← Book details Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 107

Sashe 14

Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**
Shigowa anwar yayi yasameshi a wannan halin shide yariga yayiwa knshi promise baze kara tambyrshi meke damunsaba tinda ya tambayeshi yaki yagaya mishi.. wucewa bathroom dinshi yayi , yayi wanka yasa kyn bacci yakoma falo yaciga da kallonshi, ummih dake zaune ta kalleshi tace "ina HAMMAD din..kou yy baccine.."

"Aah .." cewar anwar yna maida hnklinshi kn tv.

Sabree dake zaune kusa da mommy tace "yah anwar nifa se nke ganin duk yah HAMMAD ya chnza kwana biyu kwata kwata beson zama cikinmu ayi hira sede kullum yna daki.."

Mommy tace "nima dazu da anwar din yadawo daga aiki nayi mishi tmbyrnan amma yacemin shima ya tmbyeshi yace bakomi.."

"Okay..." cewar Sabreen.

Anwar yace "na tambayeshi nima yacemin babu komi kilande miskilancinne ya motsa mishi.." cewar anwar.

Mommy tace "tou allah ya kyauta.."

"Ameen.." cewar sabreen da anwar..

Da daddarema beyi bacciba yanata aikin tunani tunani se wajajen asubahi baccin ya kwasheshi, shide anwar bebi ta kanshiba a bngaren hammad hkn yy mishi dadih domin ko mgna bewani yawansonyi.

Jannarh ma hk ta kwana da tunani tunani a kn alhaji mansur..

Washegari Anwr yariga HAMMAD fita.

shi HAMMAD se wajajen 10:am ya tashi a bacci yashirya wajajen 11:pm yabar gidan kou ta kn mommah be biba don yasan cike take dashi a kn kwanan da yayi gidansu anwar. Mommy ma be gntaba tana dakinta tana bacci domin inta sallami iyalenta komawa takeyi ta kwanta.

Motarshi yahau yabar gidan beyi tunanin zuwa gun aikiba direct a.A.waziri special hospital yanufa idanuwanshi ita kawai sukeda mararin gani...

zaune take a office dinta tana duba pesion...seda yadauki permission dataji shine tace yashigo direct dayaga tana tareda pesion yawuce yazauna a kn kujerar dake nesa dasu ta yadda zesamu dmr kallonta yadda rnshi keso..tinda yashigo yadaura idanuwanshi a knta yji wani sanyi na ziyartar zuciyrshi ji yy duk dmwrshi ta gushe,,..

Dan satar kallonshi tayi tasakar mishi Murmushi shima murmushi ya mayar mata idanuwanshi tar a knta..

Se wajajen 12:pm tasamu masu ganin doctor din suka tsagaita.. mikewa tyi ta nufo inda yake tace "black how farh.." tyi mgnr tana karasowa, tazauna kan kujerar kusa dashi..Murmushi yayi idanunshi na knta yace "gud morning anty jannarht.."

"Morning kuma black..12:pm fa yayi afternoon de kou..yakake.."

"Lafia lau anty jannarht.."

"Ya Mommah.."

"Alhmdllh.."

"Yau tinda wuri kazo gun antynnaka kou.." tyi mgnr tana smiling.

"Yeah..I missn you kmr bngniba jia nkeji.."

Murmushi tayi tace "su black...ynzu bazakaje nka office din bane.."

"Yeah.."

"Why.."

"Bnajin zuwa yau.."

Cikeda zolaya tace "kazama lazy baka biyu antynkaba.."

Murmushi yayi yace "uhm mutum yyita aiki kmr computer..ni ynzuma bnajin dadin aikinne kwata kwata.."

Murmushi tayi tace "nace mka knada dmwa kacemin A'ah..kou bnkai ka gayamin bne.."

"Aah ..kinsan meye antyna.."

"A'ah seka fada..kafinnande kayi breakfast?

Girgiza kai yayi tce "lah knason ulcer ya kamakane.."tyi mgnr tana mikewa ta hado mishi tea dmn tnada kyn tea a office din hada mishi tayi me kauri takawo mishi ya amsa ..tazuba mishi superghetti jelop da farfesun naman kaza a sama . Takawo mishi gabanshi kallon abincin kawai ykeyi da tea din dake hannunshi ..ya kalleta takoma mazauninta tazauna tace "kaci mna.."

