Sashe 58
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da hannunta ta yi masa nuni da ɗakinsu yaya, ya miƙe gently hannunsa ɗaya cikin aljihu da nutsuwarsa ya ƙarasa cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, bai da tabbacin ko Muraad ya amsa, ya yi cak a bakin ƙofa ya zuba musu ido, Ana na jikin Yaya ya rungumeta kanta a ƙirjinsa yaja idanunsa ya lumshe, ƙirjinsa na ɗagawa a hankali, alamar shima bacci yake yana jingine da bango, Yaa Sam ya harɗe hannayensa a ƙirji idan ya kalli Babban yaya sai ya kalli Ana, sai kuma ya kalli yadda take rungume a jikin yaya, ya ɗan runtse idanunsa, ai yayanta ne, bai kuma ci ya ji abin da yake ji a yanzu ba.
Ya jima yana kallon su kafin ya juya ya fice daga É—akin ya yi wa Innti sallama jikinsa a sanyaye, zuciyarsa ta yi masa nauyi.
***
BIYA.
Batty na zaune a bakin gaban ruwan ta yi shiru tana wasa da ruwan da ƙafafuwanta data saka a ciki, idanunta ya kaɗa ya yi jajur kamar an wasa mata gaushi a cikinsu, barkonon da take ci idan ƙanƙarar maitar ta motsa a ƙare bata san kuma inda zata samu wani ba, ta yi kuka sosai da birigma duk a gaɓar kogin ita kaɗai idanunta suka kumbura. Daga bayanta ta ji an dafata cikin sauri ta juya sai taga Shatu ce, wata ajjiyar zuciya ta sauke tana jan numfashi ta ce "Shatu kin bani tsoro, ki ce na yafe miki"
Shatu ta marairai ce fuska ta ce "Shatu kika ce mini fa? Haba mutuniyar, ba masoyiyar?"
"To ai ki maitata ce ta motsa, bani da lafiya bana jin daÉ—i, mutum nake son ci Shatu"
Shatu ta waro idanu waje ta ce "Ke Batty mutum fa, ai ba'a cin mutum wallahi"
"In ji wa? A na ci Mado ma cinye shi akai, ba mutuwa ya yi ba, kurwarsa aka kame wlh"
Jikin Shatu a sanyaye tana kallon Batty ta ce
"Shatu ya ake cin mutum to? Mece maitar nan, a ina take ɗakko ki nuna mini ita" Batty ta girgiza kai idanunta ya kawo ruwa ta yi saurin goge hawayen ta ce "Nima ban san mece maita ba, amma kafin a kashe Innata, ita ce ta bani maitar, ina jin ƙanƙarar maitar na mini yawo a ciki babu daɗi Shatu. Kekam kin ji daɗi Innarki ba'a kashe ta ba, kuma tana son ki, ana ba ki amince da yawa, kina yin wanka kina sauya kaya, ina jin kamar ina wari fa" ta yatsuna fuska ta ce "Shanshanani fa ki ji Shatu wari nake yi, ɗoyin dauɗa nake" Shatu ta girgiza kai cike da damuwa.
"To yanzu wa za ki ci? Ke kika ci Mado?"
Batty ta ce "A'a Yaaye ce ta cinye Mado, ai ni ban taɓa cin kowa ba, amma an taɓa yankawa an soya an bani na ci" sai ta yi saurin kara bakinta a kunnen Shatu ta ce
"Kuma wallahi naman mutum akwai daÉ—i"
"Ce Allah Batty? Nima zan ci"
Yanayin Batty ya sauya ta ce "A'a, ai ba kyau tunda ke ba mayya bace babu ruwanki, kuma idan kika je gidan mutanen da ba ki sani ba, aka ba ki abinci kar ki ci, kar ki yi kwaÉ—ayi Shatu, idan kikai mafarki ana ba ki É—anyen nama ki ci, to kar ki ciki, idan ba haka ba, kina ci watarana za ki wayi gari kina kallon kayan cikin mutane. Ki dinga addu'a kina neman dafa'i na sharrin mayu"
Ita dai Shatu bata ce komai ba, domin kamar almara haka take kallon abin, bata ma san mene maita É—in ba, ta kuma gaza gane maganar Batty. Sai ta ce "Jiya da daddare na ganki Batty, ina kika je?"
