Sashe 10
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Innti ta ce za mu yi aure watarana, muma haka mijinmu zai dinga yi mana? Ya dinga shigowa gida tsirara babu tufafi a jikinsa?"
Bashi da amsoshinta, daman shi bai taɓa amsa ko tambaya ɗaya ba a rayuwarsa idan ya shige tambayoyin jarrabawa, iya su kawai. Zata sake yin magana ya ɗora yatsarsa a saman ƙaramin bakinta alamar "Ya isa"
Sai ya matsar da bakinsa dab da fuskarta ya hura mata iska, nan take idanunta ya fara lunshewa jikinta ya saki murus ta yi kamar zata faɗi ya taro ta a tafukan hannunsa tare da kwantar da ita ya lulluɓe mata jikinta. Ganin baccinta ya yi nisa ya saka shi juyawa zuwa inda Ana take tsaye, tunda ya shigo ɗakin ko yatsar hannunta bata motsa, ya matsa dab da ita yana ɗan kallonta taƙi yadda ta kalle shi, tana da taurin kai kafiya da zuciya, tana da sauƙin hali da shiga rai kamar kuɗi, da daɗin zama da baiwa ta karatu, bata taɓa shiga sabgar mutane.
Ya saka hannunsa ya juyo da fuskarta. Sai a lokacin ta kalle shi da blue eyes balls É—inta, sai wani haske ya fita kamar magic.
Da idanunsa ya yi mata alamar "Menene?"
Sai yaga ta yi murmushi, har dimples É—inta suka lotsa ta lumshe idanunta gashin idanun suka bi fatar wajan kwanciya suma.
Kuka ya dace ta yi kamar sauran Æ´an'uwanta, amma sai yaga akasin hakan, suna da kamamceceniyya na hali, shi da ita. A hankali ta dube shi ta ce
"Babban yaya ka je ka kwanta"
ÆŠas! Yatsunsa suka bada sautin magana
"Ke kuma fa?" Haka ƙarar ta bayyana.
"Bana jin bacci"
Sai yaga tana ta murmushi jikinta ya shiga rawa sosai, ya sani idan zai kwana a tsaye yana hura mata iska ba zata taɓa ɗaukanta ko aiki a jikinta ba, sai ya kama hannunta kamar tana jira ta lumshe idanunta ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi tana sakin wata ajjiyar zuciya, duk yadda take ƙoƙarin taga hawaye ya fita a idanunta amma ya ci tura, wani irin raɗaɗi na azaba ƙirjinta yake yi mata. Gani take idan suka rasa Innti sai tafi kowa shiga damuwa a wannan duniyar.
"Ya......yaaaa" ta kasa magana.
"Zafi ƙirjina yaya....
"Ka danna mini ƙirjina"
Ta faÉ—a a rarrabe, jikinta na kakkarwa.
"Ba zan iya taɓa ƙirjinki ba Shalelen Innti"
Haka numfashinsa ya bata amsa, ganin da gaske ƙirjinta ciwo yake yi ya jata jikinsa ya rungumeta daga tsayen da suke, tafin hannunsa ya ɗora a bayanta ya dinga shafawa har sai da ya ji ta yi gyatsa ciwon ya faɗa mata. Tana jikinsa ta ce "Kamar na mutu, bana son Daada, bana son ganinsa" ta rufe idanunta da ƙyar numfashinta na sarƙewa ta ce
"Ko dai ba babanmu bane?"
Yaya ya yi mata shiru.
"ÆŠan iska ne fa, yana zuwa wajan karuwa"
"Iskanci yake yi da Ta....,"
Bai bari ta ƙarasa ba, ya danna jijiyar wuyanta sai ta tafi luu ya yi saurin rungumeta, bai san me ya sa yake jin soyayyar Ana fiye da komai ba, banda Innti mahafiyarsa ce, wani lokacin har tsoro yake kar soyayyar Ana tafi ta Innti yawa a ƙirjinsa, yana ƙoƙarin dannewa kar ya nuna fifiko ita da mahaɗinta, shi ya saka yafi hukunta Ana fiye da Iftihal ɗin.
