← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 64

Sashe 9

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yes, saboda ta ce zan auri yarinyar idan aurenta ya mutu saboda ita?" Ta buÉ—e baki za ta yi magana ya yi saurin É—ora yatsarsa akai ya ce "Shhhh, mu kwanta" yana faÉ—in hakan ya jata zuwa jikinsa suka kwanta.

***
Batty kasa runtsawa ta yi a wannan daran, bata tsoron a gaban kowa ta ce ita mayya ce ita da Innarta, bata sani ba ko ana yarda da ita ko akasin hakan, tunda mayen gaskiya ba zai fito ya nuna kan shi ba. Taja idanunta da sukai laushi ta lumshe su, a hankali bacci ya fara É—aukanta tana daga zaunen da take.

"Hiyaam....

"Hiyaam....

"Hiyaam!"

Haka ta ji wata kamilalliyar murya na shiga cikin kunnenta, muryar me taushi ce, da nutsuwa da kamala, sautin me muryar yana nuna neman agaji domin murya ta nuna a wahale yake, bata me yake nufi da Hiyaam ba, suna ne, ko kalma ce, ko sunan wani gari bata da tabbacin me yake buƙata. Yana cikin duhu a kuma ɗaure yake da wasu igiyoyi. A hankali ta fara tafiya zata ƙarasa inda yake domin ya juya mata baya ne bata ganinsa.

"Hai Batty, kai yaro Batty" muryar Gana ta ratsa cikin kunnenta, a É—an firgice ta farka daga baccin da É—an jujjuya kanta ko za taga mutumin sai ta fahimci mafarki take yi. Yau bata yi mafarki da Innarta ba sai da wani bawan Allah.

Gana dake tsaye ta kalli Batty ta ce "Tashi ki je maza ga Saleh can a bayan bukka yana jiranki na ganshi da ƙunshin leda a hannunsa, maza tashi Batty ki je" Sai ta ɗan turo bakinta gaba cikin yanayin ƙuruciya ta ce. "Saleh ƙirji yake matse mini Yaaye, kuma ina jin zafi sosai"

"To don ubanki da yake matse miki ƙirji ba abin daɗi yake kawo miki ki laƙume ba" Batty kallon Gana kawai ta yi idanunta da ya yi damshin hawaye, hasken fatar fuskarta sai ƙyalli yake ta cikin aci balbal ɗin da Gana ke haske ta dashi.

"To idan kina bani abinci kuma ina shan kindirmon nagge ba zan ji yunwa ba. Kuma ki faɗa mini su waye suka shigo rugarmu suka kashe jama'a suka tafi da wasu har da Innata aka kashe saboda taƙi shiga wani addinin daba Musulunci ba. Yaaye ina son yin karatu sosai ki saka ni a bokoko don Allah"

"Ƙaniyarki da karatu, bokokon a wuta da Allah Ya tsinewa masu makarantar bokoko kike so? Za ki shige ki samu Saleh ko sai na ɗaure ki a turke" ta girgiza kai a hankali tana haɗiyar zuciya don bata son kwanan cikin dabbobi. Sosai take fargabar zuwa wajan Saleh tsoro yake bata ma. Har ta yi gaba ta dawo ta ce. "Kin san mutanen da suka shigo rugar Yari? Idan kin sani ki waɗe mini su Allah sai na cinye kurwarsu tunda suka yanka mini Innata. Kuma ki faɗa mini kin san mene Hiyaam? Idan abinci ne ko kayan daɗi ki bani kin ji"

Gana ta ce "Na boni, na sani yana wajan Saleh. Kuma duk ranar da kika kuma cewa Innarki mayya ce sai na yanka ki a gidan nan, tunda Baffanki ba lafiya gare shi ba" Batty ta yi wa Gana ƙuri da ido. "Saboda kar a ce kema mayya ce tunda ke ƙanwar Innata ce ko?" Sai ta washe bakinta tana lumshe idanunta ta ce "Idan aka tambaye ni kam zan faɗe musu gaskiya"

Zangarniyyar kara ta É—akko ganin haka ya saka Batty zabura tana zura yatsarta a baki ta fara tsotsa ta yi waje. Gana ta fara tunanin dole ta raba Batty da rugar Yari tun kafin taja mata masifa.