"Maitar dare. Nima ai na ganki a jiyan wajan ƙarfe uku na dare kin fito shan ruwa a kogi"
Shatu ta zaro ido ta ce "Ni É—in?"
"E, nima ai kin ce kin ganni haka ne?"
Shatu ta ce "Ni a mafarki na ganki fa"
"Zahiri ne, da babu Dafa'i a jikinki wallahi da tuni na kama kurwarki Batty, ki daina kwanciya da ƙishirwa, idan mutum yana jin ƙishirwa kuma yaƙi shan ruwan har ya kwanta bacci, to kurwarsa bata jurewa, tana tashi cikin dare duk inda ruwa yake ta nema, a wannan tafiyar tana haɗuwa da kurwa kala-kala, muma mayu muna fitowa, kuma duk kurwar da babu Dafa'i a jikinta nan take ake kame ta, madadin mutum ya farka da lafiya kamar yadda ya yi kwanta sai ya tashi cikin jinya. Shatu duk mutuwar da ake yanzu ta farat ɗaya wallahi mayu ne da yawa, sharrinmu yana da yawan gaske"
Idanun Batty ya kawo ruwa ta ce "Shatu ke kamar jinina ce bana son na rasa ki, zan ba ki magani sosai, idan kina tare da maye a cikin gida ko maƙwafta ne ku, muddin kikai wannan wallahi sai dai maye ya ganki ya barki, daga ƙarshe ma ko inuwa ɗaya ba zai iya haɗawa dake ba. Ki samu Igiyar yaɗiya, sai ki bubbuga da dutse, sai ki samu sassaƙin maɗaci amma da dutse ake sassaƙe wa, ba da adda ko gatari ba, ko magirbi ba. Ki haɗa su waje ɗaya ki zuba a babbar roba ko ƙwarya sai a zuba ruwa akai, sai ki samu ɗanyen tafarnuwa ki zuba a ciki, sai ki rufe ruwan, ya yi awa ashirin da huɗu ki dinga sha kina wanka, idan mayen a cikin gidanku yake ki dinga wankan safe da yamma, idan a maƙwafta ne da yamma kawai za ki dinga yi, ba maye ba ko Inna Badakuwa ce nan gani nan bari Shatu sai ta Allah bata mutum ba" Shatu ta yi shiru tana sauraran Batty. A hankali ta miƙe ta ce
"Bari na koma cikin gari kar Innata ta ji shiru" Batty ta jinjina kai kanta a ƙasa.
***
BAFFAS ESTATE.
Tunda ta zauna a hadaɗɗan parlourn kanta a ƙasa yake, tana jin yadda idanu wajan huɗu suke kallon ta, Azizah, Hajiya Umaimah sai kuma Mamy, da Hajiya Kaltum ƙanwar Hajiya Umaimah. Mamy ta kalli Ahlam a hankali ta ce "Allah Ya nuna mana lokacin Nikkah da alheri, ya saka mutuwa ce zata raba tsakaninki da Liman" ita dai bata iya cewa komai ba, kanta yana ƙasa abinta.
Liman ne ya kame fuska ya ce "Amin Mamy"
Ta miƙe tana faɗin "Idan zata tafi ka yi mini magana Please Asad" nan ma ya ce "I'll"
Azizah zuciyarta a cunkushe tabi bayan Mamy da kallo ta ce "Mikirar mace, wallahi ina zargin idan ba ita ta rusa aurena da Baffa ba, kuma wallahi indai ina raye Baffa bashi da wata mace a duniya sama dani"
Hajiya Kaltum ta ce "Ko ba Hajia Ni'ima ba? Ai na jima da fahimtar kamar tana da saka hannu a ƙin auren Baffa, hatta hatsarin Baffa wallahi ita nake zargi ke har mutuwa Hafiz Baffa ma ina saka ran ita ta tsara komai, saboda ta samu gado me yawa, ba tana taƙamar zaratan yaranta maza har biyu ba, ga ƴar auta Hidaya da late Hafizz Hafizz Baffa ya ɗauki son duniya ya ɗora a cikinta tun kafin ma yaga zuwanta duniya, da yana raye aka haife ai ƴar kallo za ki zama a gidan" Hajiya Umaimah girgiza ƙafa kawai take yi, ba tare da ta ce komai ba.
