← Book details Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 107

Sashe 71

Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi se kin fitomin da matatarh yau mommah..." Yy mgnr yna kuka tari ya taso masa nan ya fara tarin da jini...

Hnklin daddy yy mtkr tashi aje aka kira doctor nan aka kori kowa zuwa waje,. Suna Fitowa daddy ya juyi ga mommah Rai a matukar bace "wallahi zainab na baki yau da zuwa gobe inhar baki fada inda yarinyarnan takeba a bakin aurenki..." Yna fadar hkn ya fice fit.

Hnklin mommah ne ya dugun zuma ya tashi,ta tsani kalmar saki Domin kou yayane tanason mijinta kuma uban yayanta batason rabuwa dashi,duk wani abinda zata fada cika bakine amma sam bata iya rabuwa da mijinta,.

Washe gari daddyn abuja ya iso garin hnklinshi a matukar tashe, sedama ya gnshi hnklinshi ya kara tashi, dole rnr sukabar asibitin suka koma a.a waziris hospital Sam ba hkn hammad yasoba yaso a barshi a can ya mutu, Dan bega amfanin rayuwarshiba babu anty jannarht. Daddyn abuja dayaji mgnr yasa aka bazama neman jannarht din gari gari,Ada daddy yaso sakin mommah amma daddyn abuja ya hanashi dole ya kyaleta Amma yy alqawarin seya canza mata ta yadda da knta zata gane kuskurenta.

Daddyn abuja da knshi yake jinyar hammad, Dan dmn duk a yyn gidan yafison hammad,. Hammad Kam ciwo yakici yaki cinyewa kullum kara gaba ciwon yakeyi danma daddyn abuja yna tausarshi sannan yasa anyi masa rbutun dangana anata bashi ana shafe masa jikinshi, saukide sede acee na ubangiji,Domin hammad kam rayuwarshi tana cikin garari saboda anty jannarht,.

Jannarht Kam tadan fara sakin jikinta amma kullum cikin tunanin mijinta takeyi, sukan fita itada ni'imar kmr guraren saloon da gun kyn cosmetic, shima se in ni'ima ta matsa sannan jannarht ke rakata,. Sunajin dadihn zama dasu kwata kwata basuda problem, mutane ne su masu karamci.kmr katsinawa❤️💋

Abih Kam ya nemi layukansu dukkaninsu ya rasa, fatanshi Allah yasa suna cikin koshin lafia.

Jawaheer da mama rabi kuwa sun rasa ta ina zasu bullowa lamarin da an balle wata kofar se wata kofar ta bullo,.

After jsha'i byn sunyi dinner.
Zaune suke a bedroom din jannarht din suna hira yyinda ni'ima ke bawa jannarht lbrin auren datayi,. "Inason mijina yna sona Amma uwar miji ta hanani zama saboda ban haihuba..kuma munje asibiti anyi mna gwaji an tabbtr lafiarmu lau lokacinede be zoba amma mmnshi taki yarda seda tasashi ya sakeni,,,"

Jannarht tace "ayyah..Wai meyasa iyayen miji keyin hakane.."

Ni'ima tace "son zuciyarta.."

Jannarht tace "Allah yasa mufi karfin zukatanmu.."

"Ameen...aini ina tunaninma baxan karayin aureba har abadan kwara in zauna inyita azumi.."

Jannarht tace "why.."

Ni'ima tace "Ina tunanin bazan taba samun namijiba me sona da kulawa daniba kmr shi...uwa uba ma ya iya tafiyar dani..",

Murmushi Jannarht tayi tace "Kai bakida dama sis.."

"Allah kuwa sis zakiga bakouwani namiji bne ya iya tafiyar da mace, nasan knsan hkn tinda kema knyi auren nan kinji abinda akeji..."

Jannarht tace "ya akayi kikasan nataba aure.."

"Nji Ummih na bawa hajiya lbrin aurennaki ai kema de uwar mijince..."

Jannarht tCe "hkne kam sis and na girmeshi.. "

Dariya ni'ima d
Ta kwashedashi tace "kamarya kin girmeshi..hmmm namiji bya kadan maybe beyi miki cin dazaki gane hkn bne,."

Murmushi Jannarht tayi zuciya fal dmwa tace "nifa bema taba kusantataba..."

"What.... Be kusancekiba kikace da gaske sis." Ni'ima ta tmbyeta cikin rashin fahimtarh.

Jannarht tace "wallahi knga ke ba wadda Zan boyewa komi bace tinda har kema kn gyamin naki,,,be taba kusantataba duk watannin da muka kwashe a gida daya a daki daya.."