Idanunta lumshe tana tsotsar yatsa a bakinta jikinta sanye da kayan saƙi na Fulani farare tas, hatta ƙarfta sarƙa ce da wuyanta, fararan ƙafafuwanta a bayyane a haka take tafiya har ta ƙarasa inda Saleh ke laɓe yana jiranta. Yana ganinta ya washe bakinsa sosai ya ce "Masoyiyata Batty ki yi murmushi mana ko zan ji daɗi haba Batty" ta kau da kai zuwa gefe guda tace

"Ni dai mu kunce, na daina kulaka kuma ba zaka sake taɓa mini ƙirji ba, tunda ka fara taɓa mini suke zama kamar balo wacce ka taɓa kawo mini daka je birni"

Saleh ya gyara tsaiwa ya ce "Yanzu ma biredi da lemo ja na ruwa na kawo miki Batty duba kiga"

"Ce Allah rantse in ji"

"Da gaske nake duba"

Hannu ta miƙa zata amsa ya yi baya da hannun ya ce "To bani na taɓa kaɗan kin ji? Gana da kanta ta ce na dinga yi" shiru ta yi alamar tunani sai ta ce "Amma sau ɗaya ko?"

Ya kada bakinsa wajan faÉ—in "Kayya Batty, Gana fa Innarki ce ta san ba zan cece ki ba ki buÉ—e kawai kuma ni zan aure ki" da sauri ta ce "A'a walle, É—an boko nake so kyakkywa dogo wanda zai dinga goyani yana shillani"

"To na ji buÉ—e mini"

Tattare rigar ta yi sama jikinsa har rawa yake yi wajan yin abin da ya saba na taɓe mata matasan ƙirji, data fara jin zafi yaga zata gudu sai ya manneta da bangon ya shiga murzawa da ƙarfi ihu ta saka ta fashe da kuka tana yarfe hannunta.

"Wayyo... Wayyo shikenan ya cire mini kindirmona wayyo kindirmona na barinkaÉ—i na lalashe"

Gana na jinta ta yi iska da ita, addu'a take yi dama zai lalata mata rayuwa a wajan ta wuta da bala'in yarinyar. Dan haka ta É—auki niyya gari na wayewa zata fice da Batty daga rugar Yari.

***

Sun daina jin kukan Innti!
Sun daina jin sautin muryarta!
Sun daina jin hargagin Daada!

“Mene ya faru?”

Jadid, Jaheed, da Iftihal suka shiga tambaya a ƙasan zuciyoyinsu, banda Yaya wanda tunda ya yi ƙasa da kan shi bai ɗago ba, bai kuma motsa ba, ya gaza sakin rezar data murmushe a tafin hannunsa, jini sai zuba yake kamar a lokacin rana ta take.

Ƙirjinsa ne ya shiga harbawa da yi masa rawa, wani abu ya tsaya masa a ƙahon zuciyarsa, baya ko motsi.

"Suma ta yi" cewar Jadid.

Sai ya durƙushe a wajan da jikinsa da bashi da ƙwari saboda lalurar dake damunsa, hawaye na bin farar fuskarsa. Jaheed daskarewa ya yi daka tsayen da yake jinin jikinsa ya daina gudana na wani lokaci, idan akwai wani abu da ake kira da tsoro, sun riga da sun gama shiga, tsoran rasa Innti shine abin da zai wa zuciyoyinsu wahalar ɗauka, ba balle ƙwaƙwalwarsu ta yarda zasu iya rasa ta. "Ka kira sunanta, zata amsa"

"Ba zata amsa ba" Jadid ya bawa Jaheed amsa nan take yana riƙe kan shi.

"Babban yaya!"

Suka kira sunansa a gigice ganin jini na zuba a hannunsa, bai ji kiran ba, saboda ya shiga cikin tunaninsa ne sosai,kama hannunsa da suka yi ne ya dawo dashi cikin zahiri. Ya kalli Jadid da Jaheed, ya dubi hannunsa da suka riƙe, fararen idanunsa da suka rine da ja ya buɗe musu sosai, curarriyar girarsa na haɗewa waje guda.

