← Book details Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 107

Sashe 78

Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa hammad yayi dukya qosa yabar gun. suhaim ya biyoshi suka isa bakin car din ya bude ya daukko pot dinshi hammad ya shiga yyma car din key ya tayrda ita a hnkli a hnkli yake juya kan motar kmr byaso.. dai dai yazo fita car dinsu jannarht tasako kai dole ya koma da nashi car din dan me shigowar yasamu dmn shigowa,,, packing yy dmn dukta qosa saboda kallon da Deen ke binta dashi. a hnkli ta fara ziro lallausar kafafuwanta. sauranma suka fito..

Hk kawai hammad yabi yammatan da ido niimace kadai yasamu dmr ganin face dinta, Amma sauran sede bayansu ya gani, besan sanya yabi bayansu da idoba...

shi kuma Deen ya gyara packing din motar ya fito ya bisu a baya yana karewa Bayan Jannarht kallo, a zuciya yace "Allah yy halittarh.." krsawa yy gaf da jannarht, se wani shishige mata yakeyi ita kuma tana kauce masa.

Bynta Hammad yasamu dmr gani hk kawai yaji gabanshi yy mummunan faduwa, ya tsinci knshi dason ganin fuskarta danse yaga ta baya da ynayin tafiya taso tayi kama da Jannarht dinshi. "Meze kawo jannarht dinka Nan.. Kuma jannarht batasa gyale,sannan tna matar aure ai bazata yard namiji yyta manne mataba..." wata zuciya ta gaya masa hakan. Nan da Nan tunani tunani suka dabaibaye zuciyarshi..gyara packing din yy Dan yaji jikinshi yy sanyi bayajin ze iya driving dole se jikinshi ya koma normal.

Suna shigowa gurin, kallo ya dawo kansu musammanma jannarht se wow wow wo kawai akeyi yadda kasan motar ambulance.😛
Karasawa sukayi suka zauna a kayataccen gurin da aka tanada dansu. Camera man kuwa Nan ya samu dmr aikinyi da video man, ai abun nema ya samu.. jannarht Kam duk jinta takeyi a takure kmr tana tsirara take jinta abinka da ba asaba ba.

Shigowar tasu a kn idon anwar yaganesu niima, da aisha, bin jannarht yy da kallo, se yga kmr ita Amma yasan ba ita baceba Dan anty jannarht batasa gyale,.. "Amma kuwa kmr ta bace..." Anwar ya fadaea zuciyarshi. wayrshi ya dauko yayi dealing num din hammad danya shaida masa yaga wata me kma da jannarht. Hammad yna ganin call din tsuki yy ya danna masa busy, yana gani ya kara kira ya kashe wayar yace "ko ubanme zanyi masa oho.." yasaka wayar a silent, Yayi bending a kn seat din motar zuciyarshi fal tunanin matarsa,se yji tunanin ya dawo sabo dal a fagen zuciyarsa.."I miss you wife.." ya furta kmr zeyi kuka.

Akace niima ta fita tayi jawabi a matsayinta na babbar qawar amarya..jikintane yadau rawa Dan ita bata iya Irin wannan zawabin cikin cinkoson mutane.nan ta fara rokon jannarht kmr zata kwanta mata kn ta ceceta ta fita a madadinta.. "a cikin dumin jamaarh nan.." jannarht ta tambayeta.

"Eh Pls Dan Allah ki temakeni kmr yadda Allah ya temakeki kk fita pls,,ki fiddani kunya ..Wlhy ban itayawa,se jikina yadau rawa..ammake nasan zaki iya tinda you are a doctor kin saba jawabai, nikam bn saba ba,...."

Dukse tabawa jannarht tausayi, a duniya babu abinda bazata iyayima niima ba saboda sun temakesu a lokacin dasuke bukatar temakon. "Dan Allah sister pls.." niima tace tana kamo hannunta.

Safiya da Aisha ma suka tayata rokonta,dansun sam da ganinta akwai ilmi a cikin kanta. Dukda suma sunadashi amma ba kmr itaba.

Jannarht tace "okay.." Nan niima taji dadih. "Thanks dear.." Jannarht tayi smiling tace "bkm..amma hk zan fita da dan gyalennan.."

Niima tace "kinyi fine wlhy shigarki batayi komiba frnd.."

