← Book details Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 107

Sashe 39

Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hnkli ta karasa ta yaye lulluben da aka rufeshi dashi. Cikeda tausayawa take kallonshi duk yabi ya rme kmrba hammad dan kwalisaba. Nan da nan taja allura, da temakon anwar tayi masa allurorin. har guda biyu kan kace meye zazzabin yadan fara sauka da ciwon kirjinma.. Duk yna jinta komi datakeyimasa ji ykeyi kmr ya tashi ya rungumeta. Ynada tabbacin daze rungumeta ze samu sassaucin abinda ykeji a rnshi.

A hnkli yake bude idanuwanshi dasukayi masa nauyi. Ya saukesu a kn kyakyawar fuskarta. Babu inda yafi kallo a fuskarta musamman da karamin bakinta dayake tsuit kmr gidan tsutsa. zaune tke a kn hannun kujerar dayake kwance.tana hada mishi magungunan dazesha da daddare.

A hnkli ya furta "Anty i love you.." Dukda muryar tashi ta marasa lafia ne amma babu wanda bejiba a falon. Ido suka zubo mishi kowannwnsu hamdala yakeyi a zuciyrshi. Na samun sassaucin jikinnashi.

Itako mandiyar cak ta tsaya daga hada mishi magungunan ta zuba mashi ido ..hk kawai taji tanajin tausayinshi matuka..

Anwar ne yace " anty beci abinci bafa tin jiya..sorry da dukna rudene bn fadaba..se ynzu dnaga yadan samu nji ddh.."

Dr jannarht tace "okay..bb dmwa hado masa tea yasha..."

Tou anwar yace ya nufa kiching ya hado mishi tea din yadawo dashi a kofin tangaran. Ya mikawa anty jannarht, amsa tayi. Kna ya dago hammad din dayaketa kallonta ya jingina bynshi da byn kujerar. Se sannu suketa jero masa. Be samu dmr amsawaba se kallonta kawai dayaketayi kmr ze cinyeta.

Duk tabi ta tsargu saboda kallon dyketayi mta. Mika masa cup din tea din tayi yaki amsa.. "Kasha mna pls.." Tce cikeda tausayawa.

"Ki bani pls.." Ya furta babu kunya.

Ganin btada niyar bashidin Ya jawo hannunta ya dangana da bakinshi. Hknan badan tasoba ta fara bashi tea din a baki...yy kurba daya biyu..kawai aka bankado kofar falon aka shigo bb kou sallahma.

A tare duk suka juya dan ganin waye.. Wazasu gani mommah ce mama rabi na biye da ita.

Zumbur anty nahnah da anty salaha suka mike tsaye...

Jannarht ma bkrmin rzana tayiba yayin datayi mutuwar zaune ta gaza ko kwakwaran motsi jikinta na kakkarwa.

Alhaji zubairu da alhaji abdullahi kuwa cikeda mamaki suke binsu da kallo.. Tab sun tabbtr yau akwai bala'in da aketa gudu.

Tin shigowarta falon idanuwanta suka sauka a knsu ..cikeda tsana take kallon jannarht din datayi mutuwar tsaye shi kuma hammad ganin hkn yasa ya ajiye cup din tea din gefe ya rike hannunta cikinnashi gam..

karasawa tyi cikin zafin nama ta fisgo hannun jannarht amma ina ai hammad ya rike dyn hannun. Tna haki tace "Shegiya tsinanniya karuwa kawai..kinzo kin lalatamin yaro ..tou wallahi mugun alkaba'ir dinki seya koma knki...summum ma kasau tsinanniyar karuwa.."

jannarht de knta na kasa duk jikinta yy sanyi.. Yynda hannunta dataketaja ya farayi mata zafi.

Daddy ne yazo ya rikota yna fadin "Meye hk zainab zaki karya musu hannun yarinya ne.."

"Dallah matsa ni cikani ..maci amana kawai..yanzu daddy ace dakai ake cin amanata dakai za,a hada baki asacemin yarona a boye.."

Mama rabi tayi carab tace "Amma alhaji kaji kunya..sam bamuyi tsammanin wannan shine sakayyar dazakayiwa zainab ba duba da yadda ta nace a shekarun bya tace ita sam sekai...amma koudayake ba laifinka bne ..ai anci moriyar gangane.." Cewar mama rabi datake mgnr cikeda tsiwa tna zare ido kmr na mujiya.

