← Book details Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 107

Sashe 100

Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dai dai Dr nahnah ta fito harabar asibitin, tnaso taje side din dasuje ajiye yaransu, taga Noor danyau rigima takeji. Car dinsu tayi packing, tsayawa nahnah tayi dan ganin car din anty jannarht. Nan suka fito da ita , sun rirriqeta, hnkli tashe, nahnah ta karasa, Dan ganin tabbas anty jannarht ce, kallo dya tayi mata tagane cikine da ita, "Subhanallahi..." Ta fada, dai dai ta qaraso da ita aka kamata, aka shiga cikin asibitin da ita,.... Alhaji yna tsaye, yga shigowarsu, hnklinshine yayi mummunan tashi, dya dora idonshi a kn Jannarht.... "Hibbarh ... " Ya fada murya na rawa. Kafin yayi wani tunani, anshige wani daki daw ita. Komawa yy yazauna dafe da knshi. "Oh ya rabbih...nasan gizon data saba yimin ne takeyimin...ya Allah la yafeni...." ya fada yynda wasu hawaye masu zafi suka fara bin kuncinsa.
Ganin hkn daya daga cikin securitys dinsa ya qaraso yace "sir knada bukatar hutu, ya kamata muje masauki..." Be jira amsar saba ya kamoshi, ya fito compound yasashi a motar, dreva yashiga yaja motar sukabar asibitin, motar sojojin na biye dashi.
A motarma hnklinshi gaza kwanciya yy se kuka kawai yakeyi kmr karamin yaro, direct babban gidanshi dake Nan kaduna alqali road suka nufa dashi.

Ana kwantar da ita a gadon asibitin tafara sharara uban Aman da babu komi se chocolate, Dr nahnah tace su Ummih su jirasu a waje, da knta tayi mata goge Aman kna ta farayi mata gwaje gwaje, Nan ta gano dan cikin dake jikinta, dukda batasan komiba game da cikin Amma ta tsinci knta a farin ciki mara misaltuwa. Ruwa tasa mata da allurorin bacci, Dan alamomi sun nuna mata bata bacci. Ba afi minti gomaba, da ruwan ya fara shigarta, bacci me nauyi ya dauketa. Cikeda tausayawa nahnah ke binta da ido, dagani, cikinnan na jikinta yna sata a whla Dan dukta rme tayi haske, hamdala kawai nahnah keyi a zuciyarta, jikinta yna bata tabbacin cikin nan na qanintane Hammadu. Ficewa tayi daga dakin tasamu, su Ummih da ni'ima tsaye cirko cirko, tace jikin alhmadulillah ansa mata ruwa zaku iya shiga.... Suka shige dakin, nahnah ta nufa emergency room din, da aketa fmn cetou wannan baiwar allah, taje tasamu, an samu daidaituwar numfashinta, jininma dake zuba ya tsaya, ansa mata drib, Se ynzu nahnah tasamu dmr gnin fuskar matar, gabanta ne yy mummunan faduwa, ganin mugun kamannin matar da Jannarht. Byn an kammala komi, anty salaha da nahnah a tare suka nufo office din nahnah, suka zazzauna anty salaha tace "knga wani ikon allah nahnah, Ni senaga kmr matarnan taso tayimin kamanni da wata dana sani..."
Nahnah tace "ashede bani kadai ngniba, Wlhy kamanninma ya baci, ke a tunaninki wacece..."
Anty salaha tace "na rasa wacece, ammande jikina yana bani kouma waye makusancinmune..."
Nahnah tace "nide senaga kmr anty jannarht kou..."
Salaha tayi Jim kna tce "kwarai kuwa, Wlhy itace, oh ikon Allah knsan ance, kou wanne mutum akwai wanda yy kma dashi,"
Nahnah tace "hkne, Amma kamaninni ya bace..."
Salaha tace "gaskia kam... daganin matar tna cikin tsananin wlha ga ulcer datayi mata chronic..."
Nahnah tace "Allah srki...kou ina daddy yaganta oho.."
Salaha tace "ina tunanin sune suka bigeta,bakiga yadda hnklim daddy ya tashiba.."
Nahnah tace "Allah ya tashi kafadunta..."
Nahnah ta amsa da ameen. "Ke albishirinki..."
Salaha tace "goro meya faru.."
Nahnah tace "An kawo anty jannarht, fa kuma Wlhy cikine da ita..."
Cikin rashin fahimta salaha tace"bnganeba,,,wacce anty jannarht din.."
Nahnah tace "ta black mna,,,Wlhy cikine da ita na fin wata biyu.."
Salaha tace "kai Dan allah..ke ina kika ganta.."
"Nce miki ankawotane dazu asibitinnan ynzu hk tna can nasa mata ruwa.."
Cikeda farin ciki Salaha tace "oh Allah me yadda yaso...kou ina black yaganta ya dura mata cikin oho..",
Nahnah tace "su suka sani, Amma wlhy inada tabbacin cikinshine, kndesan anty jannarht babu namijin dazata budewa jikinta, haka kawai, sede hammad din.."
Salaha tace"tabbas...tou masha allahu alhmadulillah...kice munsamu qaruwa, ubangijin yasa a raba lafia.."
Nahnah ta amsa da "ameen de,,,knsan kuwa bkrmin whla takeshaba, ta biyo gidanmu knsan muma hk muke whlr nan in munada ciki, "
Salaha tace "Allah sarki anty jannarht, kice tnashan baqar whla, alhmadulillah, nji dadih daban mutuba nga anty jannarht da ciki, fatan Allah yasa a sauka lafia...shi gogan yasani kuwa.."
Nahnah tace ,"Wlhy bnsaniba, knsan be jima da dawowa daga kanoba, yna nan yna isknci, jiyama danaje gidan nasamu anata daru, yace wallahi seya saki jawah.."
Salaha tace "hammadu kenan Dan daru,,,me tayi daze saketa,,,"
"A kn tana shigar masa daki...nande nabar mommah se ruwan jaraba, take antaya masa, knsan hammad da taurin kan tsiya, ita kuma mommah knsan mama rabice controller dinta.."
Salaha tace "hk rayuwa takefa sekiga mutum Dan uwankane, amma baya kaunar ci gabanka, yadda kikasan ba jininka bne,,,"
Nahnah tace "hkne ubangiji yashiga tsakanin nagari da mugu amma lamarin, da gyata.."
Salaha tace "ameen...Allah yayi mna me kyau..."
"Ameen..."

