Sashe 26
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gabaɗaya suka juya a tare suna kallon Azizah wacce tun ɗazo laɓɓanta suke rawar tambayar son sanin inda Sayyadi Baffa ɗin yake, gida ɗaya suke rayuwa dashi, amma ta kusa wata ko fi bata sanya shi a idanunta ba, ko motsinsa bata ji. Babu ma wanda yake jin motsin Baffa ɗin daga Nadiyah sai Diyanah sai kuma Mu'allim Hafiz Baffa ɗin. Makomar baikonsa da yake kanta take son sani sama da shekaru Biyar amma babu wani cikakken lamarin da zai iya bata tabbacin zata zama mata a wajan shi, zata zama uwar da zata cigaba da kulawa da rayuwar yaransa Nadiyah Sayyadi Baffa da Diyanah Sayyadi Baffa, tana son ta maye gurbin murgayiya matarsa Diyanah Hafizz Hafizz Baffa, wacce a tunaninta rashin Diyanah ɗin a rayuwarsa shine ya hana shi aure. Damuwarta ɗaya ce, yana son ta? Yana jinta a ran shi kamar yadda itama take jin idan yaƙi aurenta za ta yi silar ɗaukan rayuwar duk wacce zai aura a matsayin mata. Ko kuma yana jin kamar ya tsufa ya girma da auren ne saboda tagwayen yaransa da suka zama Ƴan'mata? Ta sani Dattijo ne shi, amma irin su ne ake kira da Suger Daddy. Babbar hujjar dake sawa Azizah ta ji ta karaya da komai yadda tunda take zaune a gidan sama shekaru biyar bata taɓa ganin kamannin Sayyadi Baffa na, hatta ƙwayar idanunsa kodayaushe suna cikin glasses ne, ko a photo babu kamarsa, duka gidajen t.v da suke ɗora Wa'azinsa live ko recording babu kamanninsa.
"Na shiga uku"
"Maganin shiga uku Allah" Hajiya Umaimah ta bata amsa tana watsa mata harara ta gefen ido. Mu'allim ya ce "Wajan Nadiyaah da Diyanah kawai zaka san inda Baffa ya je uncle"
"Bari na je wajan nasu daman zan duba jikin Nadiyah Sayyadi Baffa, sai na ji bayani a can" Mu'allim ya miƙe yana nufar sashin mahafiyarsa ya ce "Laba'sa Uncle" daga nan Uncle ɓangaren yaran Sayyadi Baffa ya nufa
***
Da ƙyar ta samu shigowa Bright Fm ɗin yau idanunta a kumbure saboda kukan da ta yi a dalilin cire sunanta da aka yi aka saka na Yussy, gashi labarin ya hau iska sai positng ake yi a social media bayan Yussy ta ƙirƙiri photon Malam Sani da Maryama da Talatuwa sai jaririn a Ai. Mutane nata sharing suna jinjina mata wasu a dalilin hakan suke following page ɗinta. Ahlam ta yi kuka ta ji raɗaɗi da ƙuncin zuciya sai da ta yi kamar ta ajjiye aikin. Da ƙyar Engineer ya saka ta a gaba kamar yarinyar goye yana lallashinta kafin ta haƙura ta janye.
Program ne da ita amma bata da nutsuwar yi, dole Anees ya karɓeta ta hanyar amsa tambayoyin masu saurare da sanya musu waƙoƙin nishaɗi, mutane da yawa Golden voice kawai suke tambayarsa sun fi jin daɗin muryarta a program ɗin.
Bisa dole ta amsa.
"Mita 116 kuke sauraro, Bright Fm Redio mitar zamani tashar zamani...,"
Sai ta numfasa "Me sauraro barka da rana, barka da wayewar garin yau. Golden voice É—inku ke tare daku a daidai wannan lokacin, kuma zan cigaba da kasance daku har zuwa lokacin da abokiyar aikina zata amshe ni..."
Nan ma ta sake yin shiru, Anees ya zuba mata idanu yana murmushi.