"Babban yaya hannunka"

Ya sake buÉ—e musu idanunsa. Sai suka yi saurin sakinsa, daya motsa idanunsa ya basu tabbacin umarni yake basu da su je su kwanta jikinsu a sanyaye suka koma shimfiÉ—arsu tare da kwanciya.

Shima kallonsu kawai yake yi, ganin da gaske ba za su yi bacci bane ya saka shi miƙewa tsaye, ya ɗauki bakin rigarsa ya yi musu firfita, duk yadda sukai ƙoƙarin juyawa suka gagara, saboda wata iska me daɗi data ratsa fuskokinsu, wacce basu taɓa jin irinta ba, nan take ta mantar da su abin da ya faru da halin da Innti take ciki, wani nauyayyen bacci ya ɗauke su. Babban yaya ya ja numfashi ya cika bakinsa da iska ya fesar, sannu a hankali ya zare rigar jikinsa duhun fatarsa me ɗaukan idanu ta bayyana, da yawan lokaci jikin mutum na yin ɗumi amma koyaushe sanyi ne a jikinsa idan tsautsayi ya saka ka raɓo da jikinsa, sai ka ji kamar ka taɓa ruwa me sanyi ne don haka ba kasafai yake gogayya da mutane ba. Sumar kan shi har ƙasan wuyansa.

Baƙa suɗik da ita, idanunsa da surkin blue blue sak irin na Ana komai da komai.

Jikin bango ya zubawa idanu, a hankali ya matsa sai bangon ya buɗe masa ya fice, yana zuwa tsakar gidan yaga Innti kwance a ƙasa babu numfashi ya durƙusa dab da ita yana kallon ta sosai, tamkar zai mai data ciki saboda soyayyar uwa haka yake ji a ƙirjinsa.

Ta cikin idanunsa ya hango ƙashin hannunta daya goce, ga jini nan yana gudana a wajan, sai daya fara saka ta nauyayyen bacci kafin ya yi bisimillah a zuciyarsa ya shafi hannun, tsananin azaba ya saka Innti firgita zufa ta jiƙe mata jiki amma iskar da yake hura mata ta baki ya hanata farkawa ko yunƙurin motsa bakinta, ya saka farin zare wajan naɗe hannun ya shafa mata magani, kana ya saki hannunta. Shi kaɗai yake iya ganin zaren kuma. Haka yaja yatsunta sukai ƙara ya daidaita musu zama, sai ya miƙe tare da Innti a hannunsa ya tsallake Daada ya kwantar da ita saman katifar ɗakin kafin ya miƙe ya fita. Har zai fice waje, ya ji sautin kukan Ifti, tabbas ita ce, yasan Ana ba zata taɓa kuka ba, suna da saɓani ta nan.

Kamar walƙiya ya ratsa ƙofar ya shige, Ifti na durƙushe tana rera kuka da muryarta da bata fita sosai saboda kukan data sha. Ana kuma na tsaye jingine da bango ta zubawa waje guda ido, yana hango yadda jikinta yake rawa da kakkarwa idanunta kamar su fita waje, jijiyoyin kanta sun yi reras a saman goshinta sai fuskar numfashi take yi. Babban yaya ya motsa.

"Yaya" Ifti ta kira sunansa.

Da sauri ta miƙe ta nufi wajansa tana riƙe shi "Mene ya samu Innti? Me Daada ya yi mata, yaya mun shiga uku idan muka....,"

Bai bari ta ƙarasa ba ya saka hannunsa ya shafi kanta yana mata tattausan murmushi.

Ajjiyar zuciya ta shiga saukewa sanda ya bata tabbacin Innti lafiya ƙalau take."Me ya sa Daada yake dukan mahaifiyarmu? Me ya sa yake shan giya? Me ya sa yake zuwa wajan karuwa, haka kowanne mahaifi yake Yaya?" Ta sake fashewa da kuka.

Jikinta har wani ɓari yake.
Chapter 9 · 0% Book details