"Inajin kunya..." Cewar jannarht. Nan sukaji m.c ya kara yage murya yna kirawo sunan babbar kawar amarya. Jannarht ce ta miqe jiki a sanyaye tafara takunta na qasaita kmr dawisu ta isa tsakiyar filin, duk inda tayi masu video da masu hotuns suna biyeda ita... tana futowa tsakiya filin kallo ya dawo gareta, shi knshi m.c seda ya girgiza da kyaunnata,mace kmr mtn aljannar...

Suhaim ya taba Anwar yace "ka ganta ko...wallahi itace wadda nagani jiyannan da da bebs dinmu na jiya sukazo..yaka gnta kmr matan indiayawa yaseen ta hadu iya haduwa.."

Anwar da yy mutuwar zaune yace "kai wannan kmr anty jannarht..."

Cikeda rashin fahimta Suhaim yace "eh sunanta jannarht, ashe kasanta Allah yasa yar uwarkuce aini da adai dai wallahi.."

Anwar Kam duk zuciyarshi ta tsinke ..."Kai wallahi kmr tayi yawa..." ya Ciro wayrshi yayi dealing num din hammad amma beyi picking ba... Cikin harshen turanci ta fara jawabi da coll voice dinta me rikita zuciyar me sauraro.

Hammad tayarda car din yy yabar harabar gurin zuciyarshi fal tunani tunani.

Muryarta ta daki dodon kunnen anwar kara gywale Ido yy tabbas babu makawa anty Jannarht ce, rufe idonshi yy ya bude ya kara tabbatrda ita dince tana mgna wushiryarta kasa da sama suna bayyana yyinda haqorinta na maka ke wani haske wal wal, yna haske gurin...

Jiki na rawa Anwar ya mike ya fito daga cikin gurin ya tari napep yace a kaishi hotel din Dan yasan zuwa lokacin hammad ya isa hotel din.

Be kaiga karasawaba ya juyo danya amsa key din room dinshi da gun anwar... Tinda ya shigo gurin yake jiyo murya kmr tata jikinshi har yna rawa yy packing car din ya fito ya kraso inda yake jiyo muryar tata,Amma me baya hangota mutane duk sunbi sun rufe gun,se video sukeyi mata danma akwai security, da wanima seya kaiga isa inda take.

Gabaki daya ilahirin jikinshi rawa yakeyi yyinda bakinshi ke kakkarwa, yna ambato sunanta cikin zazzaqar muryarshi...runtse idonshi yy ya bude a zuciya yace "ya rabbih kasa ba mafarki nakeyiba Allah yasa itace...ya rabbih kasa qarshen whlatace.." Tutture mutane yashigayi danya samu ya dangano da inta take. Segashi tsundum a tsakiyar filin,...wayyooooo...ido ya zuba mata tabbas itace wadda yagani dazu kuma jannarht dinsace..."hasbunallahi wani'imal wakeel.." ya furta yna zubo mata ido kyawunta ya isa kyawunta na rudashi yna gigitashi,bkrmin kyau tayi masaba kmr ya sureta ya gudu... Itama shidin ta zubowa yyindata tsaya da mgnr datakeyi saboda tsabar firgici seda abun mgnr ya fadi a hannunta, ta zubo masa ido ji takeyi kmr a mafarki take ganin black dinta daf da ita... Nanfa kallo ya dawo knsu wanda ke zaune ya tashi tsaye Dan ganin meke faruwa, mc yazama dan kallo...su Aisha da ni'ima da safiya suka matso kusa kusa Dan ganin meke faruwa, ango da amaryama ba a barsu a bayaba. Da Alhaji suhaim.

Kwallah ne suka shiga zirya a kn kuncinshi na murnar ganinta, Nan ya shiga qoqarin karasowa inda take security suka riqeshi ya kwashe ya karasa gabanta ya kamo hannunta, ya tsugunna a kn guiwowinsa, tabbas itace ba wataba. Dago idanuwanshi yy yasauke a knta still hawaye na zirya a kn kuncinsa. "Jannarht..." Ya furta hawaye na yawaita a kn kuncinsa.

Nan masu video suka karu kowa se ciro wayarshi yakeyi yna musu video,camera man da video man Ma Nan suka kara kwazo gun aikinsu..shikam suhaim abun mamaki ya tsaya kallo dukya daburce kanshi ya kulle.. hakanya kasance a bangaren niima da qawayenta.