"Ehmn. Ko ina kake, ko zaka, ko me kake yi ka tabbata ka kasance da Golden voice domin mu yi nishaÉ—i tare, mu ilimantu a tare. Kiran farko dawa muke tare?"
Daidai lokacin da Ahlam ke yin program ɗin Anees ya saka a live mutane sai ganin kyakkyawar fuskarta suke. Daga gefe guda shima wayarsa me ƙirar Tap tana hannunsa a hankali ya numfasa kaɗan kafin ya juya ya kalli na kusa dashi ya ce
"Wacece ita?"
"Ahlam Abdallah Kurmi sunanta tana aiki a Bright Fm Rd"
Ya É—an yi jim can ya ce "Ina son ganinta, a nemo mini ita immediately"
"Yes sir"
***
1976.
TIVLAND.
Da ƙyar Dooshima ya danne zuciyarsa saboda sosai kukan Anum ɗinsa wacce yake so fiye da kowa da komai a duniyar yake hargitsa masa lissafi, idan ka cire Anum Jarumi shine abi mafi soyowa a zuciyar Dooshima idan yana buƙatar kasancewar su a raye dole ne ya ɓoye su kamar yadda aka saba wannan gudun tsira da ran a duk sanda Sojoji sukai musu wannan zuwan na bazata. Ya saka hannunsa ya share zufar dake bin fuskata yana kokarin mayar da hawayen idanunsa. Yana zuwa ya tarar Kaka baya harabar wajan sai ya nufi ƙofar gidan da suka ɗan zagaye. A ƙofar ya tarar da ɗan'uwansa Haan hannunsa riƙe da kibbau, daga can ɓangaren ya hangi iyalan Imande.
Ikur da Imande family ɗaya ne, kaka ɗaya ne ya haifi iyayensu. Kamar yadda Kaka ya haifi Dooshima da Haan haka a ɓangaren Imande mahaifinsu ya haifi Terhemba da Uji, da Kaka da Ityo uba ɗaya ne ya haife su, duk da sun fito daga ciki guda amma kowa yaja iyalinsa ya raɗawa iyalin sunan da suke ganin ya dace dasu. Akwai bambanci hali da ɗabi'a a bayyane, Imande sun kasance masu son zuciya da zafin rai, suna da mugata tare da ƙetar dasu kan su basu san adadinta ba.
Wannan dalilin ya saka suke da burin ganin duk abin da zai zo na samu da ci-gaba ya fito daga ɓangaren Imande kawai banda iyalan Ikur. Wajan ya ɗauki shiru sai kaka ne ya dubi Sojojin da fahimta da nutsuwa ya ce
"Kuna ganin tsoron da kuke ƙoƙarin sakawa zuƙatanmu zai saka ku samu abin da kuke so ne? Mun rasa rayuka masu yawa saboda ku, ku bari mu yi rayuwa yadda muke so"
Wani soja ya ce "Naga kamar kana da fahimta Dattijo, ƙarasu nan mu yi magana"
"A'a Kaka kar ka ƙarasa"
Kaka ya juya ya kalli Dooshima sai ya yi murmushi me kamala ya ce "Na yi imani da Aondo, babu abin da zai faru Dooshima"
Haan ne ya ce "Kaka suna ƙoƙarin kawo mana sauyi ta hanyar hana mu amfani da Addinin gargajiya ((Traditional beliefs)"
Kaka ya ce "Haan!"