tin dare be rintsaba hkma washe gari, duk zuciyrshi bb ddh, babu abinda yakeyi Masa gizo bace, wannan baiwar allah daduka bige, hnklinshi ya gaza kwanciya, dasafe ya gaza breakfast, kou wanka beyiba, hk yashiga car dreva yaja sukabar gidan suka nufa AA waziris hospital.

**
Hk kawai yake jin zuciyrshi bb ddh, dya kwanta mafarkanta kawai yakeyi, jikinshi na bashi, duk inda take bata cikin koshin lafia. Niima ya kira danjin yaya take Amma se sahura ta daga kasancewar a gida sukabar wayoyinsu dazasuje asibitin. Dagawa tayi Dan ganin sunan hammad, ta gaisheshi ya tmbayeta Ina me wayar tace "ai suna asibiti, anty jannarht bata da Lafia dmn tin kafin mu dawo kaduna take ciwon, yau kuma se ciwon ya qaru,,,"
Hnklin hammad yy mummunan tashi, yace "meke damunta..dmn kuna kaduna.."
Sahura tace "eh...amai take fama dashi da ciwo ciwo de..."
"Wani asibiti.."
Sahura tayi Jim kna tace, "bnsaniba, ammande nasan baze wuce AA waziris hospital ba..."
Bece komiba ya katse wyr hnklinshi a matukar tashe ya daukko key ya fice daga gidan mommah na kallonshi,ya fice a rikice, tna kwala masa kira amma bebi takantaba, ya fice abinsa, car yashiga yajata yafice daga gidan a guje direct AA waziris hospital ya nufa.

A harabar gidan sukayi kicibus hammad ya kalleshi kallo dya yy masa ysan yna cikin tashin hnkli. "Daddy yaushe kashigo kaduna.."

Alhaji dake a firgice yace "yesterday.."

Hammad yace "okay sweetheart,,,akwai wani abu dake damunka ko.."

Alhajin ibrahim yace "no son..."