Kamo hannayenta yy duka biyu hawaye na zirya a kn kuncinshi yace "Ina kika shiga my wife..kina barni da dumbin soyayyarki da kaunarki..dana mutu tabbas da sonkine yy ajalina...ina sonki fiyeda yadda uwa take son danta..Ina sonki fiyeda yadda nakeson kaina..ina sonki fiyeda yadda nakeson rayuwata...inasonki!..Inasonki!!,,..inasonkiiii!!...I can't live without you...Ina sonki flower..." Ya fasheda kuka me tsanani yyinda hawayen ke sauka a kn hannunta.... Runtse idanuwanta tayi tanajin bugun zuciyarta na qaruwa, yyinda hawayen shi dake dika a kn hannunta masu zafie,, zafinsu harga qahon zicciyarta..bude idanuwnta tayi tar a kn kyakyawar face dinshi, cikin lokaci kankani ta hango ramarshi Kiri kiri ta bayyana. zubawa kwayar idonshi,ido tayi..babu abinda take gani se tsabar tsantsar kaunarta da begenta...idanuwantane suka cika da kwallah ganin masoyinta na hawaye,, Kan kace kwabo hawayen sun fara sintiri a kn kuncinta unexpected...

Rungune hannunyenta yy a kirjinshi,cikeda shaukin da bakina baze iya misaltashiba.. "Nasan kina sona..Pls kice kina sona..." Hammad yace still hawayen soyayya na zirya a kn kuncinshi. Itama hawayen takeyi bakinta ya gaza buduwa ballantana tayi mgna...

Nan jikin kowa dake gun yadau sanyi, guri yadau tsit kmr anyi mutuwa, suna kallon zallar ainihin masoyan asali.....

"wallahi na rantse da ubangijina ina sonki... I love you my love know because of who you are..inasonki..ina sonki..fiyeda yadda duk wani masoyi keson abinesonshi..ina sonki fiyeda yadda me rai yakeson ran dake jikinshi....you are my breath!..." Hammad ya fada yna kara fashewa da kuka hannunta rungume a kirjinshi, "Dan allah kice kina sona koda sau dayane..pls kice kna sona kada in mutu banji kin furtamin kalmar I love you ba...plssssssss.....kice kina sona, koda shine kalmar karshe dazanji a rayuwata, inhar nji kalmarnan daga bakinki zanyi mutu ina alfahari da kalmar a zuciyatarh....."

Hawayene suka kara yawan sintiri a kn face dinta... "Pls say you love me...Dan Allah..pls my life.." Hammad ya fada yna kallon hawayen dake zirya a kn kuncinta, Ni ykeyi kmr ya lashesu.. "I love you black Dina..." ta furta muryarta cikin sanyi, me sanyaya zuciyar me sauraro.
"Wow...." ya furta.Ai kmr ansashi a aljannarh murna kmr zata kasheshi yau anty ta furta masa kalmar love , wayyo dadih ina zesa knshi..amma ya rasa dan murna....mikewa yy yakai mata wani Irin wawan runguma,,, tsam ya rungumeta a jikinshi yna hawaye yace "tnks..tnks... Tnks for everything my flower..I love you more and more and moreeehhhh..inasonki fiyeda kowa a duniyarnan..inasonki my breath..." hammad ya furta, cikeda shauki.

Nan guri yadau tafi wasu suka fashe da kuka tsabar tausayawa masoya biyu nan dan dagani bkramin son junansu sukeyiba. ,,wasu kuma tsabar shaukin soyayya kawai yasasu kuka. Cikin masu kukan harda niima....
zuwa lokacin Anwar ya dawo ya tarar da abinda ke faruwa shikanshi fashewa yy da kuka me tsanani, Kai kace mutuwa akayi masa..nanko tsabar farin cikine, da taya abokinshi murnar yau yasamu soyayyar anty jannarht completely."INNALLAHA MA'ASSABEEREEN..." shine abinda anwar ya furta a fili still hawaye na zirya a kumatunsa. Suhaim Kam knshi ya kulle... 🤔

Yna rungume da ita hawaye na zirya a kuncinsa suna sauka a kn kafadarta,, itama hkn ta kasance tana hawayen yyinda suke sauka a kn faffadan kirjinshi... Tsunkuyowa yy ya fara lashe hawayennata da harshenshi. Habawa nan gurin ya kara kacamewa da tafi, wasu suka hau kuka, wasu harda zama tsabar shaukin ganin JANNARHT DA HAMMAD masoyan asali kenan....
Chapter 78 · 0% Book details