"Bazan iyaba.." yy mgnr yana marairaicewa.

"Meyasa..'"

"Kiyi feeding dina pls.."

Murmushi tyi tace "ummih tyi feeding dina nikuma inyi feeding dinka.."

Yace "pls badan halinaba.."

Yar dariya tayi tace "aa halinnaka ma ai babu bad black dina.." tasowa tayi tazauna a kn canter table tadaura abincin a kn cinyarta tashiga feeding dinshi..tana feeding dinshi tana bashi labari shi sam be fahimtar me take cewa shide kawai fuskarta yakebi da kallo datayi close to him se yaji kamshinta kmr a jikinshi duk duniya bega tularen dayakai nata dadihba.. lomar abincin tabashi yaki amsa "Na koshi.."

"Kadanfa kaci..Haba black dina ci mana .ci mana black kji black din anty jannarht .."tyi mgnr cikin wasa amsa yy yaci daga hk yace ya koshi shi ko ganinta yayi se yji duk duniyrnan beda wata saurn dmwa.

Kwashe komi tayi tamaidashi mazauninshi tadawo tazauna tace "yauwa inajinka.."

"Damefa.."

"Au hrka mnta..dakacemin nasan meye ..mlm katuna .."

Yace "Ayyah kinga nama mnce mezance
..."

"Kai black ka gyamin mna pls.." tyi mgnr tana marairaicewa.

Kallonta yakeyi besonko kyaftawa.."sowie inna tina zangaya maka.."

Murmushi tayi tace "tou...ni zanyi mka albishiri.."

"Okay name.."

Murmushi tayi ta kwashe labarin tsakaninta da mansur tabashi ...

Shin murna zeyi komi..harga zuciyrshi beyi farin cikiba ammande a fili yace "tou Alhmdllh..ammanke kinasonshi.."

"Tou gani nande nadesan kawai ya burgeni..Amma kabani shawara yaka gani.."

"Allah yazaba abinda shine alkhairi insha allahu zantayaki adduarh.."

"Tnks my black.."

Nan suka cigaba da hirarasu shide HAMMAD dukse yji jikinshi yy week..

Rnr a nan ya wuni yna kallonta tana aikinta se 6:pm yabar asibitin itama tawuce gida..

Seda yashiga motar yaduba phone dinshi yga miss call din anwar kusan 5 miss call kai tsaye gida ya nufa. yna wanka yji shigowar anwar..fitowa yy kugunshi daureda towel da karami a hannunshi yana goge knshi..

Anwar dake zaune a kn bed da wayrshi a hannunshi dagowa yy ya kalleshi yace "naduba office dinka bngnkaba akacemin bkzoba why..nkiraka bkyi picking ba nadawo gida still nga bknan.."

"Blood nadan gjine shiyasa yau na huta..."

Jim anwar yayi yace "gajia kuma kwata kwata yaushe muka fara aikin dazakace kagaji.."

"Nide nce mka ngjine pls ka brni.."

Tsuki anwar yayi yace "Allah tin wuri kadawo normal in jinnu ne ke dmnka kyi mgna a samo mgna mgni.."

"Mtwss Allah yarabani daganin jinnu sede kagansu can.." cewar HAMMAD ya isa bakin wardrobe dinshi yadauko kaya marasa nauyi yasaka..

Tsuki shima anwar din yy yajuya mishi bya dmn chart ykeyi yacigaba da kynshi.

**
Tini Jannarht ta nunawa alhaji mansur tyi accepting dinshi aiko nan ya fara nuna mata ruwan love kullum se sunyi waya yna bata kulawa a nata bngrenma babu laifi..

**
HAMMAD kam komi se kara tabarbare mishi yakeyi yama dena zuwa gun aiki kwata kwata kullum yna gun anty jannarht inba ita ygniba kwata kwata be ganewa ruhinshi da gangar jikinshi. Anty jannarht tazama madubin rayuwarshi.

alhaji mansur yazo yagaida ummih sosai taji zucyrta ta natsu dashi sha tara ta arziki mansur yayi mata ...tini ummih tasanarma da abih yaji dadih sosai yayin da yayi Fatan alkhairi.

