← Book details Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 107

Sashe 77

Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowa tayi daga wankan taga kyn da ni'ima ta ajiye mata, shafa tayi ta shirya cikin lace din nata doguwar rigace me bayyaba surar jiki. Wow kyn sun amshi jikinta kmr a jikinta aka dasasu, ya bayyana komi da komi na jikinta, hips dinta ya zauna radau dashi a cikin rigar komi da komide acan acan. Dakin ta nufo lokacin an gamama niima tayi kyau kmrba itaba. "Zauna ayi miki.." cewar fatima.

"Dade an barshi kwalliyar tayi yawa.." cewar jannarht.

Niima tace "ki zauna ayi miki Dan kadan.."

Batason gaddama hk ta zauna aka farayi mata makeup din, niima tace "ayi mata sosai da sosai pls.."

Jannarht tace "bnaso nida zansa hiijb.."

Fatima tace "inkin isa in zama soyayyiya."

Niima tace "ai jannarht batayiba.."

Aisha dake gefe tace "kikasa hiijb anty jannarht kinci amanar kyaunnan da kikayi.."

Jannarht tace "harda ke aisha.."

"Eh pls kisa gyalenki knga yaune kadai dan Allah.." cewar Aisha.

Fatima tace "ai bazama ta fara sa hijjb ba wasa takeyi.."

Niima tace "hmm aka barta tsaf setasa hiijb jannarht cefa"

Fatima tace "intasa hiijb aita cuceni.."

Suka kwasheda dariya.. aka gama ma jannarht din makeup din bkrmin kyau tayiba duk makeup dinma yafi amsarta, fuskarnan ta bada shape me matukar kyau da tsaruwa dn lips dinta ya Kara tsut dashi. Ai Nan suka shikata da magiya babu yadda taso dole tasa Dan gyalen da ni'ima tase mata Amma ji takeyi kmr q tsirara take, aka kashe mata dauri gaban sumarta ya bayyana dmn Allah ya wadatata da suma a gaban goshi aka kara gyaresu yadda zasuyi kyau suka kara fitowa, Kai akwai matafa a duniya. Har gidan Ango yazo da amaryarsa mota daya suka, security nayi musu jiniya sukabar gidan, motocin yammatan amarya suka tashi. Jannarht da aisha da ni'ima da safiya a motar jannarht suka fice a gidan dmn safia tasan gun dinner din direct gun suka nufa.

Na cikasa muku readmore dinku. Tnks mu hade gobe.
[10/30, 3:50 PM] +234 803 727 9133: INSO CUTA NE..68

Book din na kudine Ga masu bktr cigbn su nemi 08033368013.

*Sabon book Dina me suna AUREN YIMA KAI..fans karku bari a baku labari, labarine me cikeda nishadantarwa da fadakarwa,and ilmantarwar.*

Taro yayi taro, wanda yasamu halattar manyan mutane da yayansu, daga garuruwa daban daban.

Amarya da ango suna shigowa fili taron ya fashe video man yazo ya fara aikinshi, hk camera man ma duk inda sukayi seya bisu ya kashe musu picture. Nan suka isa gun da aka tanada dan amarya da ango. M,c yazo ya fara nashi aikin.

Hammad da Anwar da suhaim guri daya suka zauna, gabaki daya hammad ya tsani hayaniya, jefi jefe se yy tsuki. Hammad ne ya bude taro da adduarh cikin harshen turanci Kai dajin yadda yake turanci Kasan ya kware a fannin. Manyan mata suna ganinsa suka rude suka hau ihu daga masu wow..se masu wayyo Allah na kyau..wwanna wani guy ne..wasuma suman zaune sukayi.

Su niima kuwa Sun kusan izowa kenan motarsu ta tsaya, sukayi sukayi motar Nan taki tashi.
Niima tadau salati. "Munbani.. kunga tonon asirin da motar Nan tayi mna kou?" Tyi mgnr tana binsu da kallo.

Jannarht tace "maybe Dan an jima ba a tayarda ita bane tinfa da mukazo daga kaduna.."

Safiya tace "wai daman ta jima a ajiye..tab"

Niima tace "eh wallahi..dmn seda jannarht tace kada a fita da ita nace dole se ita zamu hau gashinan ta watsa mana kasa a ido.."

Safiya tace "tashin hnkli..ynzu qaqa za ayi.."

Aisha tace "a kira bakanike mna yazo da sauri.."

