← Book details Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 107

Sashe 36

Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kimanin kwanaki biyu begantaba dukse yakejinshi beda lafiya, besan wani irin sone yakeyi mataba, ynasonta fiyeda tunaninshi, bya bacci baya iya komi ta ddh sbda rashin ganinta. Kou Yaso zuwa anwar ke tausarshi kn yy hkri don allah zuwa nan da wasu kwanaki seyaje. Yace kou fitrnan dasukeyi hadarine in aka gnsu aka gayawa mommah. Kawaide yajishine ammashi sam ba dmwrshi bace don mommah ta gnshi.

Bata waniji karfin jikintaba amma dukta gaji da zmn gidan but ba kmr adaba dasuke cikin walwala dukkanninsu yn gidan, a ynzu kowa kagani a gidan baya cikin jin ddhn rayuwa. Harda hajiyar chardi data zamo kmr yar uwa garesu, domin taso tafiya suka hnata. Dmn batada aure aurenta ya mutu kuma batada ya mace se namiji babbabe yna misra karatu. Se iyayenta da kullum tke cikin waya dasu.

Shiryawa tyi tsaf don zuwa office ta fitou ta tadda ummih a falon kasa itada hajiyar chardi. Gaidasu tayi suka amsa bb yabo bb fallasa. Ummih ta zuba mata ido cikedaso da kauna. Kullum ta kalleta takaicine ke rufeta mace har mace amma ta mare a hammad.. Mikewa tyi tna fadin "Ummih znje office yau.."

Ummih ta kalleta tace "Bakida lafiyan a hk zakije aikin..."

Daga mata kai tayi..hajiyar chardi tace "Dakin bari kin karajin sauki.."

"Alhmdllh..naji dama hajiya..wadanda nake dubawane suke isata da kira shiyasa nkeso in leka yau.."

Ummih takalleta tace "Okay..allah ya tsare allah ya bada saarh..plskarki jima de.."

Ta amsa da "tou ummihnah.."

Hajiyar chardima adduarh tayi mata. Hartakai bakin kofar fita daga falon ummih ta kirawota. "jannarht.."

Juyowa tayi ta amsada "Na'am.."

Ummih tace "Kin tambayi mijinki zakije aiki yau.?
[10/30, 3:47 PM] +234 803 727 9133: INSO CUTA NE..40

Ga masu bktr cigbn littafin su nemeni domin book din na kudine. 08033368013.

"Insha allahu znyi kokari bazan karyaba kema sekiyimin kokarin ya sakeni din.dan allah." Cewar anty jannarht da duk tabi ta kosa taga ya saketadin.

"Tou shikenan.." Cewar anty nahnah. Fita tayi ta kirawosu ummih suka dawo .anty nahnah ce ta temaka mata takaita toilet tayi fitsari domin batada karfin yin wanka, anty nahnah tace zatayi mata amma tace aah inta samu sauki zatayi,. Brush tayi mata kna ta kamo hannunta ksncewar duk jikinta bb kwari. Zaunr da ita tayi a gefen gadon ta jin ginata da fillow. Ummih de se binsu takeyi da ido tana mamakin ganin jannarht din ta dena hawayen. Tea ta hada mata ba laifi tadansha tabata magunguna kna ta temaka mata ta kwanta, dyke a magungunan akwaina bacci , baccine me mugun nauyi ya dauketa. Ummih ta kalli anty nahnah tace "sannu da kokari nagode.."

"Hbade bkm ummih..allah de ya bata lafiya..knsan ynzu se an rinka lallabata ana bata baki sbda tadan samu kwanciyr hnkli..inba hkba gaskia bb rnr dazata samu sauki..inde tna a hkne kullum kuka .."

Hajiyar chardi tace "tou ..insha allahu yarinyata mungode."

"Bkm hajiya.." Cewar anty nahnah. Mikewa tyi hadi dayi musu sallama tabar dakin. Ummih de bynta tabi da kallo, tanada tabbacin wannanma yar zainab ce donga kamanni nan sak, a zuciyrta tace itade zainab sam yaranta basu biyo bakin halintaba.

Mommah kam washe gari da sassafe ta figi mota tabar gidan. duk inda tasan hammad na zuwa a rnr seda taje, babushi babu alamarshi, se yammaci ta dawo gida da wani sabon bacin ran, tana shigowa side dinta sukayi kicibus da daddy daya shiga dubata be gntaba shine yazo fita, kallo daya yy mata yga dukta fada kmrba itaba , nan da nan yaji mugun tausayinta ya ratsashi abinka da abinda mutum keso, dukse yji haushintan dayakeji ya gushe a rnshi. ratseshi tazoyi domin ta wuce ya rike mata hannu cikin taushin murya yace "zainab ina kikaje.."