**

"Mama rabi wai har ynzu bnji wani lbriba a kn mgnrmu ta kwanakiba..nifa hrynzu inasonshi Wlhy jiya da mukaje gidansu dana gnshi nji dmn ace na mallakeshi.." jawaheer dake kwance a kn cinyar mama rabi a falonsu take mgnr cikeda sangrta.

"Haba mamana bani nace miki kada ki damuba..ai knsan mgnrnan seda siyasa zata fito dole kuma sena shirya a kn yaronnan uban yan taurin kn..daman tini nagama da uwar tasu." Cewar mama rabi.

"Wlhy mama dukna kosa.."

" karki damu nifa nce miki mgnrnan angama.. ai mutuwace kadai zata hanaki shiga waziris family.."

Wani irin kayataccen Murmushi jawaheer tayi harta hngo yadda zata rinka fafah a cikin frnds dinta tab ai har takunta seya chnza..

Mama rabi ma in hknya kasance setafi kowa farin ciki ai kowa rai yayiwa dadih barin meshine.. kou ita zainab datake auren dan family din bawani dadih takejiba hasalima hassadar hkn takeyi itafa bata kiba ace ita take bawa zainab zanin dazata daura wa gindinta amma hkn beyuba ance hassada game rabo taki..kujifa uwa daya uba dya kenan allah yasa mudace.

**

Abufa yakici yaki cinyawa hammad kullum abu kara gaba ykeyi har daddynshi ya fahimci hkn yakirashi ya tambayeshi meke damunshi yace bkm kawaide beji dadih bne amma da sauki daddy yace yaje asibiti yace eh daddy yayi masa ftn samun lafia..

Hatta mommah ta fahimci ramar da yayi wata rna takirashi ta tambayeshi meke dmunshi yace zazzabine cikeda son dannata tace "tashi inkaika hospital ramar tyi yawa kmr ba my son ba.."

Murmushi yayi yace "nje tnks Mommah.." tyi mishi fatan samun sauki.

Mommyn anwar kam tin tini ita tafara tmbyrshi a kn meke dmnshi yce bkm..dole tabarshi tazubawa sarautr Allah ido..

Anwar kam shi bemasan mezeceba a lamarin HAMMAD duk yabi yazama kmr ba handsome ba kuma me ilmi..

HAMMAD tini yadena zuwa aiki kullum yna tareda anty jannarht inba ita tabashi abinciba bya iyaci ..tafi kowa fahimtr ynada dmwa saboda tre da ita dashi suke yini kullum seta tmbyeshi amsar dyace bakomi..

HAMMAD fah harya koma bin Anty jannarht har gida se after isha'i yadawo gidansu,..ummih de tana ganin ikon Allah ita in a son samuntanema kou kaunar ganin HAMMAD batayi inta hnshi yna tada mata da wani bakin ciki na uwarshi daya dade a rnta..tasamu jannarht tyi mata mgna a kn batason tarayyarta da hammad anty jannarht tabata hkri tace insha allahu zatayi kokarin zamewa daga gareshi ummih tace "better.."

Anwar de nashi ido duk a tunaninshi shakuwarne yayi tsanani har HAMMAD yake bin anty jannarht gida.

Inba anty jannarht HAMMAD ygniba beda natsuwa beda hnkli inya gntane hnklinshi ke dawowa gareshi ..yy soyayya amma besan hk zafinta yakeba yessss se ynzu ya tabbtr dacewa SO CUTA NE...baya iya bacci se yaji muryarta inhar beji muryartaba baya rintsawa sede yatashi zaune yayi zugum yayita kallon hotunanta dake wayrshi wanda ya dauketa a sace batare data ganeba ..anwar de be taba tabbtr dacewa ana kwana da kwanakiba ba ayi bacciba se a kn HAMMAD..

Jannarht kuwa in zata amsa wayar HAMMAD sede in ummih tana falo ta lallaba taje bedroom suyi wayr kou intana bedroom ita takoma falo..tanata kokarin ta janye jikinta daga gareshi ammashi bemasan tanayiba.
Chapter 14 · 0% Book details