Ya É—an sumbaci goshinta kana ya kwantar da ita kusa da Æ´ar'uwata ya yi musu addu'a shima ya fice daga cikin É—akin ta jikin bango.
Ya zauna a tsakar gidan, iska na kaɗa shi tana tafiya da duk wata damuwa dake ƙasan zuciyarsa, bayan ya lumshe idanunsa na wani lokaci, sai ya ji sanyin jikinsa ya yi masa yawa, iskar ma haka, ga wani haske dake shigar masa ido sosai, sannu a hankali ya buɗe ido, ya shiga ƙarewa wajan ido, ba tsakar gidan Innti bane, tsakiyar dokar daji ne, gefen ƙoramar dake gudana a wajan.
Cikin bacci Jadid da Jaheed suka ji muryar Innti tana kiran sunan su, a hankali suka buɗe ido, bakinsu ɗauke da addu'ar tashi daga bacci. "Innti?" Jadid ya furta a hankali "Har an kira sallah kuna bacci? Wannan baccin na magani da mene ban saba ganin irinsa ba" Jaheed ya miƙe zaune.
"Ban san ya aka yi mukai nauyi ba yau"
"To ku tashi, kar ku rasa jam'i"
Ta faɗa tana miƙewa tsaye, kaɗan kaɗan hannunta yake mata ciwo, gefen fuskarta a kumbure haka ta fita, ta dubi Iftihal ta ce
"Ana bata fito ba?"
Kafin Iftihal ta yi magana Ana ta fito daka cikin banÉ—aki kan nan babu É—ankwali, Innti ta yi sak ganin kan Ana kamar bishiya saboda tsabar yawa da tsayi, Iftihal ma kallon Ana take yi da mamaki a fuskarta.
"Allah Ubangiji ka shirya mana zuri'a, Ubangiji ka shirya mini Aysha, da asubar nan ki shiga banɗaki babu kallabi kamar kuntacciya, haba Ayshatuna, me ya sa kike so na dinga yaƙi da baki akan ki ne, haka ki kaga ƴar'uwarki na yi? Kin manta abin da ya same ki ne jiya a cikin bayan gida?"
"Fitsari nake ji sosai Innti"
"Sai ya ba ki damar fitowa haka? Ki raba kan ki da Aljanu Ana, ina rabaki da Aljannu"
"Ni ina ruwana da wasu Aljanu" ta faÉ—a tana kumbura baki
Innti ta ce "Au haka kika ce?"
"Nifa Innti zan so ganin Aljanun ma idan akwai, ko matar dana gani kawai mafarki ne, babu wasu Aljanu a duniya, kuma Innti ki yi shela, masu yi mana kashi da asuba kamar masu cikin fara don Allah su daina" kasa magana Innti ta yi idan ta biyewa Ana bata san wacce kalma zata iya amfani akan yarinyar ba. Ganin ta yi shiru ya saka Ana ta yi murmushi tana kashe idanunta "Allah Ya yi mini arziƙi na kai ki Umara da Hajji Sahibarmu abar ƙaunarmu walwala da jin daɗinmu idan bake babu gida lantarkin gidanmu baya goya marayu na karya miki ɗan kwali Babarmu"
Murmushi Iftihal ta yi tana kallon mahaɗinta gabaɗaya ita babu Daada a lissafinta, gashi ita kuma a duniya tana masifar son mahaifinta yarinya me nutsuwa bata da hargagi ko ɗaya, saɓaninta ɗaya da Ana, ita Ana data saka ƙafa waje dukkan farincikinta zai kau ta haɗe fuska bata buƙatar kowa sai iya su kawai, miskila ta bugawa a mujalla a rubuta taurin kai da kafiya akwai barkwanci amma. Iftihal yawan fara'a da murmushi duk wanda ya yi mata magana babu ruwanta, she's so friendly to everyone. Akan wannan matsalar har daina magana suke yi na minti biyar, Ana tana ganin kaf duniya Iftihal kawai take da ita matsayin ƙawa, idan kuma tana kula wasu shikenan sun ƙwace mata nutsuwar zuciyarta masifar kishin yan'uwanta gare ta.