"A gafarce ni Kaka, Aondo ya bayyanar mana da UWA MAMAA mu huta"
Sojan ya ce "Ba cutar daku za mu yi ba, sauyi za mu kawo muku wanda zai taimaki rayuwarku, a cikin jeji kuke rayuwa babu ilimi, baku da addini guda ɗaya da za ki ce shine kuke bi, ina so ku amshi addinin Yesu Almasih, a kafa muku gari a sanya masa suna, a gina muku makarantu, da kasuwanni na ƙawa da jin daɗin rayuwa, a baku dama na shigowa sabgar siyasa a ware muku yanki guda tare da wakilcin mutum ɗaya da zai jagorancin dukkan ƙabilar Tiv"
Uji daga ɓangaren Imande ya ce "Mutum ɗaya da zai mulki jama'ar Tiv? Kenan bamu da ikon yin abin da muke so sai bisa sahalewarsa? Ka bamu hujjar da zamu yadda" babu wasa a fuskar Sojan ya ce "A shekarar 1976, Najeriya tana ƙarƙashin mulkin soja, bayan kisan shugaban ƙasa
Murtala Mohammed. Wannan ya kawo sauye-sauye da dama, ciki har da:
Ƙirƙirar sabbin jihohi Inganta tsarin mulki da gudanarwa rasirin gwamnati ya ƙara shiga cikin yankunan karkara, ciki har da Tivland, har daku ƙabilar Tiv ɗin"
"Bamu yarda ba, bamu amince ba"
Dooshima ya yi furucin saboda wasu kuskure daya hango. Akwai soyayya mai girman gaske tsakanin Imande da Ikur family. Sai Uji ya ce yana buÆ™atar magana da shugaban sojojin, suka je gefe guda tare da yin magana. Bayan sun kammala sojan ya kalli Dooshima ya ce "Ina son na nuna maka komai a bayyane na tsarin da muke son kawo muku ka biyuni mu je" Dooshima ya juya ya kalli Kaka da Haan. Dooshima ya ce "Zan je, ka kula mini da Anum kafin na dawo, ka riÆ™e ta ita da Jarumi a wajanka É—an'uwa Haan" Haan ya ce "Aondo na tare da kai" Dooshima motar sojojin ya shiga ta “trucks, jeep†wacce suka zo da ita saboda hanyoyi basu da kyau akwai “dirt roadsâ€
Suna tafiya Terhemba ya kalli É—an'uwan nasa da suke uwa É—aya uba É—aya Uji ya ce
"Kamar kun ce wani abu da sojojin nan ko?"
Uji ya ce "Ka yi tunani Terhemba, idan za'a sake fitar da mulki a Tiv Imande sune mafi cancanta, muna buƙatar hakan idan Dooshima yana nan, ba zai bari mu samu cigaban zamani ne, na yi abin da ya kamata"
"Me ka yi?" Terhemba ya tambaya da tsoro.
Sai Uji ya buɗe hannunsa ya ce "Na siyar da Dooshima, na siyarwa da sojoji shi matsayin Bawa" daidai nan wata iska ta karaɗe wajan da wani ihu da gurnani mara daɗin ji, iskar na lafawa suka fara ganin mutane na faɗuwa ƙasa matattu fiye da mutane 20.
A tsoron Kaka ya ce "An sake yin abin kuskure wannan bala'in ba zai lafa ba zai UWA MAMAA ta bayyana" ya juya da sauri ganin gidansu na rushewa yana shigewa ciki. "Anum Jarumi, suna ciki" Haan ya faɗa a gigice yana nufar ciki da sauri Kaka ya riƙe shi ya ce "Sai haƙuri amma mun rasa su"
***A hankali take juya kanta da ya yi mata nauyi tana fuskar numfashi da ƙyar ƙoƙarin tashi take yi amma kamar an saka dutse an danne ta haka take ji, kamar me shayar da yaro haka take ji ana sha mata Nono wata zufa ta wanke mata jikinta, ilahirin jikinta ciwo suke mata gabar an saka abu an mata dukan tsiya ga wani irin sanyi da gaɓɓanta sukai mata. Duk yadda take ƙoƙarin buɗe ido da dakatar da abin da yake faruwa da ita ta kasa, ji ta yi ba zata iya tashi ba, an danne ta sosai ta kowanne ɓangare a jikin nata.
"Ayshatu" ya kira sunanta yana kunna hasken ɗakin asibitin da take ƙwance. Sai ya yi turus ganin zanin jikinta a bankaɗe sai motsi take amma ta kasa buɗe idanunta.
Babban yaya ya koma gida balle ya kira shi shine muharraminta sannu a hankali ya fara takawa zuwa inda take ya ranƙwafa kaɗan ya ce "Nanaah" a hankali ta buɗe idanunta ta sauke ganinta akan Haysaam ɗin.