Fisge hannunta tyi daga hannunshi ta nufa bedroom dinta, binta yy yaje yasameta tana zaune a gefen bed dinta ta rafka uban tagumi. Karasawa yy yazauna a gefen bed din yadaura hannunshi a kn cinyarta.. "Zainab kinki kiyi hkri a kn lmrin yaronnan kou.." Ai kmr tna jira ta fasheda kuka me cin rai tna fadin "ynzu daddy ni zakacima mutumci a gaban yan uwanka ..dn kaga yadda na nace sekai na jure wulakncin kowa a knka amma shine ni zka wulakntani ynzu kou..." ta karashe mgnr tna kra fashewa da kuka.

Kamota yy ya sata a gefenshi yace "Me nyi miki na cin mutumci..ni bnci mutumcinkiba zainab..kuma bn wulakntakiba..kecede abinda kikayi sam bakiyi dai daiba..."

Fisge jikinta tyi daga nashi tace "Saboda nace bnason auren dana da karuwarnan.." Cewar mommah tana sharar kwallah.

"Yeah..ngade aiba haramun bne kouda ace itadin krwarce .." Cewar daddy.

"Eh ba haramun bane..ammani a gareni haramunne domin banaso..wlhy bna kaunar yarinyar kuma inde ina numfashi bazata zaunamin da danaba seya saketa indeni na tsugunna na haifeshi.." Cewar mommah. Ido yabita dashi yariga yagano duk maganganun dazeyi mata bazata fahimceshiba, "banda yadda znyi da dan uwana, saboda ya isane yy hkn.." Cewar daddy.

Kara kulewa mommah tayi tace "eh ya isa saboda shi ya haifamin yaron..wannan ai isar baka isa bace..ga,danshi dya isa dashi meyasa be aura mishi itaba.."

Dafe kai daddy yayi yace " Bakiji abinda danki yaceba a gaban kowa..shi yace ynasonta ..sanadinta nemafa yashiga wannan matsanancin ciwon zuciyar..hba zainab.." Cewar daddy cikin laushin mgna.

"Ni da an barminshi ya mutu..dyafiyemin..domin da inga aurennan kwara ace gawarshi na gani innayi kukana na wadansu kwanakine..amma ynzu in ina ganin yaronnan da yarinyarnan bakin cikine ze kasheni.." Cewar mommah tna share hawayen dake zubo mata a fuskarta.

"Allah ya kyauta.." Cewar daddy.
mikewa yayi ya fice daga dakin domin yga duk yadda zeyi mata bazata fahimceshiba. Tariga tyi nisa batajin kira.

Yna fita wayrta ta shiga ringing dubawa tayi taga sunan mama rabi ya bayyana baro baro. Dagawa tayi ta kara a kunne. Daga bngaren mama rabi tace "ya ake ciki ne wai zainab..yarinyafa tariga ta tare a gidanta tn jiya..dukda baki aiko da motarba sede na kira safara'u ita ta aiko da motoci aka kwashesu itada frnd dinta aka kaisu gidan .."

Mommah da knta yayi zafi tace " am sorry jiyannan kaina yy zafine shiyasa.."

"Uhmmm..ynzude ya ake ciki mgnr ango da tsinanniyr yarinyarnan..wlhy jiya sam bnyi bacciba.ita knta yarinyarnan dana gya mata jiya tashiga tashin hnkli.."cewar mama rabi

Mommah tasauke dogon numfashi tace " nikaina bnyi bacciba wlhy yauma tin sassafe na fita knganni nan se ynzu na dawo.."

"Ina kkje.." Cewar mama rabi.

" naje nemo yaronnan ne..tinda kwana nyi kiran lmbrshi baya shiga har safema na kirashi bya shiga.. Mama rabi shegen yaronnan kashe wyr yy ..ya myr dni yar iska a garin kaduna.." Cewar mommah.

Mama rabi tace "Shiyasa tin safen nke kirnki kinki dagawa.."

"Eh na bar wayr gidane..''cewar mommah.

"Ynzu ya ake ciki newai..nifa gaskia kinsan mgnr nan bata sabuwa wnkn kuturu da sabulun salo.." Cewar mama rabi.

"Yaronma dabn gnshiba..knga kuwa ni saki ba a hannu na yakeba da yna hannuna wlhy da tini na saketa ..nyi kwanan bakin cikin yaronnan daya kwana da auren yarinyrnan sam niba hkn nasoba. " cewar mommah ta karashe mgnr tana dafe knta cikeda takaici.