Niima tace "duk muna tsaye har a gyara, gashi anata jirnmu,.."

Safiya tace "dagaji gyaran ba wani me yawa bane."

Jannarht tace "ynzude a Kira bakaniken kawai.."

Niima ta Ciro wayrta a jaka ta kirawo bakanikensu dmn gidansu yna kusa da inda suke yace gashinan zuwa..ba jimawa ya iso, duk suka firfito waje bnda jannarht, ita tana ciki. bakaniken ya fara aikinshi...sukam suna tsaye suna yar hira,.

Seda baniken da knshi yace jannarht ta fito danya tada motar yaji.. sannan ne ta fito tana tsuki.. niima tace "sannu matar malam..kn fito dole ko.."

Jannarht tace "knsan Allah jina nakeyi kmr a tsirara nake.."

Safiya tace "toufarh...a hakan.. nida bnsa gyale bafa.."

Jannarht ta kare mata kallo taga Rabin nonontama a waje yake. Tace, "tab..aini nan ji nkeyi kmr in koma in sako hijjb."

Niima ta gallara mata harara tace "ki koma ki sako nikab, ba hijjb ba."

Aisha tace "Dan Allah anty jannarht kibar shigarki haka kinyi kyau sosai wlhy kmr in saceki.."

Jannarht tayi yar dariya kna tace "Aisha aini gyalen ne bnsaba dashiba..nifa inajin ko munje a car zaku barni gaskia bazan iya fita a hakaba.."

Aisha tace "a car Kuma ..gaskia da baki duba mnaba.."

Niima tace "Dan Allah aisha fita lamarinta .. jannarht setasa mka hawan jini wlhy.."

Sofiya tace "ai yau ko tsirara kike sekin fito hk bazamu barki a car ba...mu Allah ya bamu haquri."

Jannarht tace "haqurin me..kufa kukasa knku.."

Niima tace "ai na yaune kawai da gobe..wata rna ko ance kayi baza kayiba."

Safiya tace "wallahi kuwa.."

Aisha tace "duk cikinmufa kinfi shigar arziki..abinda yasa zakiga kmr kina tsirara dankimfimu dirine shiyasa, zakigs chape dinki ya bayyana.."

Safiya tace "aikuwa de..inda kece kikayi shigar da nayi ai yau a gun dinner dinnan baza a gane komiba..mazan mutane wasu se suma..Dan ba qaramin haqqi zaki daukaba.."

Niima ta riqe haba tace "Wai...yau da anyi ta"adi a hakanma ai se abinda hali yayi.."

Suka kwashe da dariya jannarht tace "Kai bakuda dama., "

Safiya tace "nifa ina kamu ma yayana.."

Niima tace "wa kike kamu.."

safia tace "anty jannarht mna.."

Niima tace "aiko seki saki..Dan wannan tayi nisa baza a iya kamowaba.."

Safiya tace "ai bake naceba uwar azarbabi.." dai dai wata katuwar car tayi packing a gabansu, dukkaninsu seda suka kalli motar saboda tsabar kyaunta, fitowa yy handsome guy dashi ya hadu ba laifi sanye ykeda mnyan kaya. Krsowa inda suke yayi cikin takun isa irinna yayan manya. "Assalamualaikum alaykum.." yy musu sallamah, idonshi na kn jannarht. Amsawa sukayi. yji ddhn hkn. "Dafarko De Ni sunana saifudden ana kirana da deen,"

Safia tace "nice name.."

Yayi smilin still idonshi na kn jannarht dako kallon inda yake batayiba. Yace "tnks sister..lafia kuka tsaya hk a kn titi.."

Niima tace "Lafia lau..car dinmune ya samu problem..muna jira ne a gyara mna .."

"Okay ayyah ..in bazaku damuba ina zakuje se in rage muku hanya.."

Dai dai kira ya shigo wayar niima amaryarce ta kira dagawa tayi Nan take tmbyr lafia basu krsoba gashi taro ya fashe babu babbar kawar amarya..niima tace "Wlhy car dinmu tasamu problem.."

Salati fatima ta dauka tace ku temakeni kuzo Dan allah ..ki kira gida a kawo muku wata car din.."

Niima tace "kai..gida yy nisa..baride mugani insha allahu zamuzo .." ta katse wayar.

Deen yace,"kmr ma guri daya zamuje...dinner din Dan sarkin kno.."

Niima tace "eh muma nan zamuje.."