Cikeda mamaki tace "kai...tab kuma lfiayarshi lau kuwa..Dan bb namijin daze ajiyeki ya iya hkri.."

Jannarht tace "lau yake sosai ma kuwa..Kuma bamu rabu ba ai har ynzu muna tare..."

Niima tace "sis ammande kuna romances..fadi gaskia.."

Jannarht tayi murmushi tace "eh munayi daga bya ba..ammafa still inajin kunya da kanin byana.."

Niima tayi murmushi itama tace "tab..kinanan shikam ynacan kin manna masa hauka.."

Jannarht tace "kmr yaya.."

Ni'ima tace "ke kinsan yadda namiji yakeji inya rabu da mace beyi sex da itaba kuwa,,,hmmm ai saukinta ace yayi having sex dake zefi samun sassaucinsa..ballantana make kin lasa masa zuma a baki tB...ai ynacan a kideme , dukda bnsaniba."

Jannarht hnkli taja dogon numfashi tace "danasan hknne dana Bari yy. " Ammafa a zuciya ta fadi hkn, a zahiride shiru tayi,.

Niima tace "Allah sarki..Wlhy harna tausaya masa..why da bazakije gun mijinkiba tinda da aurenshi a knki.."

Murmushi kawai Jannarht tayi tace "Ina zangnshi..."

"Zan kaiki kaduna ki gnshi...ku dan kebnce ki bashi abunnan.."

Dukan wasa jannarht ta kaiwa niima tace Allah ya shiryaki sis.... ni'ima ta kwasheda dariya tCe "Wlhy da gaskefa nakeyi ..."

Jannarht tace "rufamin asiri.."

"Rufin asirin kenan kije gun mijinki.."

Harara jannarht ta gallawa ni'ima tace "kibar zancannan kafin Ummih taji.."

Kame baki tayi tace "naja bakina nayi shiru..."

Jannarht tayi murmushi, zuciyrta fal kewar mijinta wani abunma se dare yayi, yariga yy mata mugun sabo kullum seya sata tyi rlzng sau biyu sau uku a dare hk da asubahima zeyi mata amma ynzu kam babu se hkri, kullum tana fama da hadiyar kwaya dare da safia, Amma a boye takesha kada Ummih ta gani.

..

[10/30, 3:49 PM] +234 803 727 9133: INSO CUTA NE..65

Book din na kudine Ga masu bktr cigbn su nemi 08033368013.

*Sabon book Dina me suna AUREN YIMA KAI..fans karku bari a baku labari, labarine me cikeda nishadantarwa da fadakarwa,and ilmantarwar.*

Kwanansu goma a asibitin kna aka sallamesu zuwa lokacin Allah ya fara sawa lamarin sassauci da temakon adduarh.

Koda suka koma gida daddy yanata kulawa dashi kwanansu biyu da sallamarh ya koma abuja. Mommah Kam ta dena zuwa inda hammad yake dan daya ganta seya fashe da kuka yace seta nemo masa matarsa. Hkn na daga mata hnkli, sanna Yana bata mata rai. Su mama rabi de kai ya kulle.

Kullum da tunaninta yake kwana dashi yake tashi, kullum se ya Kira lmbrta ta wayr Anwar Amma har ynzu bata shiga,ai Inka gnshi kasha wani tababbene.babu abinda yafi bashi haushi irin yadda ta barshi batare daya lashi zumartaba, hkn ke kara tada masa da hnkli,kwata kwata beda natsuwa kullum tunani gindinta yakeyi daya gani be shigaba se ynzu yakejin haushin knsa daya shiga da dmwarshi batakai hk yawaba, Amma ynzukam tunani kmr ze kasheshi.

Kwanansa uku da sallamowa daga asibitin har zuwa lokacin jikinshi beyi kwariba,se a hnkli. Fitowa yy sanye da kanaNan kaya ya rame sosai fuskarshi tayi fayau da ita, Yana ganin mommah ya wuceta a falo ba tare daya gaidataba ya fice abinshi. Ido mommah ta bishi dashi tana girgiza kai, tana fadin"oh ni zainabu..hmm lallai hammad..Allah ya shirya" ta fada cikeda alhinin yadda ya wuceta kmr be santaba.

Direct part dinsu anwar ya shiga mommy ya tadda zaune a falon tana ganinshi tace "sannu baba..yaya karfin jikinnaka.."

Krsowa yy yazauna a kn kujerar 1 sttr yace "alhmadulillah dasauki mommy..Ina wuni."

"Lafia lau hammadu...dafatande jiki da dama kou.."