Daddy yace "Ke baki duba abinda ita knwar taki takeyiba..is be kmtaba "

Daga mishi hannu mommah tayi tace "me nakeyi..dannace dana baze zauna da karuwaba..tou ina kn bakata.. dana baze zauna da karuwaba.. ga zabina can tana jiranshi a gidanshi ita nkeso kuma itace ta dace dashi...."

Alhaji zubairu yace "Abinda kikeyi beyi kyauba zainab da girmanki hba..."

Wata uwar harara ta ballara mishi tace "Aikai abinda kakeyi ka kyauta kou uban yan tsugudidi sallamamme.. Munafuki algungumi..."

Daddy yace cikin bacin rai "zainab ki gyara kalamnki.."

Nan ta fara zakal kalo mishi tace "Bazan gyaraba..inkai an bka kasha ni ba a bani nashaba.." Ta dawo da hnkalinta kn anty jannarht ta figota da karfi ta watsar..kwata kwata hammad beyi tsammanin hknba mamayrshi tayi ta fisgeta .. Faduwa tayi a kn tiles din falon ta danne hannunta na dama wani irin zafine ya ziyrceta.. Batasan santa ta kwallara karaba saboda tsabar azaba..

A rikice hammad ya mike da gudu don ya karaso inda take.. Mommah ta rikoshi tana fadin "Dan ubanka ina zakaje sallamamme..wato an wanke ruwan gindi an baka kasha kou..." Ta rikoshi.. ya kwace knshi btre dysn yyba ya krsa gareta jikinshi na rawa ya dagota daga kasan ya rungumeta jikinshi. "Sorry my life..." Hammad ya fada.

Cikin takaici ta karasa ta figo hammad din amma anty jannarht din tna jikinshi...

Daddy yace "Zainab ki kiyayeni ..zan lamumci komi daga gareki..amma knga yaronnan beda lafia kika kuskura kikayi silar wani abu ya sameshi sekin raina knki..."

Da karfi tashiga kici kicin kwace jannarht daga jikinshi amma ta kasa, dagowa tayi ta tsinka mishi mari tna fadin "Dan ubanka tinda ba knwar uwarka bace ka rabu da ita ..in kuma tarena haifeku seka gyamin.." Cewar mommah tna haki.

Cikin bacin rai daddy ya karaso ya fisgota ya zaunar da ita a kan kujera nan tyi zaman dabas a kn kujera. Ran daddy bkramin baci yyba yadda ta gallawa hammad din mari harga zicciyrshi yaji zafin marin. "zainab ki kiyayenifa.." Daddy yce rai a matukr bace.

Cikin matsifa tace "Ankiiiiii a kiyayeka din..!"

Mama rabi dke gefe ta karaso ta fisgo jannart dake jikin hammad se wani kara rungumarta ykeyi jikinshi. Da karfi mama rabi ta fisgota daga jikinshi tna shirin jefar da ita yabi ya rikota... "karki fara.." Hammad ya furta idanuwanshi cikinna mama rabi.

"Inyeee rashin kunya zkyimin..." Cewar mama rabi.

Mommah ta taso tace "Ai dolene yy miki rashin kunya ke kuwa an wanke ruwan gindin karuwa an bashi yasha..ai ynzu kouni be ganina da daraja.."

Anty nahnah ce ta karaso ta cire anty jannarht daga jikinshi da kyar shima ya saketa.. Gabaki dya hannunta zafi yaketayi mata yyn dtake jinshi kmrba nataba.

Da Ido mommah tabi nahnah tace "Inyeeee wato kema an asirceki kou...dan kn ubanki...hardake za a munafurceni.."

Mama rabi tace "Wai gaskia zainab wannan mutsiface ga zuriark ..shegiya tna fama da ido firi firi irinna gogaggun yan bariki...ti kafin ta shigo take haddasa miki jaraba."

Mommah tace "Ai wallahi seka saketa yanzunnan dan ubanka..."

A razane ya Dago red eyes dinshi yna fadin "Haba mommah..."

Mommah tayi carab tace "haba din uwarka..Wallahi kajina rantse rantsuwar dan musulmi seka saketa.."

Daddy yace "A kn meye ze saketa..ke waye ya rabaki da abinda kikeso zainab.."

''Kasan wallahi yau kou yna yawo zindir tsabar haukar sonta dayakeyi seya saketa..." Mommah ta furta.

