← Book details Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 107

Sashe 73

Inso Cuta Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammar daketa qoqarin yaga face din jannarht amma babu dama yace "Uhm nifa Komi zakuce baxan iya muku tsaraba ba..sede in baku kudi ki siyo..kawai se inyita fama da kya kmr wani mace.."

Murmushi niima tayi tace "yah kna raina matafa dayawa.."

"Ina Ni na isa.."

Murmushi tayi tace "yaka baro anty zuhura da bby amnah.."

"Lafia lau suke..." Suna tafe suna hira har suka iso Amma jannarht kam tayi shiru batayi mgnaba, tanade jinsu.

Packing tayi yah ammar ya fara fitowa da bah dinshi a hannunshi da gudu me gadi yaxo ya amsa ynayi masa sannu da zuwa amsawa yy fuska a sake.

Jannarht ce second din fitowa kna niima ta fito.

Ido ammar ya zubowa jannarht dmn shiyasa ya fito da wuri danyaga wacece me kamshi turarennan kallo daya yy mata yaji wani abu ya tokari kirjinshi..."wow..Allah yy halittarh.." ya fada yna Kare mata kallo kasa kasa. Wuceshi jannarht tazoyi tace "ina wuni.."

Lafia lau..." Ya amsa a saqe, riko hannunta niima tayi tace "amm sorry bn gabar muku da junaba a car hira ta kacame nida yah ammah...wannan sunanta jannarht kasan na gaya mka munyi baki tou sune.."

Yah ammar yace "nice beautiful jannarht..."

Se taji wani iri dayace mata beutiful, seta tunada hammad.

"Anty jannarht ga yah ammar.."

Jannarht tace "sannu yah ammar.."

Yace yauwa Anty jannarht.."

Dariya ni'ima tayi tce "knga bross ko ynada wasa.."

Murmushi Jannarht tayi ta ratsasu ta wuce ciki. Niima da yah ammar suka shigo falon Nan ya gaidasu Ummih da hajiyarau, zuciyrshi na mararn sake ganin anty jannarht ita kam ta shige bedroom dinta. Dan hira suka tava kna kna ya nufa bngarenshi yy wanka yayi sallah. ya shirya cikin kaya marasa nauyi,kna ya nufa dining Dan dmn duk zuwa yna tarar da abinci a dining dinshi sede in ni'ima batanan. ya kira niima a waya tana dagawa yace "kuzo mna.." tace "okay.." kna ta katse wayr ta kalli jannarht tace "tashi muje.."

Jannarht tace "ina kenan.."

"Bngaren yah ammar.."

''ni baxanjeba jiki dawo Ina jirnki.."

"Kai sis kide kra temakawa.."

Jannarht tace "in zaki kwanta a kasa bazanjeba.."

Mikewa niima tayi Dan tasan tinda tace bazataje to bazataje din bane. "Kinada bakin hali.."

Jannarht tace "nji nagode.." niima ta fice a dakin ta nufa bngaren ammar din. Tana shigo tasameshi yama fara cin abincin, "Ina jannart din.."

Krsowa tayi ta zauna tace nace tazo taki.." yace okay bade hkn yasoba..yaci abincin ya koshi suna hira yanata santi harya koshi kna ya dawo kujerar kusa da ita yace "kai sister jannarht ta hadu iya haduwa macece billahillazi.."

Niima tayi dariya dantasanshi da barkwanci tace "macece kuwa amma kwalelece.."

Batare daya fahimci me take nufiba yaci gaba da koudata niima de dariya kawai takeyi Dan yah ammar ynada barkwanci ba laifi. Tare suna dawo falon Nan aka cigaba da hira da Ammar dasu Ummih niima de ta dawo daki gun jannarht suka dasa tasu firar.

Kwanan ammar biyu da dawowa tunanin jannarht ya addabi rayuwarshi ya hanashi sukuni, gaf yariga ya fahimci ya afka login sonta dukda kuwa haduwarsu daya tin rnr dayazo jannarht bata kara bari sun haduba dukda yna bala'in son sake sata a idanuwanshi.

9:11pm ya kira niima a waya yace tazo bngarenshi..ba jimawa ta iso tasameshi kwance a kn kujerar 3sttr krswa tayi tazauna a kn 1 sttr, tashi zaune yy yace "sis howfarh.."

Nima tace "Normal brosse..yane wai naga wannan dawowar taka baka wani sakeba.."