Daga mata kai yayi..

"Yauwa baba Dan Allah ayi haquri asawa zuciya dangana wata rana se labari, Komi yy tsanani yana tare da sauki, *wa innaka ma'al usrun yusrah.* Allah ne ya fada... Sannan INSO yazama CUTA, HAQURI MAGANI NE Dan allah kayi haquri kji baba.."

Se yaji kmr kwallah dake mkle a idanuwanshi zasu zubo, daga mata kai yy yace "tnks mom." Cikeda tausayawa mom tace "bkm son..."

miqewa yy ya nufa kofar dazata sadashi da side din anwar. Zaune yasameshi a falonshi yna kallo tv hannunshi riqe da rmt control. Krsawa yy ya zauna a gefenshi, Anwar ya kalleshi yy smiling yace "blood dina how farh ya yarh jikinnaka .."

"Babu sauki.." cewar Hammad.

"Babu sauki kuma..kaifa musulmine ..." Cewar Anwar.

"Hmmm..nifa bazan warkeba se rnr danaga Antynarh.."

Anwar yace "zaka gnta very soon in Allah ya yarda..Amma pls kayi hkri kasawa rnka dangana pls.."

"Hmmm nifa dazaku gane kudena bni haqurinnan kwata kwata bana gane yaren nan.." hammad ya fada yna kwancia byn kujerar,

Anwar ya kame baki yace "okay sir sowie.. kada kayi hkri.."

Hammad ya galla masa harara, "kjika kuma..pls ni tashi ka kaini gidansu anty jannarht..Dan Allah Kar kace bazaka kainiba.."

Anwar yace "basunan gunwa zamuje.."

"Mugani ko sun dawo pls..ni kodama basu dawoba inna ga gidannasu nasan zansamu sassaucin abinda nakeji a zuciyatarh.."

Dafe Kai Anwar yy yace, "Kai...ynzufa nashiga ukuna ni anwar.. adade na huta amma ynzu nabani, na shiga uku.."

Hammad ya marairaice yace "pls blood..kasan bazan iya zuwaba.."

Anwar ya miqe yna fadin "wayyo Allah na babana nashiga uku kuma..."

Hammad yace "sowie.." dakinshi ya nufa ya shiryo kna ya fito hannunshi rike da car key, miqewa hammad yayi a tare suka fito compound din suka shiga car anwar yaja sukabar gidan. Direct gidansu anty jannarht suka nufa, a waje sukayi packing suka fito suka nufo get din. Me gadin na zaune waje yanajin redio suka karaso, "sannu dazuwa alhaji.." cewar baba me gadi yana rangwafawa.

Hammad yace "sannu baba ..Ina wuni.."

"Lafia lau alhaji mutanen makka..kazone ka kamani kou..adeyi hkri ka yafemin alhaji nfa bni nace subar garinnanba,."

Hammad yace "in kamaka kuma baba..Ni bnce Zan kamakaba.."

"Kace mana alhaji lokacin dakazo hajiya sunyi tafiya..."

Se ynzu hammad ya tuna shi bemasan ya fadaba, "am sorry baba bnsanma na fadaba.."

Me gadin yace "ai ba komi alhaji..nasan duk a cikin sone da kauna..."

Anwar yy murmushi yace ''sosaima kuwa.."

Hammad yace "tadawo ne pls.."

Baba me gadi yace "aah alhaji basu dawoba ..ai duk rnr dasuka diro garinnan sena nemoka nayi mka bishir.."

Hammad yace "da nyi mka babbar kyauta..Amma har yanzu baka samu labarin inda sukeba.."

"A Wlhy bamu samuba.."

"A motar haya sukaje.." hammad yace.

"Aah a motar gidane..dreva ne ya kaisu.."

"Okay...dreva din beedawoba shi.."

"Eh bedawoba ..inmade ya dawo munan bamu ganahiba.."

Anwar de na tsaye yna kallonsu..

"okay ynzu zan baka num dina Dan Allah duk rnda yazo gidannan ka kirani kasanar dani.."

Me gadi yace "to alhaji insha allahu kuwa.."

Hammad ya bawa me gadin num din Anwar Dan har zuwa lokacin beda waya beyi welcome back din sims dinsaba. Hammad yabi get din gidan da kallo harya juya zasu wuce ya dawo ya shiga cikin gidan anwar na biye dashi, suna zagaye wajen gidan, hammad na murmushi gani yakeyi kmr ze ganta.. "blood nifa gaskia nagaji.." Anwar ya fada yyndaya gaji da zagayen gidan.
Chapter 71 · 0% Book details