Mama rabi tyi carab tace "Ai gaskia ya saketa kawai kowa ya huta.."

Tini idanuwanshi suka fara zubda kwallah yna kallon direction din da anty jannarht din take ...

Mama rabi tace "Tab kukama kakeyi..."

Mommah tace "Wallahi kouda zeyi kukan jini ne seya saketa..."

Daddyn anwar yace "Zainab don allah..."

Ai batama jira mezeceba ta dktr dashi "Da allah mlm bansakaba a cikin iyalina..tsaya matsayinka na karere.."

Hammad yace cikin muryar kuka "Mommah wlhy inasonta bakina baze iya furta mata kalmar sakiba.." Yy mgnr yna hawaye.

Ido suka zuba masa cikeda tausayawa. Ita knta jannart ta tausa masa.

Mama rabi kou wani uban tsuki taja tace "Dayake tare kukazl duniya da ita.."

Mommah tace "Ai yau dan ubanka kouda tare kukazo duniya wallahi sekun rabu...kai kouda ku hnta da jini ne yau sena rabaku...maza ka furta mata karmar saki."

Tsugunnawa yy kn guiwowinsa yace "Pls mommah na rokeki karki rabamu..rabuwa da ita dai dai yake da rabuwa da rayuwata...pls daddy kyi mta mgna..ka bata hkri" ya krashe mgnr yna kallon daddy.

Daddy kam iyakar bacin rai zainab tasashi a yau. cikin fushi yce " zainab kika kuskura kikayi silar rabuwar auren yarannan...na tabbtr baki taba ganin fushinaba...ina tabbtr miki da zaki gani. Inhr kikayi silar rabuwar auren nan nasu."

"Aiko sede ayi duk wadda za ayi..wlhy seya saketa yau kou in tsine masa yabi duniya.." Cewar mommah.

Zuciyr hammad tyi wani mummunan bugawa...

Daddy yace cikin bacin rai... "Inharya saketa ynzunnan kema sekisan inda zakiyi saboda yna sakinta nima nasakeki ..." Yna gma fadar hkn ya fita yabar falkn.

Mutuwar tsaye mommah da mama rabi sukayi, tinda mommah take bata tabajin abindaya girgizataba daga bakin daddyn ba se yau. "Daddy ni zaka saka..a kan wannan jakar.." Mommah ta furta murya a sanyaye. Mama rabi knta ta girgiza. A zuciya tace "Ynzu inya saketa nikuma a gunwa zan rinka samu...tab ai bazata sabuba .." Mama,rabi ta fada a zuciya.

Mommah kam byn daddy tabi tana masifa har bakin compound harya shiga cikin car amma ta tsaya bakin car din tna fadin. "Ynzu daddy nice kake ikirarin zaka saka.." Ya nata nanata mgnr cikeda mamaki a kn fuskarta. Mama rabi dmn tana fitowa itama ta biyo bynta ta tsaya kallon ikon allah.

Hammad kam mikewa tsaye yayi jiki bb kwari ya isa inda anty jannarht take rakube ya kamo hannunta me lafiyar ya dagota tsaye. Hannunshi cikinnata ya karasa ya dauki key din motarta da tarkacenta. Suka fita sukabar falon. Anwar yabiyo bynsu ya amshi key din motar hannun hammad din. Mommah na ganinsu suka shiga motar sukabar gidan. Amma ina hnklinta na ga daddy daya furta yau itace ze saki. Itakam mama rabi cikeda takaici tabisu hammad din da ido.

Kowa fitowa yy cikeda damuwa kowannensu yaja motarshi sukabar gidan.

Mommah ta fashe da kuka tna fadin "Kgni kou daddy sun hadamu gashinan burinsu ya cika sunbar gidan...daddy a gaban makiyana kake furta cewar zaka sakeni..yau ni zaka saki daddy ni zainab mtrka ta auren saurayi da budurwa.." Tana mgnr tna nuna knta.

Daddy kam rai a bace yce "Ace da zafi..ama shine ke kike kokarin raba dnki da abinda yakeso.."

Rntane ya kara baci tace "A kn tsinanniyarcanne zaka sakeni daddy.."

Beda lokacinta sam don tagama bashi haushi. ya tayrda motrshk ya kauce mata yabar gidan.
Chapter 39 · 0% Book details