"Kai yaronnan dan bnzane wlhy..ynzude meye solution.." Cewar mama rabi.

"Wlhy kaina ya kulle mama rabi..duk juyi dya inna tina yaronnan ynada auren yarinyarnan se inji kmr in kashe kaina dan tsabar bakin ciki.." Cewar mommah dake cikeda tsantsar takaici.

"Hmm baride zainab ji nkeyi kmr nyi hauka wlhy..jiya se bacci barawo ..ji nkeyi dmn bacci nkeyi ina mafarkin wannan mutsibar.."

"Hmmm..ai yaronnan ya tonamin asiri..ynzu ni zainab muhammad gumel aji wannan lbrin wai dna ya auri shegiya kuma tsohuwa ai na shiga uku a cikin frnds da makiyyana..." Cewar mommah.

Mama rabi tace " hmmm ynzude ni daxa a gnshi komi yazo da sauki...amma yaronnan ya nunawa kowa yna sonta tinda gashi bbshi bb lbrinshi."

"Inma an gnshi mama rabi base inze saketanba.." Cewar mommah.

"Kajimin mgnr bnza..bake kika haifeshiba baki isa kisashibane kike nufi kou yaya..mtwsss..da allah inkin nemoshin kyayimin wya..bnda lokacin mgnr bnzarnan..aiduk soyayyar dakike nunawa diyankine yaja miki hkn.." Tna kaiwa nan ta katse wayr.

Mommah kam bakin cikin duniyrnan kmr ze kasheta. Abufa kmr wasa seda akayi kwanaki biyu babu hammad babu labarinshi. Inkaga mommah zakace sabon kamuce a hauka. Ga mama rabi ta takura mata sosai a kn mgnr. Gabaki dya mommah ta rasa ina zata rnta taji ddh. Duk tabi ta birkice.kullum batanan tana hnyar zuwa nemn hammad.

Shikam gogan hnklinshi kwance tini natsuwarshi tadawo gareshi, kullum cikin ci yake ya koshi ga hutu.tini yy bul bul abunshi. Abu dya ke damunshi shine tunanin anty jannarht dason ganinta.

Anwar yakan koma gida shikam hammad be zuwa ko ina yna nan zaune gu daya. Daddyn hammad shi sam besan cewar hammad din bama ya nan bllntna yasn yau yashafe kusan kwanaki biyuba bya gida.

Anty jannarht kam tadan samu sauki ba laifi. Kulawa sosai take samu a gun anty salaha da anty nahnah. A kwanaki biyun datayi a asibitin Abih yazo duba jikinta yafi a kirga don a rna yna zuwa sau biyu. Safe da yammacih, kuma duk zuwan dazeyi seyaza da kayan dubiya.

Yauma kmr kullum yaxo dasafe kuma ya dawo da yammah. ze wuce ummih ta rakoshi har bakin motarshi. "Abih..bnjikaba har ynzu a kn mgnr jannarht da auren yaronnan.. " cewar ummih. Datake mgnr byn sun iso bkin motar.

Jim abih yy ya jingina da motarshi yna karkada key a hannunshi yace "karki dmu rukayyah ..zn nemi mahaifin yaron muyi mgna insha allahu.."

Jim ummih tyi cikeda fuskar tausayi tace "Dan allah abih ka tema ..kaga batasonshi kuma ita zata zauna a gidan..matsalolin zasuyi mata yawa in aka tilastata..ga uwar mijinma bb ddh.."

Kuri abih yy mata da ido. Kna yce "Hkne rukayyah...karki dmu zaki jini insha allahu.."

"Tou abih mungode allah yasaka da alkhairi.." Cewar ummih.

"Ameen..." Abih yce hadi da shigewa motar yaja yabar asibitin zuciyrshi fal tunani tunani. Ummih ma juyawa tayi ta koma cikin asibitin. Duk zuciyrta bb ddh.

Mommah ce zaune mama rabi na gefenta tanata zazzaga balai da matsifa, itade mommah na jintane amma ta tabbatr sam mama rabi bata kaita jin zafin lamarinba. "Wannan wacce iriyar mutsiface..ni rabi..kai wallahi hada abu dake zainab beyiba..yaza ayi yau kusan kwanaki biyu kenan ankai yarinyarnan amma babu yaronnan babu dalilinshi..." Cewar mama rabi data cokalo dnkwali gaban goshi.
Chapter 36 · 0% Book details