"Okay tazo gidan sauki.. ku shiga mu qarasa kawai,"

Jannarht tace "aah mungode.."

Jin muryarta yy ta dakar masa dodon kunne, "wow..dmn kina mgna me kyau..." cewar deen.

"Nop kurmace..." Jannarht ta bashi amsa a takaice.

Smiling yyy yace "am sorry..kinada kyau far..pls ya sunanki.."

Jannarht ta dauke kai.. niima tace "ka barshi kawai mungode.."

Daidai me gyaram car din yace "hajiya niima motarfa taki tashi nayi nayi.."

A tare sukace innalillahi.. niima tace "yanzu babu wani dabara daza ayi ta tashi sulei.."

Sulei yace "gaskia babu sena kaita gareji.."

Deen yace "ku shiga mu qarasa mna hajiya pls karkuce A'arh Ni ba Dan yanka Kai bane,,.."

Safiya tace "ai bamuce Kai Dan yankan kai bane..mu shiga kawai bamuda zabi." Ta krshe mgnr tana kallonsu,

Niima ta kalli jannarht Dan itace zata bada problem dan tasan da wuya tashiga. "Jannarht muje.." niima ta tambayeta.

"Kuje mna..Ni zan koma gida.." tace a takaice.

Deen yace "kiyi hkri beauty ki temaka mushiga.."

Kou kallon inda yakema batayiba..

Niima tace "Dan Allah zakie shiga muje?.."

"Ku tafi mna nce zan koma gida,"

Safiya tace "ki koma gida kuma anty aida abu beyiba gaskia kefa babbar qawace..knga kuma anata jiranmu Dan Allah mutafi.."

Aisha tace "pls anty jannarht muje Dan Allah.."

Hk badan tasoba suga shiga motar shi kam Deen murna kmr zata kasheshi. Niimace tashiga gaba, jannarht a baya itadasu aisha da safia.

Hammad Kam a Nan inda yake zaune matan dasuka kawo knsu gunshi sunfi dari, bakin ciki kmr ze kasheshi harseda ya zagesu sannan suka saurara masa, sukam su Anwar da suhaim se dariya sukeyi...
"Mtwss hayamiyarnan ta isheni ,,da Yan iskn Yan matannan,,pls tashi muje ka mayar Dani hotel..." cewa Hammad daketa faman tsuki, yy mgnr yna kallon suhaim.

Anwar yace "ba hotel ba dandi.."

Hammad yace "dallah yimin shiru bakai naceba..suhaim nace.."

Suhaim yace "sede kakan suhaim ba suhaim ba..ynzu inbnda bakada hnkli sekawai mu fice a matsayinmu na mnya baki.."

Hammad ya yatsina fuska yace "bikin na ubankane.."

Anwar ya kwashe da dariya yace "Inna ubanshine ai bazezoba saboda za ayiwa mom kishiya,da ynzu yna gida yna kuka.."

Suhaim ma dariyar yy yace "bar Dan iska shege kawai.. ni bani car key in dauko mna pot musha abarmu mushaqata.." ya karashe mgnr yna kallon anwar danshine car key ke hannunshi.

Hammad yace "a Nan zakashamin pot ka addabeni da hayaki..aiko kayi kadan.."

Suhaim yace "karka takuramin gaskia..bttr ma ka tashi ka tafin.."

"Pls ku maidani hotel nacefa am tired.." cewar Hammad.

Anwar yace "ngde knada hannu..kai meye amfanin hannunka.."

"Kasande ko inada lafia na tsani driving ballantana banda lafia..bazan iyaba dazan iya da tini na tafi wallahi .." yy mgnr yna marairaicewa.

Suhaim yace "gaskia hammad bkayiba, billahillazi nide ba Dan iska bane dazan kaika hotel sannan in kra dawowa Kuma again..sede ko anwar..." Ykrshe mgnr yna juya akalarshi ga anwar.

"Okay nine Dan iskan dazan kaishi kenan..aisede ya zauna a gama a watse..ynzude ai babbar qawar amarya ake jira dasunzo seta fashe shikenanfa.."

Hammad ya kule yace "okay..bani car key.." mika masa Anwar yy yace "a gayas..inkaje kabawa dreva car din ya dawo mna dashi.."

Hammad yace "dayake Ni Dan iskane.."

Suhaim yace "Kaine babban Dan iska ma kuwa...."
Chapter 77 · 0% Book details