Ajiyar zuciya yy yace "dole ki ganni hk sis na kamufarh.."

Niima tace "kmrya.."

"Wallahi tin rnr danaga jannarht na kamu da mutsifaffen sonta..."

Zaro Ido niima tayi tace "seriously.."

"Wallahi tallahi..."

"Tab..to tin wuri ka roki Allah ya yaye mka .."

Ammar yace "why...nifa sonta nakeyi bawai wasaba.."

"Nasani ai..tanada aurefarh.."

"Habade wasa kikeyi.." ammar yace danshi sam be yarda da mgnrtaba.

"Wallahi da gaske nakeyi tanada miji..."

Amanar yace "lallai kuwa ze saketa Ni na aureta kenan..ammafa batayi kma dame aureba.."

Niima tace "lallaima bross..ta ina za a fara hkn ya saketa ka aureta..hmm ai ya fika sonta dukdade bnsan yadda Kai kakejiba..Wlhy da aurenta yah ammar abarma mgnr Nan.."

"Hmmm a barta how...da gaskefa ni sonta nakeyi..tinda ke kinzo da ciki baki zanyima hajiya mgna.."

Niima tace "ba hk bne bross..haba inda bata da aure ai da tini na hadaku muma musamu kyakyawan iri..Amma matsalar auren.."

Ammar yace "ba aureba aah yasa tantabarace ..hk nima Zan aureta.."

"Hmm yah ammar kenan ka taba ganin inda akayi aure kan aure.."

"Za a fara a kaina dannide ngni inaso..malama tashi ki barmin falo tinda bakinki be fadin alkhairi."

Mikewa niima tayi tace "Uhm nide ba ruwana..tinda allah ya gni na fada mka gaskia.." ta juya tabar falon tana murmushi. Ido ya bita dashi ya tabe baki.

Washe gari takanas yaje yasamu hajiya ya tambayeta ta tabbtr masa da cewar itadin mtr aurece..tab nan ake yinta shi kuma gashi Allah ya jarabceshi da kaunarta Kuma gaskiq bayajin ze iya haqura..

Qaqa zata kaya kenan.🤔

Sorry for the typing erros.
[10/30, 3:49 PM] +234 803 727 9133: INSO CUTA NE..66

Book din na kudine Ga masu bktr cigbn su nemi 08033368013.

@saadatubintuabdullahi✍🏽

*Sabon book Dina me suna AUREN YIMA KAI..fans karku bari a baku labari, labarine me cikeda nishadantarwa da fadakarwa,and ilmantarwar.*

Kewarta ya addabeshi dan hk ya nufa gidanshi Nan ya kwana , a dakin anty jannarht kwana yayi yana rungumar kayan sawanta ynajin kamshin perfume dinta a jiki, se yakeji daman ace itace yake runguma haka, ga azabar fllng na damunshi fiyeda ada tinda ya fara romantic dinta shaawarshi ta kara yawa fiyeda ada, ga kewarta ga shaawarta, abun ya zmr masa biyu. sometimes se yarinkaji kmr tana kafa masa daddadan bakinta a kn burarshi, se yayita zillow ya tayrwa knshi hnkli babu inda za a kwantar masa, duk mommah ce taja masa da ynzu yna Nan tare da matarsa ynashan abubuwanshi. 7:am yabar gidan babuci babusha inysana tafiya kmr ze karye, ya nufa gidansu ynayin packing ya fito direct side din daddy ya nufa, yna zaune yna lazimi ya shigo zaunawa yy ya takure. Byn daddy ya shafa adduarh ya juyo ya kalleshi yace "my son ya akayi.."

Hammad yace "gud morning dad.."

"Morning..yaka tashi..kalleni inga face dinka.." cewar daddy

Dagowa yayi ya kalleshi shima shidin yake kallo. "Kayi slp yau kuwa.." daddy ya tambayeshi

Girgiza masa kai yayi,.. "bakayiba?" daddy ya kara tambayarshi.

"Yeah..daddy bna iya bacci kullum tunanin matata nakeyi, da kewarta.." hammad yCe murya a kasalance.

"Hmmm..wato bazaka sawa knka dangana ba ko my love..rayuwarka ta chanza kmr ba hammadunaba...karinka tinawafa samu da rashi duk na Allah ne.."

Hammad yayi carab yace "aini ban rasataba daddy..duk mommahce tajamin, be wucema dasa hannunta na rasa matata, nide gaskia a fitomin da iyalina tin ban kaiga mutuwaba..ko in lalace.."