Dai-dai nan Babban yaya ya fito yana gyara zaman Jallabiyar jikinsa, ya dubi Innti jin tana maganar Aljanu, kana ya dubi Ana, Innti ta yi mamakin ganinsa domin data shiga É—akin baya ciki, dai-dai nan ma Jadid da Jaheed suka fito, Babban yaya ya yi waje suka bi bayansa.
Alwala Ana ta yi haka Iftihal daman tuni Innti ta yi, a tsakar gida sukai sallah bayan sun idar sukai azkar suka É—ora da tilawar Kur'ani. Innti ta kunna wuta ta fara É—ora É—umamen tuwon da suka yi jiya, gaban Ana sai faÉ—uwa yake kar dai É—umamen za su ci yau ma, sun manta da abin da ya faru jiya banda Ana da Innti da Babban yaya.Abin yana zane a zuciyoyinsu raÉ—au.
Suna idar da karatun, Iftihal ta fara share tsakar gidan, Ana kuma ta fara wanke-wanke. Ƴan mazan na dawowa suka fara nasu aikin, Jaheed jan ruwa a rijiya ya cika ko'ina, Jadid na zaune yana karatun Alqur'ani saboda bashi da lafiyar yin aiki. Babban yaya kuma ya haɗa kayan Innti dana Ana dana Iftihal ya wanke tas ya shanya, Jaheed ya wanke nasa dana Jadid.
Bayan sun gama kowa ya yi wanka ya shirya weekend ne, Babban yaya sai 11 zai tafi farm center, Jaheed kuma sai 12 zai je shago Ana da Iftihal kuma babu makaranta. Suna zaune a tsakar gidan iska na kaɗawa gwanin sha'awa, sun shimfiɗa tabarma a ƙasan bishiya suna jiran Innti ta kawo musu ɗumamen tuwon. Ana ta miƙe ta nufi ɗaki babu jimawa ta dawo hannunta ɗauke da waya tana ta murmushi a fuska
Jadid ya ce "Yau kuma kin tashi daga mafarkin zama marubuciya kin É—auki burin Iftihal na zama Æ´ar jarida Allah Ya shirya mutum muna ganin ta kanmu a gidan nan" murmushi kawai ta yi masa bata ce komai ba.
"Muna É—aukan rahoto kai tsaye daga gidan rediyon Innti, me rahoto Ayshatul-Haleeym Ana"
"Ƴar jarida kika zama yau?"
Ta kashewa Jaheed idanunta.
"Yaya Jaheed, me zaka iya cewa akan É—umammen tuwon da Innti take yi yau?"
Yana murmushi sosai ya ce "Ɗumammen tuwo duniya ne, ba'a bawa yaro me ƙiwa"
Ta juya idanunta ta koma kan Iftihal ta ce "MahaÉ—ita ke mene ra'ayinki?"
Iftihal na murmushi ta ce.
"Kai mahaÉ—ita, É—umame akwai daÉ—i"
Tun kafin ta ƙarasa kan Jadid ya ce
"Kina zuwa inda nake zan kwarfeki, da wasu idanunki kamar na mage wasu koraye"
A hankali Babban yaya ya juya nasa idanun da suke blue akan Jadid sai kawai ya É—auke yana cigaba da danna waya. Ana ta koma kan Innti ta ce "Hajiya Inntinmu ta gargajiya, me za ki ce akan wannan É—umamen da kika yi mana yau don Allah"
"Allah Ya cika miki burikanki na alheri Aysha, ya shirya mini ke". Ta lumshe idanunta kamar yadda ta saba kamar me jin bacci can ta buɗe su akan Babban yaya tana ƙarasawa kusa dashi.
"Babban yaya magajin uba, me zaka ce kai kuma"
Kamar ba zai motsa ba, sai kuma ya ɗago kan shi ya sauke mata fararan idanunsa masu launi a cikin nata, bai san me ya sa ba, sai ya ji murmushi yana shirin suɓuce masa, ya kawar da kan shi zuwa gefe guda.
Duk yadda Innti taso Ana ta ci tuwon fafur taƙi ci, ta tsani tuwo kamar mutuwa.
Bayan sun gama ci, Innti ta samu Yaya a cikin ɗakinsu ta ce "Yaya, Ana taƙi cin abinci fa tun jiya, na rasa yadda zan yi mata"