Liman ya kalli Hajiya Kaltum ya ce
"Is this the right time da za ku yi wannan maganar? Haba Ummy" ta kalle shi.
"Ni na mance wai matarka ka kawo ashe Liman. Ke yama sunanki kika ce É—azo?"
Kanta a ƙasa ta ce "Ahlam sunana"
"Ke dilla bana son iyayi, sunan gaskiya"
Slowly Ahlam ta ɗago kai ta kalli Azizah, shigar alfarma ce a jikinta wuyanta ya sha daham, ta yi kamar ba zata yi magana ba sai ta ce "Halimatu sunana" Azizah ta taɓe baki
"Hajiya Halimah kenan ko?"
"No" kawai Ahlam ta ce.
Azizah ta ce "Kan uba, uban mene no?"
"Ina nufin ko airport ban taɓa zuwa ba, ban kuma san ranar zuwana ba, amma ina da rufin asiri dai-dai gwargwado in sha Allah"
Hajiya Umaimah ta ɗago kai ta kalli Ahlam sosai, taga gabaɗaya lace ɗin jikinta bai fi 150k ba, ɗan kunnen ba gold bane, ta kalli hannunta a maƙale da ya yi yaushi ta taɓe bakinta ta ce "Ok, ashe ke nakasasshiya ce?"
Wani abu ya daki zuciyar Ahlam ta É—ago a hankali ta kalli Liman sai ya yi saurin runtse idanunsa yana É—auke hawaye ya fara cika idanunta. Azizah ta ce "Disable kenan ko?"
Hajiya Kaltum ta ce "Ko shi ya sa daga zuwa neman aure aka É—aura auren? Wannan ai dole Liman ya auri lafiyayyiyar mace gsky"
"Let's go" Liman ya miƙe yana riƙo hannun Ahlam, bai jira ya koma part ɗin Mamy ba, yana da tabbacin ma likita ne yake duba Mu'alim itama tana wajan Al'ameen ɗin. Suna shiga mota Ahlam ta fashe da wani irin raunataccen kuka, wanne irin aure ne wannan, tun kafin ta shiga? Ba zata iya ba, gwara ta nemi ɗaukaka a aikinta akan wannan zaman na aure, babban gida ne sun fi ƙarfinta. Ta kowacce fuska, Liman ya kasa ce mata komai sai hannunta daya riƙe.
Wajejen 8:00 na dare ya sake dawowa ya ɗauke ta, zuwa wajan awards, sabuwar Abaya ya saka me masifar kyau, shi da kan shi ta yi masa kyau, lokacin da suka ƙarasa event ɗin ya cika sosai, ta riga shi fitowa suka hadu da Zainab Alƙali suka yi ciki, Anees tun daga nesa yake mata murmushi ta yi ƙasa da kanta. Waje suka nema suka zauna da Zainab Alƙali, Yussy sai ƙwainane take, ta saka wasu shegun kaya, ɗuwawunta ko motsi ba ya yi ya haɗe da bayanta ya shafe. Zainab Alƙali ta zunguri Ahlam
Ta ce "Ga mutuniyar fa, yau sai Allah"
Murmushi kawai Ahlam ta yi hankalinta akan wayarta, ta samu kanta da yin research akan TIVA. Zainab Alƙali ta ce
"Ke kawai nake jira a bawa award na tafi"
Ahlam ta ce "Wa fa?"
"Wawa" cewar Zainab Alƙali.
"Kefa kin san dole sai an ba ki award, akaf Bright Fm waya kai ki kawo news tell me?"
"Uhm"
Aka ci aka sha.