing a cikin gidan Allah Allah yakeyi ya fita yaje ya ganta, zuciyrshi na mararinta, se yakejin kmr yy shekarane be gntaba dan fitarnan da yayi,. Fitowa yy hannunshi rike da ledojin ya nufo falon gidan, Haka kawai yaji bugun zuciyrshi ya tsananta adduarh yashigayi Allah yasa alkhairine...

Kai tsaye ya tura kofar shiga bedroom dinta, "beautiful anty narh.." ya fada dai dai ya danno kai cikin dakin, Nan ya sauke idanuwanshi a kn gadon, wayam, cikin natsuwa ya shiga raba idanuwanshi a dakin, haka kawai yaji gabanshi na faduwa fiyeda tunanin me karatu, watsar da ledojin hannunshi yy nan qasan dakin, ya nufa bathroom, tura kofar yy yashiga yaga wayam, hnklinshine yy matukar tashi, gashi tinda tazo gidan bata taba fitaba inbawai sun fita tare bane, "Antynarh
...! Antynarh...!! Antynarh...!!! Dan Allah kina inane ki fito bnason irin wannan wasan zuciyatarh zata iya fashewa..." Nan ya shiga zagaye dakin yna sambatu idanuwanshi sunyi luhu luhu, hatta drowers din dakin seda ya bubbudesu, Wai kou nan ta shige, saboda tsabar tashin hnkli bema lura da cewar bb akwati dayaba,. Tashin hnkli wanda ba asa masa rana! Hnklinshi a matukar tashe ya fito falon gidan hannunshi rikeda wayrshi yna dealing num dinta se akece masa is not reachable, hnklinshi a matukar tashe ya jefarda wayar a kasan falon, kna ya nufa kiching yna kwala mata Kira, nanma wayam, bedroom's din gidan Kam babu inda be shigaba cikin lokacin kankani ya hargitsa gabaki daya ilahirin gidan, har harabar gidan ya fito yna nemanta lungu da saqo kmr wani tababbe se y kwala mata kira, ykeyi.

Me gadi dake zaune yaganshi ya fito hnklinshi a matukar tashe se faman dube dube yakeyi, krsawa yy gareshi yace "sannu alhaji lafiya de kou..."

"Ina matatarh!!..." Hammad ya fada cikin daga murya,.

Me gadi jikinsa na rawa yace "nide naga wasu mata dattijai sunzo sun tafi da ita hardama akwati naga ta dauka ita hajiyar ansa a motar nashama tafiya zatayi...."

Zuciya na tafasa rai a matukar hargitse hammad ya watsama me gadin wani irin gigitaccen mari,,,,tsabar azabar da me gadin yaji na Marin seda ya dena ji na wasu yan dakiku,,,, "what me kake fada...matar tawa ta fita zuwa ina....tou wallahi seka nemomin matata tinda bada izinina ta fitaba..." hammad ya fada a rikice yyin daya cakumo masa wuyan rigar baba me gadi, jikin me gadi har rawa yakeyi yace "alhaji kayi hkri...na tuba..."

Sakinshi hammad yayi, tsabar bacin rai idanuwanshi sun koma red sosai, sun kumbura suntum, tsabar bugun zuciya kmr zuciyrshi zata fito fili, nuna me gadin yy yace "inhar nadawo gidannan ba tare da matataba, kayi kuka da knka Dan wanda yake lahira seya fika jin dadih!" Yna fadar hkn ya juya ya nufa cikin gidan,.

Me gadin kuwa fashewa yy da kuka yna fadin "shikenan anjamin matsifa..Aikou me xakayimin tinda ina samu bazanbar gidannanba..." Ya krsa ya zauna kn bencinshi ya sharce majina yna hawaye,.

Car key dinsa ya daukko kna ya fito compound din hannunshi rikeda wayrshi still yna dealing num dinta amsar dayace kmr dazu nor reachable, Daman kouda ya fita gidan dzu wayarta na airplane mode, hnklinshi a matukar tashe ya shiga motarshi yy Mata key me gadin yabude masa get ai kmr ze kasheshi ya fice daga gidan, da temakon Allah ya isa gidan Amma ya buga tukin gangance,. Get man ya wankale masa get ya shigo, kou packing din kirki beyiba ya fito daga motar ya nufa hnyar shiga falon gidan me gadin ya biyoshi a guje yna fadin "alhaji ina wuni..."

Ai hammad bata amsa gaisuwarshi yakeba hannu yakai ya murda murfin kofar yajita a rufe kwankwasa gidan ya shigayi yna kwalawa jannarht kira... "Anty jannarht pls ki bude kofar nine meyasa kika fito batare da izininaba..pls ki bude kofar inason in gnki I miss you my princess..."

Cikeda tausayawa get man din ke kallonsa yace "alhaji ai basanan basu jima da tafiyaba..muma sede mukaga ana sanya akwatina a cikin but... batare damunsan xasuyi tafiyarba."

Idanuwanshine suka kara rufewa zuciyrshi ta kara tsinkewa yynda jikinshi ya dau rawa hnklinshi ya kara tashi cikin tsawa yace "gidan ubanwa sukaje...Ina sukajemin da matata Ina zasu kaimin matata...." Jikin me gadi yahau rawa yace "Wlhy bamu saniba Amma da dukkan alamu sunyi tafiya ne..."
Chapter 68 · 0% Book details