Daddy ya zuba masa ido yace "tou ayi hkri dan Allah.."

Hammad yace "nide kayima mommah mgna ko mama rabi nasan sun san inda matata take..inba hakaba zansaki yarinyarnan.."

Daddy yace "saki kuma ..why.."

Hammad yace "nifa banasonta daddy kasani kada in rinka shiga haqqinta kawai Zan saketa ta aura wani.."

"Karka sake knjina ko..karka fara dan Allah..bakasan Allah ya tsani sakiba dukda shine ya halatta, Dan Allah kyi hkri kasa salama a lamarin ka roki Allah ya kawo sassauci kaji babana.."

Hammad yace "tou daddy..amma hk zancigaba da zama yau kimanin 1month kenan bnga iyalinaba a hk zan mutu.."

Daddy yace "aah bazaka mutuba a haka babana..kadeyi adduarh pls...kanade cin abinci ko.."

Hammad ya daga masa kai..

"Yauwa son pls ka rinka cin abinci Dan Allah.."

"Okay daddy tnks..." Ya fada Hadi da mikewa da niyar barin falon. "Take care pls.." cewar daddy.

"Okay Tnks alot daddy me..." Kna ya juya yabar falon jiki a sanyaye. Ido daddy yabishi dashi harga Allah yna matukar tausayin dannasa, a kullum yna rokon Allah ya kawo masa sassauci.

Direct falon mommah ya nufa, abun mamaki ya ganta zaune a falon abinda be taba ganiba a rayuwarshi ta tashi da wuri Sam bata tashi da wuri. Yazo ze giftata yaga rashin dacewar hakan yace "gudmorning..'' yana tafiya.

Mommah ta bishi da ido, "son yanzu dukka tsaneni saboda mace ko.."

Juyowa yy yace "niban tsanekiba mommah kawaide ki fitomin da matata ..ko ki gyamin inda take.."

Mommah tace a hasale "Inka kara cewa in fito mka da matarka se nayi mummunan bata maka rai..ita din kudice dazanyita boyeta,, kou itadin gold ce dazanyita adanarta..."

Hammad yy murmushi takaici yace "duk wadannan abubuwan dakika ambata tafiso daraja da matsayi a guna mommah...pls ki fahimceni anty jannarht, ita ta dace dani Dan Allah kisota kicirewa knki kiyayyarta Nizan zauna da ita kuma ina sonta why da naki baze zama adduarh ba garemu.."

Mommah tace "Allah ya kiyaye inyi muku adduarh kaida wannan yarinyar tsohuwar macen...har gaba da abadan bazan taba santaba saboda banasonta din bna kaunarta.."

"Ni ina kaunarta ..kuma Allah na kaunarmu,, harga Allah nyi miki biyayya mommah...nifa kina daukar haqqina tinda kin hanani zama da abinda nakeso.."

" banasonta Dan ubnka.. ka zauna da zabina ita nakeso.."cewar mommah.

"ni kuma abinda kikesoda din .. bnasonta nadeyi biyayya da kika auramin ita na zauna da ita, da naso a rnr Zan saketa.."

"Ai kuwa da nci kutmar ubanka.."

" Dan Allah mommah ki nemomin matata ki barmu muyi zamanmu lafia.."

"Har gaba da abadan bna fatar ka kara zama da yarinyarnan a rayuwarka...sakintama zakayi duk rnr daka gnta kji na gya maka.."

"Wallahi mommah bazan iya sakintaba..Kuma in baki nemomin matataba Zan fara zinace zinace har in haifo dan zina in kawo miki a matsayin jiknki, kuma ki reneshi ki goyashi a bynki.., tinda kinfison na zinar..kin hanani in zauna dame kwantarmin da hnklina.." yna gma fadar hkn yabar falon. Baki sake mommah ke kallonshi. ",Oh duniya taxo karshe..dole ka gyamin mgnr Nan tinda tsohuwar mace tabaka gindinta kaci...ta mallakeka..Kai Allah ya isa tsakanina da shegiyar yarinyarnan.." Mommah ta fada zuciya fal tsanar jannarht harga Allah bata tunanin zata taba son Jannarht a rayuwarta kullum kra ganin lefinta takeyi, Dan hk kara tsanarta takeyi bata tunanin zata taba sonta hat gaba da abadan..
Chapter 73 · 0% Book details