Hammad de yjishine kawai amma yasan dole akwai abinda ke dmnshi. "Meya sameka kazo hospital.."
Ya kwashe lbrin komi ya gayawa, hammad, shi knshi hammad hnklinshi ya tashi, a tare sukw shigo, daddy ya nufa inda yke tunanin wadda ya bige din tna ciki. Shikam hammad direct office din nahnah ya nufa. Nan yasameta tana duba system dinta. "anty Wai an kawo mata nan.." hammad ya tambaya anty nahnah.
Dagowa tayi ta kalleshi tace "seka zauna aiko..."
"Ke knsan bazan iya zamaba...pls Ina take..muje ki kaini pls.." tashi anty nahnah tayi, a tare suka fito tna gaba yna binta a baya, suka isa dakin da jannarht din take.

Tna zaune jikin yadanyi dama, daga jiya zuwa yau ankara mata ruwa leda shida, da sauri akasa ruwan saboda jikinta bb ruwa. Niima na gefenta tna bare mata kedar chocolate tana sa mata a baki, Nan da nan setae cinye a kara bare wani... Ummih na zaune bisa kujera ta zuba mata ido, duk tayi kwaro kwaro, se uban fari data kara, farin seya kara mata kyau. Suna shigowa dakin ta zuba masa ido, haushi haushinshi takeji, sbda shine yasata a whlr nan, ta gama jinyar farkewar da yayi mata, se ynzu kuma ta koma jinyar cikin daya dura mata.

Idanuwanshi na sauka a knta duk yabi ya rikice, se yji wani Irin mugun tausayinta na ratsashi, dagani yasan tanajin jiki matuka, kou yace tna kan jin jiki.

Niima da ummih suka zuba musu ido, krsowa yy inda jannarht take idanuwanshi sun rufe, "sannu flower...sannu Allah ya baki lafia.."

Ummih de na kallon ikon allah...seda nahnah ta matsa ta rada masa a kunne, "gafa Ummih..." Nan yadawo hayyacinsa, ya tsugunna yna sosa keya ya gaida Ummih ta amsa, fuska a sake, kna ta miqe tabar dakin.

Jikinshi na kyarma ya jawo kujerar da ummih ta tashi ya zauna ya kamo hannunta cikinnashi,yace "flower kinga yadda kika rame...." Se kuma yafi nonuwanta da kallo ksncewar bb hijjb a jikinta sannan bb brezia a jikinta, "anty miqe damunta pls...",

Anty nahnah tace "kafini sani ai..."

Cikeda rashin fahimta yace "menene..."

Niima de murmushi tayi, jannarht kam daya kusantota kmr ta rungumeshi takeji, saboda kamshin lotion din jikinshi datakeji,,,

Nahnah tace "anty jannarht nada ciki...kuma nka..."

Wani Irin tsalle ya daka ya tsugunna kasa bisa guiwowinsa yace "anty mi kikace Dan Allah maimaitamin..."

Niima tace "kwallo ya afka a raga.. ka zana namijin fama, an samo Dan kano..."

Farin ciki kmr hammad ze mutu Dan murna, sujjada yayi ya daga hannu yyma allahnsa godiya ya zubawa jannarht ido kawai ya fashe da kuka, ya taso ya rungumeta, itakam se qara shigewa jikinsa takeyi, saboda dadin lotion din dake jikinshi, se taji kamshin yafi mata ko wani kam ddh a duniya. "Allah sarki Antynarh...Allah yayi miki albarka uban giji yasa aljannar makomarki, Allah yasaka miki da alkhairi, Allah ya baki haquri da juriyar riqemin amanar cikina dake jikinki..." ya kara rungumeta yna hawaye.

Anty nahnah tace "mlm saketa mna, batafa da lafia so kakeyi ka gotar da ruwan dake hannunta,,,,"

Da kyar hammad ya saketa ya koma yazauna ynajin farin ciki mara misaltuwa, "alhmadulillah..." Ya furta a zuciyarta, yynda hannunshi na cikinnata.

Anty nahnah tacee "mu hk za a barmu bb tukuici.."

Hammad yace "dole a baku tukuici anty,,,ke nabaki company nina dake dubai na motoci, ke kuma niima na baki, company dina na na jirgi dake Americans..."

Niima ta zaro ido... "Wannan kyauta ai tayi yawa..."

Nahnah ta rangada guda, tacee "aah Wlhy mungode Allah yasaka da alkhairi aini nasan bross mahaukatan kudi gareka... ubangiji ya kara budi na alkhairi, "

Niima ma godiya ta farayi masa tna hawaye, "Allah ya biya, ubangiji yabar zmn tare, Allah yasauki anty jannarht lafia, "
Chapter 100 · 0% Book details